Al’ummar Babura sun shirya gagarumin taron girmamawa domin karrama Dr. Salisu Mu’azu, bayan nada shi a matsayin Daraktan kuma babban likitan asibitin koyarwa na Rasheed Shekoni da ke jihar Jigawa, da kuma samun matsayin mamba na Cibiyar Kasa (mni).

Da yake jawabi a wajen taron, Shugaban Kwamitin Shirye-shirye, Rabiu Umar, ya bayyana cewa an gudanar da taron ne domin nuna godiya ga Allah da kuma murnar manyan nasarorin da Dr.

Mu’azu ya samu.

Ya yaba da kokarin Daraktan wajen gudanar da aikinsa da kwarewa, da kuma ci gaba da tallafa wa al’umma.

A sakon da aka gabatar a madadin Mai Martaba Sarkin Ringim, Alhaji Dr. Sayyadi Abubakar Mahmoud, wanda Mai Girma Alhaji Usman Sayyadi, Babban Hakimin Masarautar, ya wakilta, ya nuna godiya ga masu shirya taron.

Ya bayyana karramawar a matsayin abin da ya dace da Dr. Mu’azu, yana mai jaddada jajircewarsa, da tausayi da himma wajen yi wa al’umma hidima.

Haka zalika, Shugaban Karamar Hukumar Babura, Alhaji Hamisu Muhammad Garu, ya taya Dr. Mu’azu murna bisa nasarorin da ya samu a fannin aikin likitanci, inda ya danganta hakan da jajircewa da  amana.

Ya tabbatar masa da cikakken goyon bayan al’umma tare da addu’ar samun karin nasarori.

A nasa bangaren, Dr. Salisu Mu’azu ya bayyana godiya sosai bisa girmamawa da karramawar da al’ummarsa ta masa.

Ya kuma nuna godiya ga Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Umar Namadi, bisa damar da ya ba shi zuwa makarantar NIPSS da ke jihar Filato.

A yayin taron, mutane da kungiyoyi daban-daban sun mika kyaututtuka da lambobin yabo ga Daraktan, ciki har da reshen kungiyar likitoci ta Najeriya na jihar Jigawa, J Health Beneficiaries, kungiyar Nas nas da Ungozoma ta kasa, da kuma kungiyar masu kula da lafiyar hakora ta Babura da sauransu.

 

Usman Muhammad Zaria 

 

 

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: Babura Jigawa

এছাড়াও পড়ুন:

Bai Dace A Mika Wuya Ga Wanda Ya Nuna Fin Karfi Da Matakan Haraji Ba

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Tawagar Jami’ai Da ‘Yan Kasuwar Ta Tunusiya Ta Gana Da Mataimakin Shugaban kasar Iran
  • Bai Dace A Mika Wuya Ga Wanda Ya Nuna Fin Karfi Da Matakan Haraji Ba
  • Ministan Harkokin Wajen Kasar Iran Ya Tattauana Da Shugaban Hukumar IAEA
  • An Fara Gudanar Da Zaman Taron Hadin Gwiwar Tattalin Arziki Tsakanin Iran Da Kasashen Nahiyar Afirka
  • Amurka Ta Ce: Shugaban Rikon Kwarayar Siriya Al-Julani Ya Yi Alkawarin Cewa Ba Zai Cutar Da Tsaron Isra’ila Ba
  • Hakimin Kafin Hausa Ya Jinjinawa Gwamna Namadi Bisa Ayyuka Cigaban Al’umma
  • Sarkin Daura Zai Karrama Ja’o’ji Da Wasu Samarin Arewa
  • Yadda Za A Gudanar Da Zaben Sabon Paparoma Da Zai Gaji ‘Pope Francis’
  • Boko Haram Sun Kashe Mutum 12 A Wani Sabon Hari A Borno
  •  Kotun Tsarin Mulki Ta Gabon Ta Tabbatar Da Nasarar Nguema A Zaben Shugaban Kasa