Sin Na Ci Gaba Da Kasancewa Cibiyar Rarraba Hajojin Da Masana’antu Ke Sarrafawa
Published: 26th, March 2025 GMT
Wani rahoto da aka fitar yau Talata, yayin zaman taron shekara-shekara na shekarar 2025, na dandalin tattaunawa na Asiya na Boao, ya nuna yadda kasar Sin ke ci gaba da kasancewa cibiyar rarraba hajojin da masana’antu ke sarrafawa.
Rahoton mai taken “Nazarin tattalin arzikin Asiya, da hadadden rahoton ci gaba na shekarar”, ya nuna yadda tun daga shekarar 2017, hada-hadar cinikayya ta duniya a fannin rarraba matsakaitan hajoji, ke kara dogaro kan kasar Sin sama da dogaronta ga yankin arewacin Amurka.
Bugu da kari, rahoton ya ce yamucin cinikayya da Amurka ta haifar a shekarar 2018, bai baiwa Amurkan wata nasara ta fuskar daga matsayinta, a hada-hadar rarraba hajojin da masana’antu ke sarrafawa ba. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Sin Ta Daga Zuwa Mataki Na 10 A Jadawalin GII Na Kasashen Dake Kan Gaba A Fannin Kirkire-Kirkire
Cikin jadawalin GII na 2025, kasashe masu karanci da matsakaicin kudin shiga 17, sun taka rawar gani fiye da yadda aka yi hasashe, bisa matsayin ci gabansu, yayin da kasashen Afirka dake kudu da hamadar Sahara ke kan gaba, cikin kasashe mafiya samun ci gaban kirkire-kirkire, inda kasashen Afirka ta Kudu, da Senegal da Rwanda ke kan gaba a jerin kasashen shiyyar. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp