Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya musanta zargin kasar Amurka na cewa wasu jiragen ruwan JMI suna amfani da tudan kasar Iraqi sun kai kawo a ruwayen yankin.

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta fadawa Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran, kan cewa Aragchi yana fadar haka ne a jiya litinin, a lokacinda yake zantawa ta wayar tarho da tokwaransa na kasar Iraki Fu’ad Hussain.

 Kafin haka ministan ya nakalto korafin da jami’an gwamnatin kasar Amurka suka gabatarwa gwamnatin kasar Iraki na cewa jiragen ruwan kasar Iran na amfani da takardun bugi na kasar Iraki don gudanar da harkokinsu a yankin. Aragchi ya musanta hakan ya kuma kara da cewa gwamnatin kasar Amurka tana son raba JMI da dukkan kasashe makobta don cimma manufofinta na maida kasar Iran saniyar ware a duniya.

Ministocin biyu sun tattauna batun abubuwan da suke faruwa a yankin Asiya ta kudu wadanda suka hada da bautun kissan kiyashin da yahudawan sahyoniyya suke yi a kasar Falasdinu da aka mamaye.

A nashi bangaren ministan harkokin wajen kasar Iraqi ya ce kasar Iraki bada cikin kwancen masu gwagwarmaya a yankin.  Wannan kamar yadda kowa ya sani bukata ce daga kasar Amurka na gwamnatin kasar Iraki ta fidda kanta daga kawancen gwagwarmaya wanda kasar Iran take jagoranta a yankin.

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: gwamnatin kasar kasar Amurka kasar Iraki

এছাড়াও পড়ুন:

Har Kullum Burin Sin Shi Ne Wanzar Da Daidaito Da Cimma Moriya Tare Da Amurka

Har kullum, Sin za ta ci gaba da martaba ka’idojin kare hakkokin kamfanoninta. Duba da cewa manhajar TikTok ta shafe tsawon shekaru tana aiki a Amurka, ta kuma samar da dumbin ayyukan yi ga tarin Amurkawa, tare da bayar da gudummawa ga tattalin arzikin kasar, ya kamata gwamnatin kasar ta baiwa manhajar damar cin gajiya daidai da sauran makamantanta dake kasar. Kamar dai ko da yaushe, burin Sin shi ne wanzar da daidaito da cimma moriyar bai daya tare da Amurka.

 

 

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Har Kullum Burin Sin Shi Ne Wanzar Da Daidaito Da Cimma Moriya Tare Da Amurka
  • Babban Jirgin Ruwan Kasar Sin Ya Nufi Yankin Tekun Kudancin Kasar Domin Gwaji Da Samar Da Horo
  • Iran Ta Gabatar Da Sabbin Kayayyaki Guda 5 A Wajen Taron Kolin kere-kere .
  • Pezeshkian: Saudiyya Na Iya Taka Muhimmiyar Rawa Wajen Samar Da Hadin Kan Kasashen Musulmi
  • ’Yan ‘Mafiya’ na ƙoƙarin kashe matatar man fetur da na gina —Ɗangote
  • Ministan Tsaron Kasar venezuela Ya Gargadi Amurka Dangane Da Kokarin Juyin Mulki A Kasar
  • Pezeshkian: Ya kamata kasashen musulmi su yanke alaka da gwamnatin sahyoniya tare da kiyaye hadin kai
  • Sin Ta Yi Kira Ga Amurka Da Ta Dakatar Da Shuka Kiyayya Da Tashin-Tashina A Tekun Kudancin Sin
  • Fira Ministan Spain: Bai Kamata A Rika Barin “Isr’ila” Tana Shiga Gasar
  • Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Gana Da Takwarorinsa Na Kasashen Qatar, Turkiyya, Pakistan Da Labanon A Doha