Amurka Ta Siyo Man Jiragen Sama Fiye Da Ganga Miliyan 2 Daga Matatar Dangote
Published: 25th, March 2025 GMT
Amurka ta shigo da sama da ganga miliyan biyu na man jiragen sama daga matatar Dangote a watan Maris. Matatar ta tabbatar da hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Talata, inda ta ce hakan ya tabbatar da “nagartar da ba ta misaltuwa” na kayayyakin matatar da kuma aminci da kasashen duniya suka bai wa matatar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: daga matatar Dangote
এছাড়াও পড়ুন:
Sabbin Bayanai Kan Fashe-Fashe Wasu Abubuwa A Tashar Jiragen Ruwan Kasar Iran
Gwamnan lardin Hormozgan (mai hedikwata a Bandar Abbas), Mohammad Ashouri, ya ce wani bangare na lamarin tashar jiragen ruwa na Shahid Raja’i ya faru ne sakamakon keta sanarwar adana kayayyaki ne, wani bangaren kuma na da alaka da sakaci da rashin kulawa (a wajen ajiya).
AShouri, wanda ya bayyana ta hanyar faifan bidiyo a wata hira da aka watsa ta talabijin a yammacin jiya Litinin, ya bayyana sabbin alkaluman wadanda suka bata: Akwai mutanekusan 22 da suka bace, kamar yadda wasu gawarwakin mutane 22 ba a iya tantace su ba ko su waye ba.
Ya ce: “Wasu daga cikin wadanda suka jikkata an hanzarta jigilar su ta jirgin saman soja zuwa asibitin birnin Shiraz.”
Gwamnan lardin Hormozgan na Iran ya ce: An cimma wasu bincike na farko dangane da yiyuwar yin sakaci a wannan fanni, kuma ana gudanar da bincike sosai kan dukkan al’amuran da suka faru. Kuma babu wata daga kafa da za a yi ga duk wanda aka samu da yin sakaci a kan haka za a tuhume shi kamar yadda shari’a ta tanada.
Ya ci gaba da cewa, “Ta hanyar nazarin faifan bidiyo daban-daban na aukuwar lamarin tashar jirgin ruwa ta Shahid Raja’i, an lura da cewa, an yi jigilar kaya a lokacin da lamarin ya faru, inda hayaki ke tashi, sai kuma fashewar wani abu.