HausaTv:
2025-07-09@22:43:50 GMT

Rizai: Mun Harbo Jirage Kanana Da Manya 80 Na ‘Yan Sahayoniya

Published: 9th, July 2025 GMT

Tsohon kwamandan dakarun kare juyin juya halin musulunci na Iran Birgediya  Muhsin Rizai, ya sanar da cewa; Dakarun IRGC sun yi nasarar harbo jirage manya da marasa matuki na HKI har guda 80, kuma da akwai baraguzai 32 daga cikinsu da ake rike da su.

Birgediya Rizai ya kuma kara da cewa; Daga cikin wadanda aka harbo din da akwai samfurin “Hermes” da “Hermon” da sune kira ta karshe da ‘yan sahayoniya suke takama da su.

Birgediya Muhsin Rizai wanda memba ne a majalisar fayyace maslahar tsarin musulinci ta Iran, wanda tashar talbijin ta yi hira da shi da marecen jiya Talata, ya yi Magana akan bangarori da dama na  kallafaffen yakin kwanaki 12 inda ya ce:” Gabanin mu yi bitar yadda yakin ya kasance, ya zama wajibi mu yi Magana akan cewa, farfagandar da su ka yi, saboda matsin lambar da su ka rika fuskanta ne a cikin gida da kuma a Amurka sannan kuma a fagen duniya. Hakika ita ce Isra’ila ta ci kiasa a yakin. Matsin lambar ya kai ga cewa, Trump ya mayarwa da tashar talabijin irin CNN martani da cewa: Karya kuke yi, mun yi nasara.”

Musin Rizai ya kuma ce; Idan mu ka duba akan ko sun yi nasara, ko a’a, za mu yi nazari akan asarar kudade bisa abinda ma’aikatar kudi ta HKI ta fitar. Sun bayyana cewa, sun yi asarar kudaden da sun kai dalar Amurka biliyan 20 a cikin kwanaki 12 kadai. Kuma Na’urorin kakkabo makamai masu linzami samfurin Thaad da aka kera a cikin shekaru biyu,sun kare. A cikin kwanaki 12, sun karar da na’urorin da su ka dauki shekaru biyu suna kerawa.”

Birgediya Rizai ya kuma bayyana yadda na’urorin Rada na Iran su ka dauko hotunan jikkata da kakkabo jiragen abokan gaba 80 daga cikinsu da akwai baraguzai 32 da ake rike da su.”

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamna Yusuf Ya Kaddamar Rabon Na’urorin Rarraba Lantarki 500

A wani yunkuri na bunkasa samar da wutar lantarki da kuma bunkasar tattalin arziki, gwamnatin jihar Kano ta kaddamar da rabon kashi na farko na taransfoma 500 ga al’ummomin karkara a fadin kananan hukumomin jihar 44.

 

Gwamna Abba Yusuf ne ya kaddamar da shi a hukumance a Kano a wani shirin da nufin magance kalubalen rashin samar da wutar lantarki.

 

Gwamna Yusuf ya ce samar da taransfoma wani shiri ne na bunkasa masana’antu da zaburar da harkokin kasuwanci musamman a yankunan karkara.

 

“Wannan rabon shi ne kashi na farko na aikin samar da wutar lantarki a yankunan karkara, ba wai kawai wani aikin samar da wutar lantarki ba ne, wani muhimmin mataki ne na inganta samar da wutar lantarki ga jama’armu. Samar da wutar lantarki mai inganci na da matukar muhimmanci ga ci gaban masana’antu da bunkasar tattalin arziki.”

 

Gwamnan ya bukaci masu ruwa da tsakin al’umma da su mallaki na’urar taransifoma gaba daya, sannan ya umurci shugabannin kananan hukumomin da su kafa kwamitoci don kula da ayyukan da kuma tabbatar da tsaro.

 

Kwamishinan Ma’aikatar Raya Karkara da Cigaban Al’umma Abdulkadir Abdulsalam ya yabawa kokarin Gwamnan na inganta rayuwar al’umma da bunkasa tattalin arzikin karkara.

 

“Wannan rabon na nuna alamar ci gaba da yunƙurin da Gwamna ya yi na tunkarar ƙalubalen da al’ummomin karkara ke fuskanta. Na’urar taransifoma za ta inganta rayuwar jama’a sosai, da inganta tattalin arziƙi, da kuma jawo hankalin masu zuba jari.”

 

Bikin ya samu halartar mataimakin gwamnan jihar Kano, kakakin majalisar dokokin jihar Kano, mai martaba Sarkin Karaye, da manyan jami’an gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki.

 

ABDULLAHI JALALUDDEEN KANO.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Amurka Tana Fatan HKI da Hamas Su Tsaida Budewa Juna Wuta Na Kwanaki 60 A Karshen Wannan makon
  • Iran Za Ta Yi Nazarin Sabuwar Gayyatar Da Amurka Ta Yi Mata Na  Sabuwar Tattaunawa
  • Xi Ya Ajiye Furanni Ga Wadanda Suka Mutu Yayin Yakin Bijirewa Harin Japan
  • Asibiti Mai Zaman Kansa A Kano Zai Fara Manya Manyan Tiyatu Tare Da Rage Kuɗi Kaso 50%
  • Sin Na Bikin Cika Shekaru 88 Da Dukkan Al’ummar Kasar Ta Fara Yakin Kin Jinin Harin Sojojin Japan
  • Gwamna Peter Mbah Ya Ƙaddamar Da Jiragen Kasuwanci 3 Na ‘Enugu Air’ Mallakin Jihar
  • Hizbullah Ta Yi Allawadai Da Harin HKI A Kasar Yemen
  • Gwamna Yusuf Ya Kaddamar Rabon Na’urorin Rarraba Lantarki 500
  • Gwamnatin Kasar Iran Ta Yaba Da Kungiyar BRICS Saboda Yin Tir Da HKI A Yakin Kwanaki 12