Sanarwar ta ƙara da cewa mutane 3,824 da suka yi aiki a ƙarƙashin gwamnatin jiha sun samu N7,960,162,598.64, yayin da 4,833 daga ƙarananan hukumomi aka tantance kuma an biya su N5,983,876,606 a matsayin garatuti. A jimlace, an biya N13,944,039,204.64 a matsayin kuɗaɗen garatuti.

Gwamna Lawal bayan ya karbi rahoton ya ce gwamnatinsa ta ba da fifiko wajen daidaita biyan haƙƙoƙin ma’aikatan gwamnati, musamman waɗanda suka yi ritaya bayan shekaru 35 suna aiki kuma suka kai shekaru 60.

 

“Gwamnatinmu ta gaji sama da Naira Biliyan 13 a matsayin bashin kuɗaɗen garatuti na waɗanda suka yi ritaya daga Jiha da Ƙananan Hukumomin daga 2011 zuwa 2023, jinkirin ya jawo wahalhalu, kuma wasu da suka yi ritaya sun mutu su na jiran a biya su haƙƙin su, Allah ya jiƙan su da rahama.

 

“Don magance wannan rashin adalci, mun kafa kwamitoci guda biyu domin su duba tare da ba da shawarar biyan duk wata garatuti da aka riƙe wa waɗanda suka yi ritaya daga Jiha da Ƙananan Hukumomi, a lokacin da muka karbi ragamar mulki shekaru biyu da suka wuce, duk da ƙalubalen tattalin arziki da zamantakewa, mun biya ma’aikatan gwamnati albashin watanni uku tare da biyan su alawus-alawus. Mun kuma daidaita alawus-alawus na alƙalai da ma’aikatan shari’a na tsawon shekaru.

 

“Mun daidaita duka waɗannan abubuwa. Lokacin da muka karbi mulki, mafi ƙarancin albashi a jihar ya kasance Naira 7,000.00 ne kacal, mafi ƙarancin albashi na N30,000, wanda aka amince da shi a shekarar 2019, gwamnatin da ta shuɗe ba ta taba aiwatar da shi ba, saboda sanin nauyin da ya rataya a wuyanmu, mun aiwatar da mafi ƙarancin albashi na N30,000.00 nan take.

 

“Bayan mun duba tsarin mafi ƙarancin albashin da ya ƙaru daga N30,000 zuwa N70,000.00 a watan Yulin 2024, mun aiwatar da sji bayan duk matakan da suka dace, ta yadda a cikin shekaru biyu na mulki, mun ƙara mafi ƙarancin albashi a jihar daga N7,000.00 zuwa N70,000.00.

 

“Bugu da ƙari kuma, mun bullo da kuma aiwatar da hanyoyin kyautata wa ma’aikata a yayin bukukuwan Sallah da kuma ƙarin garabasar albashin ƙarshen shekara, wanda aka fi sani da albashin wata na 13 ga duk ma’aikatan gwamnati da masu riƙe da muƙaman gwamnati, ba a taba yin hakan ba a tarihin jihar.

 

“Sakamakon biyan kuɗaɗen garatuti ya ƙara wa ma’aikata kwarin gwiwa tare da dawo da amincewar jama’a kan harkokin mulki, za mu ci gaba da tabbatar da samar da kuɗaɗen fansho cikin gaggawa, domin yin hakan, gwamnatin jihar a shirye take ta haɗa gwiwa da ƙungiyoyin ‘yan fansho domin tafiya daidai da sauye-sauyen da muka yi.

“Yayin da nake samun wannan rahoton, ina so in yaba wa ƙoƙari da jajircewar ‘yan kwamitin, wannan ba abu ne mai sauƙi ba, ina sane da ƙalubalen da ‘yan kwamitin suka fuskanta a yayin gudanar da aiki, ba yaba da jajircewarsu.

 

A yayin ƙaddamar da kwamitin aiwatar da ayyukan fansho, gwamnan ya jaddada cewa gwamnatinsa za ta tabbatar da yin garambawul a harkokin fansho na jiha da ƙananan hukumomi.

 

“Gwamnatina ta kafa wani kwamiti da zai duba ayyukan da suka gabata na hukumar fansho a jihar, kwamitin ya kammala aikinsa tare da bayar da shawarwari kan yadda za a ci gaba, wani bangare na shawarwarin shi ne kafa kwamitin aiwatar da ayyukan fansho.

 

“Don bin tsarin Ma’aikatar Shari’a, Hukumar Fansho ta Jiha, da duk masu ruwa da tsaki za su duba tare da sabunta dokar fansho ta Jihar Zamfara domin Majalisar Dokokin Jihar ta amince da ita cikin gaggawa.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: mafi ƙarancin albashi da suka yi ritaya

এছাড়াও পড়ুন:

Kaso 90 na ’yan bindigar da suka addabi Katsina ’yan asalin jihar ne – Radda

Gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda, ya ce kimanin kaso 90 cikin 100 na ’yan bindigar da suka hana jiharsa sakat ba baki ba ne, ’yan cikinta ne.

Ya bayyana haka ne lokacin da ya bayyana a cikin shirin Sunrise Daily na gidan talabijin na Channels a ranar Talata.

Ya ce tuni gwamnatinsa ta kafa rundunar tsaro mallakin jihar mai suna Katsina Community Watch Corps, inda aka debi matasa daga yankunan da ke fama da matsalolin tsaron domin a dakile ta tun daga tushe.

DAGA LARABA: Shin Ko Zafin Nema Na Kawo Samu? Malaman firamare sun janye yajin aiki a Abuja

Katsina dai na daya daga cikin jihohin Arewa maso Yamma da ke fama da matsalar ’yan bindiga, inda mutane dauke da makamai kan kai farmaki kan kauyuka su kashe mutanen gari sannan su dauki wasu domin karbar kudin fansa. Sai dai a ’yan kwanakin nan jihar ta dan samu saukin hare-haren.

A cewar Gwamnan, akasarin maharan ba baki ba ne, a yankunan danginsu suke, inda ya ce amfani da mutanen yankin na taka muhimmiyar rawa wajen shawo kan matasalar tun daga tushe.

Ya ce a sakamakon haka, an sami nasarar kama mutane da dama da ke samar wa da ’yan bindigar kayayyaki da kuma bayanan sirri.

Radda ya ce, “Ba wai cewa muke an ga bayan matsalar tsaro gaba dayanta ba, saboda har yanzu a kan samu hare-hare jifa-jifa, amma dai yanzu an samu sauki.

“A baya akwai wadanda suke tunanin gaba daya jihar ma ta koma hannun ’yan ta’addan saboda kashe-kashen da ake yi a ko ina. Amma wannan tunanin ya saba da abin da yake a zahiri.

“Dalilinmu na kirkirar sabuwar rundunar tsaro ta jiha shi ne mu taimaka wa sauran jami’an tsaro a ayyukansu. Mun dauki mutane daga dukkan yankunan da ke da matsalolin tsaro saboda su suka fi sanin yankunansu da ma mutanen cikinsa fiye da kowa.

“Mazauna wadannan yankunan sun san iyayen ’yan bindigar nan da kakanninsu, saboda ba baki ba ne. wannan ne sirrin samun nasararmu, har muke iya zuwa mu farmake su a har a maboyarsu. Dole sai da dan gari a kan ci gari,” in ji Gwamnan na Katsina.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kwanan nan gwamnati za ta sake kara kudin lantarki a Najeriya – Minista
  • Na Biya Dukkanin Bashin Da ‘Yan Fansho Ke Bin Zamfara- gwamna Lawal
  • Sin Ta Ware Yuan Biliyan 10 Don Shirye-Shiryen Ba Da Tallafin Aiki
  • Kaso 90 na ’yan bindigar da suka addabi Katsina ’yan asalin jihar ne – Radda
  • ‘ADC za ta mayar da APC jam’iyyar adawa a 2027’
  • ASUU Ta Tsunduma Yajin Aiki A Faɗin Nijeriya
  • Gwamna Peter Mbah Ya Ƙaddamar Da Jiragen Kasuwanci 3 Na ‘Enugu Air’ Mallakin Jihar
  • Hukumar Kula da Muhalli ta Jihar Jigawa ta Kwace Gurbatattun Kayayyaki na Miliyoyin Naira
  • Kano ta sami rahoton cin zarafin yara 351 – NHRC