Tinubu ya fi damuwa da siyasa sama da rayukan ’yan Najeriya — ADC
Published: 6th, October 2025 GMT
Jam’iyyar ADC ta zargi Shugaba Bola Ahmed Tinubu da rashin mayar da hankali kan yadda matsalar tsaro ke ƙara taɓarɓarewa a ƙasar nan.
Jam’iyyar ta ce shugaban yaf i damuwa 2ajen halartar tarukan siyasa da biki, maimakon kare rayukan ’yan Najeriya.
Ɓarayin daji sun kashe kwamandan maharba a Kaduna Mata da yara 95,000 ke mutuwa a sanadin shaƙar hayaƙin girki — Uwargidan FubaraA cikin wata sanarwa da mai magana da yawun jam’iyyar, Mallam Bolaji Abdullahi, ya fitar, ADC ta ce maganar da Shugaba Tinubu ya yi a Cocin COCIN a Jos, na batun haɗa kan ‘yan Najeriya, ba komai ba ne illa siyasa kawai.
Jam’iyyar ta ce tun da ya hau mulki, ba a ga wani mataki da ke nuna yana son haɗa kan al’umma ba.
ADC, ta ce Najeriya tana fuskantar mummunar barazana daga ’yan bindiga, don haka ta buƙaci gwamnati ta ɗauki mataki cikin gaggawa domin wanzar da zaman lafiya.
“ADC na cikin damuwa sosai saboda yadda Shugaba Tinubu ke nuna rashin damuwa da yadda matsalar tsaro ke ƙara ta’azzara a ƙasar nan,” in ji sanarwar.
Jam’iyyar ta soki sugaban saboda ci gaba da halartar bukukuwa da tarukan siyasa, alhali ana kashe mutane da yin garkuwa da su a sassan ƙasar.
ADC ta kafa misali da yadda ’yan bindiga suka addabi ƙananan hukumomi tara a Jihar Kwara, inda mahara ke tilasta wa mazauna yankunan bayar da abinci, abin sha, da kuɗi a matsayin fansa.
Jam’iyyar ta ce wannan babban gazawa ce ta gwamnati, kuma har yanzu fadar shugaban ƙasa ba ta ɗauki mataki ba.
Har ila yau, ta sake kafa misali da Jihar Kogi, inda ’yan bindiga suka kashe fasinjoji tare da sace mata da yara.
Ta ƙara da cewa sama da makarantu 180 a Arewacin Najeriya aka rufe saboda rashin tsaro, lamarin da ya tilasta wa gomman yara zaman gida.
Jam’iyyar ta ce irin waɗannan abubuwa suna faruwa kusan a dukkanin sassan ƙasar nan; daga Filato zuwa Zamfara, Benuwe zuwa Neja, Kaduna zuwa Kwara, inda ake yawan kashe mutane da yin garkuwa da su.
Duk da haka, Gwamnatin Tarayya tana ci gaba da cewa tana samun “ci gaba.”
ADC ta ce wannan magana ba ta dace ba saboda ana ci gaba da zubar da jinin al’umma.
Sanarwar ta ƙara da cewa yayin da al’umma a karkara ke tserewa daga gidajensu, ake rufe makarantu, Shugaba Tinubu yana halartar bukukuwa da jana’izar ’yan siyasa.
A cewar ADC, wannan yana nuna cewa ya fi damuwa da harkokin siyasa sama da rayukan ’yan ƙasa.
Haka kuma, ta soki yadda Tinubu yake zama a fadar gwamnati yana aike saƙon ta’aziyya bayan kisan jama’a, maimakon ɗaukar mataki tun kafin irin waɗannan hare-hare su auku.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: yan Najeriya Rayuka Siyasa Tsaro Jam iyyar ta ce
এছাড়াও পড়ুন:
Ɗan bindiga ya harbe sojoji 2 a fadar shugaban Amurka
An kulle Fadar Shugaban Kasar Amurka ta White House tare da wasu gine-ginen gwamnati da dama, sakamakon harbin ɗan bindigar da ya raunata sojoji biyu a kusa da fadar.
A yayin, an harbe masu tsaron fadar biyu har lahira.
Gwamna Patrick Morrisey da farko ya ce an kashe sojojin, amma daga baya ya ce yana samun “rahotanni masu karo da juna” game da halin da suke ciki, yana mai da cewa za a fitar da ƙarin bayani idan an tabbatar.
A cikin wani rubutu a shafin X, ya ce, “Yanzu muna samun rahotanni masu cin karo da juna game da halin sojojin biyu, kuma za mu bayar da ƙarin bayani idan mun samu cikakken rahoto.
“Addu’o’inmu suna tare da waɗannan jarumai, iyalansu, da dukan al’ummar Amurka.”
A cewar rahotanni, Shugaba Donald Trump yana gidansa na hutu a Mar-a-Lago da ke Palm Beach, Florida, a lokacin da lamarin ya faru.
Mai magana da yawun Fadar White House, Karoline Leavitt, ta ce cikin wata sanarwa: “Fadar White House ta san da wannan mummunan lamari kuma tana bin diddigi. Shugaban kasa ya samu cikakken bayani.”
’Yan sandan birnin Washington DC sun ce an kama wanda ake zargi da harbin.
Sojojin National Guard sun kasance a Washington DC tsawon watanni a matsayin wani bangare na matakin Trump na yaki da laifuka a babban birnin ƙasar.
A cikin wani rubutu a dandalinsa na Truth Social, Trump ya ce: “Dabban da ya harbi mambobin National Guard biyu, wanda dukkansu suka ji rauni mai tsanani kuma yanzu suna a asibitoci daban-daban, shi ma ya ji rauni sosai, amma duk da haka, zai ɗanɗana kuɗarsa.”