Gwamnan Bayelsa ya fice daga jam’iyyar PDP
Published: 15th, October 2025 GMT
Gwamnan Jihar Bayelsa, Sanata Douye Diri, ya fice daga jam’iyyar PDP.
Mai magana da yawun gwamnan, Daniel Alabrah, ne ya sanar da hakan a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook na ainihi, kodayake bai bayyana dalilin ficewar gwamnan daga jam’iyyar ba.
Har ila yau, bai bayyana ko Gwamna Diri zai koma APC mai mulki ko kuma hadakar ’yan adawa ta ADC ba.
Aminiya ta gano cewa Gwamna Diri yana halartar wani taro da mambobin majalisar zartarwa ta jiha, inda ya bayyana musu wannan bayani.
Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Bayelsa, Rt. Hon. Abraham Ingobere, yana cikin mahalarta taron.
A cikin sa’o’i kaɗan da suka gabata, Gwamna Diri tare da tsohon Shugaban Ƙasa, Goodluck Jonathan, sun halarci bikin ƙaddamar da otal ɗin Best Western Plus da ke Yenagoa.
Haka kuma, dukkan mambobin PDP da ke cikin Majalisar Dokokin Jihar da kuma Kwamishinoni a Majalisar Zartarwa ta Jiha sun fice daga jam’iyyar.
Gwamna Diri ya taɓa zama Kwamishina a gwamnatin PDP a lokacin da Goodluck Jonathan ke matsayin Gwamnan Jihar Bayelsa. Haka kuma, ya kasance Babban Sakataren Gwamna Seriake Dickson, wanda shi ne wanda ya gabace shi.
An zaɓi Diri a matsayin ɗan Majalisar Wakilai a shekarar 2015 a ƙarƙashin PDP, sannan a 2019 aka zaɓe shi a matsayin Sanata mai wakiltar Bayelsa ta Tsakiya.
A shekarar 2020 aka zaɓe shi a matsayin Gwamnan Jihar Bayelsa, kuma aka sake zaɓar shi a 2023, duka a ƙarƙashin jam’iyyar PDP.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Bayelsa daga jam iyyar Jihar Bayelsa Gwamna Diri
এছাড়াও পড়ুন:
Jihar Kwara Ta Jaddada Kudirin Tallafa wa Wadanda Suka Tsira Daga Cin Zarafin Jinsi
Gwamnatin Jihar Kwara ta jaddada kudirinta na ba da ingantaccen kulawa da kuma ƙarfafa matakan rigakafi ga waɗanda suka tsira daga cin zarafin jima’i da na jinsi (SGBV) a fadin jihar.
Kwamishiniyar Harkokin Mata, Hajiya Opeyemi Afolashade, ce ta bayyana haka yayin ziyarar sa ido da tantance ayyuka a Cibiyoyin Tallafawa Wadanda Aka Yi wa Cin Zarafi (SARCs) da ke Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jihar Kwara (KWASU) a Ilorin da kuma Asibitin Kwarari ta Sobi da ke Alagbado.
Kwamishiniyar ta bayyana cewa cibiyar an kafa ne tare da hadin gwiwar ofishin Uwargidar Gwamna, domin jinya kyauta da kuma kwantar da hankali, da tallafi ga wadanda suka tsira daga cin zarafi a jihar.
Afolashade ta ƙara da cewa bincike da tantancewar da ake yi yanzu zai taimaka wajen tantance ingancin kulawar da ake bayarwa, da gano wuraren da ake bukatar gyara domin samar da tsarin taimako mai inganci da niyya kai tsaye ga masu bukata.
Ta kuma jaddada bukatar ƙara haɗin gwiwa da masu ruwa da tsaki tare da horar da ma’aikatan cibiyoyin SARC a fannin tattara bayanai da bayar da rahoto domin inganta tsarin tallafi ga wadanda suka tsira daga cin zarafin jinsi.
Ali Muhammad Rabiu/Ilorin