Tsohon Shugban Kasar Dimokaradiyyar Kwango Ya Koma Kasarsa Domin Kalubalantar Hukuncin Kisa Da Aka Yanke Kansa
Published: 18th, October 2025 GMT
Tsohon shugaban Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango ya dawo kasarsa daga Nairobi domin kalubalantar hukuncin kisa da aka yanke masa
A wani gagarumin ci gaba na siyasa, tsohon shugaban kasar Kwango Joseph Kabila, ya bayyana a bainar jama’a a Nairobi babban birnin kasar Kenya, bayan da a makonnin da suka gabata wata kotun soji a kasarsa ta yanke masa hukuncin kisa bisa zargin “cin amanar kasa da laifuffukan yaki.
Wannan lamari ya faru ne kwatsam da ya haifar da cece-kuce a fagen siyasa da kafofin watsa labarai, musamman ma dai a daidai lokacin da Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango ke fama da rikicin tsaro da na siyasa.
Kabila wanda ya mulki kasar a tsakanin shekarar 2001 zuwa 2019, ya jagoranci wani taron da aka bayyana a matsayin “rufeffen taron” na tsawon kwanaki biyu tare da wasu fitattun ‘yan adawar Kwango.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label Name* Email* Website Label Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Gaza Ta Bukaci A Binciki Isra’ila Kan Sace Sassan Jiki A Gawarwakin Falasdinawa October 18, 2025 Hamas Ta Bukaci A Kafa Kotun Kasa Da Kasa Kan Gawarwarkin Da Isra’ila Ta Dawo Mata Da Su. October 18, 2025 Madagascar : An rantsar Da Michael Randrianirina A Matsayin Shugaban Kasar October 18, 2025 Iran Ta yi Tir Da Harin da Isra’ila Ta kai Kudancin Kasar labanon. October 18, 2025 Majalisar Dattawa Za Ta Gana Da Ministan Ilimi Kan Batun Yajin Aikin Asuu. October 18, 2025 Gaza ta bukaci a binciki Isra’ila kan sace sassan jiki a gawarwakin falasdinawa October 18, 2025 Madagaska : An rantsar da Kanar Randrianirina a matsayin shugaban kasa October 18, 2025 Al-Houthi: Matsin lamba bai hana Iran ci gaba da goyon bayan Falasdinu ba October 18, 2025 Marzieh Jafari Ta Dauki Lambar Yabo Ta Horar Da Mata Wasan Kwallon Kafa Ta Nahiyar Asia October 18, 2025 Iran: Kudurin Kwamitin Tsaro Kan Yarjeniyar JCPOA Ya Kawo Karshe A Yau October 18, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Kotu ta daure kocin kwallon kafa a Kano shekara 8 saboda aikata luwadi
Babbar Kotun Jihar Kano ta yanke wa wani kocin ƙungiyar ƙwallon ƙafa hukuncin daurin shekaru takwas ba tare da zaɓin tara ba, kan laifin luwadi da ɗan wasan kulob dinsa mai karancin shekaru.
Kotun dai wacce ke ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Musa Dahuru Muhammad a ranar Laraba ta sami kocin mai suna Hayatu Muhammad da aikata laifin.
Tinubu na ƙoƙarin mayar da Najeriya mai jam’iyya ɗaya — ADC Majalisar Dattawa za ta tantance Amupitan a ranar AlhamisWanda aka yanke wa hukuncin, mazaunin unguwar Sanka ne a ƙaramar hukumar Dala, kuma kotun ta tabbatar da cewa ya aikata laifin har sau biyu a wurare daban-daban.
Da farko dai ya musanta zargin da ake masa.
Sai dai, bayan tabbatar da laifin ba tare da wata shakka ba, lauya mai gabatar da ƙara daga Gwamnatin Jihar Kano, Ibrahim Arif Garba, ya kira shaidu guda biyar da suka ba da shaida a kotu.
A bangarensa, wanda ake tuhuma shi kaɗai ne ya ba da shaida don kare kansa.
Bayan nazarin dukkan shaidun da aka gabatar da kuma bayanan shaidu, Mai Shari’a Dahuru ya tabbatar da cewa wanda ake tuhuma ya aikata laifin kamar yadda aka zarge shi.
Alkalin ya yanke masa hukuncin daurin shekara huɗu kan kowacce tuhuma, kuma ya bayar da umarnin cewa hukuncin zai fara ne tun daga ranar da aka yanke hukuncin.