Leadership News Hausa:
2025-10-19@19:04:17 GMT

Yadda Shagwaɓa Kananan Yara Da Kudi Ke Shafar Tarbiyyarsu

Published: 19th, October 2025 GMT

Yadda Shagwaɓa Kananan Yara Da Kudi Ke Shafar Tarbiyyarsu

Sunana Aisha Isah Abubakar (Mai Waka) Gama:

A gaskiya bawa yara kanana kudi wannan ba dabi’a ce mai kyau ba, saboda wata rana idan babu wannan kudi da aka sabawa yaro da shi wallahi illa ce babba. Sabida yau da gobe sai Allah idan suka rasa wannan kudi komai zai iya faruwa za su iya saka hannu su diba ako’ina, saboda su biya wa kansu bukatar su.

Shawara ya kamata masu dabi’ar aiken yara su basu kudi dan Allah su daina, gara ku siyi ‘sweet’ idan yaro ya dawo a bashi ya fi a dauki kudi a bashi. Allah ya sa mu dace.

 

Sunana Aminu Adamu, Malam Maduri A Jihar Jigawa:

To magana ta gaskiya sam-sam hakan bai dace ba, domin yana da kyau idan iyaye za su bawa yara kudi to, su san me za su yi da kudin kafin ma su amince su bada, don haka zai taimaka wajen kula da tarbiyyar yaro. Eh gaskiya akwai, kamata yayi sai shekarun yaro sun kai na sanin abin da ya kamata da wanda bai kamata ba sannan a fara bashi kudi, domin ya kashe. Kuma ko da za a fara bashi ya kamata a san me zai yi da shi, kuma ana bibiyar sa akan abun da ya ce shi yayi. To, shawara ta a nan ita ce ya kamata iyaye suna taka-tsam-tsan wajen bawa yaransu kudi a kodayaushe ba tare da dalili na gaske ba.

 

Sunana Hafsat Sa’eed, Jihar Naija:

Wasu ya danganta da yanayin basu kudin da suke wasu suna ganin gata ne, wanda hakan ba gata bane har a guri na, misali ni inada yara mata to, ba na kokarin na ga na basu kudi sai na tabbatar da abin da za su yi me mahimmanci ko kati ko wano kwadayi yaro yana zaune yana sha’awar wani abu. Tunda matsayinka na uwa ba sana’a ka dorawa yaro ba dole za ka nema ka bashi. To, amma a haka kawai ka ce kana bawa yaro kudi dan jin dadi, wannan sangartawa ne, kuma hakan yakan iya janyiwa yaro shiga wani yanayi idan ya rasa kudi a wannan lokacin. Ni dai ina ganinba burgewa bane ko gata.

 

Sunana Sadi Dauda Baturiya, Kramar hukumar Kirikasamma Jihar Jigawa A Nijeriya:

A gaskiya har yanzu wasu iyayen suna gangancin sakarwa ‘ya’yansu, musamman yara kanana mara wajen ba su kudi ba tare da duba yanayi da kuma hankalin yaro ba, wanda kuma hakan yana haifar da matsaloli da dama. Matakan da ya kamata a dauka su ne, za a iya bai wa yaro karami kudi amma wanda bai fa sayi minti ko biskit ko madara da sauran ababen makulashe ya danganta da waje. Ni ganau ne ba jiyau ba na sha ganin yara da matasa da aka sakarwa mara wajen ba su kudi masu yawa da sunan soyayya, a karshe suka zama ‘yan shaye-shaye wasu kuma suka zama masu bin matan banza, wasu matasan ma gidan haya suke kama wa suna dauko matan banza, Allah Ya shirya mana matasannmu, da mu bakidaya amin.

 

Sunana Princess Fatimah Mazadu, Goben Nijeriya:

Wannan abu ne wanda ke gurbata tarbiyyar yara, wadanda ba a isa a saka su ko a hana su ba, dan gani suke kudi sune komai. Iyaye yara amana ce a garesu da su basu tarbiyya, saboda su yi alfahari da su ranar gobe kiyama, ba a hana ka bawa danka ba. Amma akwai hanyoyi da dama wanda za ka bayar wanda ba za a kira lalata tarbiyya ko sangarta yaro ba. Shekarun da hankalin yaro ake fara dubawa kan asakar masa manyan kudade gudun rudin duniya da lalacewa.

 

Sunana Muhammad Isah, Zareku Miga A Jihar Jigawa:

Eh magana ta gaskiya bata yaro ne, ana bashi kudi tun yana da karancin shekaru domin akwai illoli/matsala idan har ya saba da bashi kudi yana yaro. Matakin shi ne yaro ya kai shekarun sannin shi waye ne ma’ana ya san daidai komai kankanta ko ya san babu da rashi. Shawarar a nan ita ce; iyaye su daina bawa yara kudi suna yara ba tare da sun wakilta wani ‘ya’yansu ko antin su ba idan bukatar hakan ta tashi.

 

Sunana Hassana Yahaya Iyayi, Jihar Kano:

Wannan ba gata bane lalata yaro ne, kuma daga baya su iyayen abin yake shafa. In ya yaro ya mallaki hankalinkansa ya san ciwon kansa, dan bashi dan abin da zai bukata ba laifi bane. Su yi karatun ta-nutsu tun wuri, su daina tun lkan yansu su fada shaye-shaye, ato karshen kenan.

 

Sunana Muktari Sabo, Jahun Jihar Jigawa:

Hakika akwai iyayen da suke sangarta ‘ya’yansu da kudi don nuna gata hakan kuma yana illa sosai, daga illolin shi ne; idan bai samu ba yana iya daukar na wani, haka kuma kudin suna iya sa yaro ya lalace kamar shaye-shaye wani lokaci har da kula matan da ba sa’anninsa ba. Matakin shi ne ya cika hankali kamar yadda addini ya tanada idan har kudin yana da yawa, amma ba laifi bane a bashi dan kadan. Lalle ya kamata iyaye su kula da yaransu, kuma su san irin abin da ya kamata su bawa ‘ya’yansu don bukatarsu.

 

Sunana Comr, Nr. Ibrahim Lawan Stk:

Wannan ba wani abu bane face hanyar lalata tarbiyyar su da kuma samar da gurbacewar zamantakewar irin ta malam bahaushe tare da koyarwar addinin musulunci. Eh tabbas akwai, wannan mataki kuwa shi ne lokacin da yaro ya girma ya mallaki hankali sannan ya san ciwon kansa ya kuma san ciwon yadda ake samun kudi da nemansa da kuma ciwon rashinsa, ta yadda ba zai yi almubazaranci ba. Su kasance masu kula da tarbiyyar yaransu a lokacin da suke basu kudi, sannan su tabbatar da cewa kafin ma su basu kudin sun mallaki hankalisu ta yadda ba za su almubazaranci ba. Kuma su kashe kudi ta hanya mai kyau, domin samin dacewar rayuwa mai kyau a nan gaba

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Taskira Tsokaci A Kan Mata Masu Tsananin Kishi October 12, 2025 Taskira Illolin Da Ke Tattare Da Mallaka Wa Kananan Yara Wayar Hannu October 4, 2025 Taskira Bukatar Mutane Su Kula Da Warin Jikinsu September 27, 2025

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Jihar Jigawa

এছাড়াও পড়ুন:

Majalisar Dokokin Jihar Kaduna Za Ta Kafa Dokar Wuraren Tsaro A Makarantu

Majalisar Dokokin Jihar Kaduna ta fara aiki kan dokar da za ta kafa wuraren tsaro (safe spaces) a makarantu domin karfafa ilimin yara mata a jihar.

Shugaban Kwamitin Ilimi, Honarabul Mahmud Lawal, ya bayyana hakan a babban taro kan Ilimin Yara Mata  da aka gudanar a Zariya, wanda Cibiyar Kula da Ilimin Yara Mata (CGE) ta shirya don tunawa da Ranar Yara Mata ta Duniya ta 2025.

Ya ce dokar, mai taken “Dokar Wuraren Tsaro a Jihar Kaduna, 2025,” za ta kare ‘yan mata daga cin zarafi, hana wariya, da samar da tsarin horaswa da rahoto a makarantu.

Daraktar CGE, Hajiya Habiba Mohammed, ta ce taron na da nufin kara karfafa ‘yan mata a matsayin shugabannin da za su kawo sauyi, musamman a lokacin rikice-rikice da suke fuskantar kalubale irin su aure da wuri da barin makaranta.

 

Ta ce cibiyarsu na ganin ilimi a matsayin makamin da zai bai wa ‘yan mata damar canza al’umma, kuma dokar majalisar za ta taimaka wajen tabbatar da shirye-shiryen su a makarantu.

A jawabinsa a wurin taron, Shugaban Jami’ar Ahmadu Bello (ABU), Farfesa Adamu Ahmed, ya yaba da taken taron, yana mai cewa ya dace da kalubalen da ‘yan mata ke fuskanta.

Ya ce daya cikin kowanne ‘yan mata hudu a yankin na yin aure kafin shekaru 18, kuma har yanzu ba su da daidaiton damar ilimi kamar maza.

Farfesa Ahmed ya bayyana cewa ABU na kara yawan ‘yan mata da take karɓa, inda suka kai kashi 42 cikin 100, tare da kira ga gwamnati da masu ruwa da tsaki su kara zuba jari a ilimin ‘yan mata.

 

Ibrahim Suleiman

 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Tawagar Likitocin Sin Ta Samar Da Tallafin Jinya Ga Kananan Yara Kyauta A Togo
  • Yadda Ake Alkaki
  • An Fara Yi Wa Yara Miliyan 1.6 Rigakafi A Taraba
  • Gwamnan Katsina Ya Bukaci Al’umma Su Hada Hannu Da Gwamnati Wajen Kawar Da Matsalar Tsaro
  • Fitar Da Kudi Ta Haramtacciyar Hanya Na Kara Dagula Matsalar Tattalin Arziki – IMF
  • Majalisar Wakilai Ta Gayyaci CBN Da Bankuna Kan Cire Wa Kwastomomi Kudi Ba Dalili
  • NIEPA Ta Jinjinawa UNICEF Bisa Kare Hakkokin Yara Na Samun Ilimi A Najeriya
  • Gwamnan Gombe ya ƙaddamar da shirin tallafa wa karatun yara mata
  • Majalisar Dokokin Jihar Kaduna Za Ta Kafa Dokar Wuraren Tsaro A Makarantu