Aminiya:
2025-10-16@09:00:51 GMT

Tinubu na ƙoƙarin mayar da Najeriya mai jam’iyya ɗaya — ADC

Published: 16th, October 2025 GMT

Jam’iyyar ADC ta ce sauya sheƙar da wasu gwamnonin jihohi suka yi zuwa jam’iyya mai mulki ya nuna yadda Shugaba Bola Tinubu, ke ƙoƙarin mayar da Najeriya ƙasa mai jam’iyya ɗaya.

A wata sanarwa da Bolaji Abdullahi, mai magana da yawun jam’iyyar na ƙasa, ya fitar, ya ce jam’iyyun adawa ba su damu da abin da ya kira “cin amanar siyasa” da gwamnonin suka yi ba.

Gwamna Inuwa ya naɗa sabbin shugabanni a ma’aikatar lafiya ta Gombe Ba za mu yi sulhu da ’yan bindiga ba sai sun yi tuba na gaskiya — Radda

Ya ce zaɓen 2027 ba zai zama takara tsakanin jam’iyyu kawai ba, sai dai ya zama gwagwarmaya tsakanin talakawan Najeriya da gwamnatin da ta jefa rayuwar talakawa cikin wahala.

Abdullahi, ya bayyana cewa komawar gwamnonin jihohin Enugu da Bayelsa zuwa jam’iyyar APC, ta tabbatar da cewa Shugaba Tinubu, na da niyyar raunana dimokuraɗiyya da jam’iyyun adawa a ƙasar nan.

Ya ƙara da cewa duk da cewar gwamnonin sun koma jam’iyya mai mulki a zahirin gaskiya sun bar jama’arsu ne tare da komawa jam’iyyar da ta gaza ciyar da ƙasa gaba.

A cewar Abdullahi, ’yan Najeriya da dama suna cikin wahala saboda gazawar gwamnatin APC, hauhawar farashin kayan abinci, rashin ayyukan yi, matsalar tsaro, rashin ingantaccen tsarin kiwon lafiya, da cin hanci da rashawa.

Ya ce ’yan Najeriya sun yi tsammanin gwamnonin adawa za su yi tsayin daka su kare jama’a da kawo mafita, amma maimakon haka, wasu daga cikinsu sun shiga jam’iyyar mai mulki saboda son rai.

Abdullahi, ya kuma ce duk da APC na murna da samun waɗancan gwamnoni, ADC da sauran jam’iyyun adawa suna farin ciki saboda yanzu ’yan Najeriya za su iya gane waɗanda za su tsaya domin ceto ƙasar nan.

Ya ƙarƙare da cewa zaɓen 2027 zai zama takara kai-tsaye tsakanin talakawan Najeriya da gwamnatin Shugaba Tinubu ta jam’iyyar APC.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: adawa Gwamnoni Sauya Sheƙa

এছাড়াও পড়ুন:

NAJERIYA A YAU: Yadda Cire Darasin Lissafi Zai Taimakawa Dalibai Shiga Jami’a

More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba

Cire darasin Lissafi daga jerin wajibcin da ake buƙata domin samun shiga manyan makarantu ya samu karɓuwa daga wasu ɓangarori na dalibai da malamai. Wasu dalibai sun nuna farin ciki da wannan mataki, suna ganin zai sauƙaƙa musu damar samun shiga jami’a da sauran manyan makarantu ba tare da shan wahalar lissafi ba.

 

Sai dai wasu masana sun bayyana cewa, duk da wannan sauƙin, ya kamata a yi taka-tsantsan saboda lissafi na taka muhimmiyar rawa wajen gina tunani da fahimtar ilimin fasaha, kimiyya da injiniya. Wannan ya sa ake tambaya ko cire lissafi daga wajabcin shiga manyan makarantu ba zai iya rage ingancin dalibai a nan gaba ba.

NAJERIYA A YAU: Shin Babu Wata Hanyar Magance Matsalolin ASUU Ne Sai Yajin Aiki? DAGA LARABA: Shin Ko Jam’iyyar PDP Ta Fara Gushewa Ne?

Wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba a kai.

Domin sauke shirin, latsa nan

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Ka da a ɗora wa Tinubu laifin rikicin da ke faruwa a PDP — Fayose
  • Isra’ila ta taƙaita shigar da kayan agaji Gaza
  • NAJERIYA A YAU: Yadda Cire Darasin Lissafi Zai Taimakawa Dalibai Shiga Jami’a
  • Yajin Aikin: Ɗalibai Sun Bai Wa ASUU Da Gwamnatin Tarayya Wa’adin Kwana 7 Su Warware Rikicinsu
  • 2027: Babu Ɗan Siyasar Da Zai Iya Ƙalubalantar Tinubu — Fadar Shugaban Ƙasa
  • Shugaba Tinubu Ya Taya Super Eagles Murnar Samun Cancantar Shiga Gasar Kwallon Kafa Ta Duniya
  • DAGA LARABA: Shin Ko Jam’iyyar PDP Ta Fara Gushewa Ne?
  • NAJERIYA A YAU: Shin Babu Wata Hanyar Magance Matsalolin ASUU Ne Sai Ta Yajin Aiki?
  • Dan Majalisar Tarayyar Kaduna ya bar Jam’iyyar PDP