Aminiya:
2025-10-16@11:28:05 GMT

Ka da a ɗora wa Tinubu laifin rikicin da ke faruwa a PDP — Fayose

Published: 16th, October 2025 GMT

Tsohon Gwamnan Jihar Ekiti, Ayodele Fayose, ya ce bai dace a ɗora wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu, laifin rikicin da jam’iyyar PDP ke fama da shi ba.

Ya bayyana haka ne yayin hira da gidan talabijin na Channels a ranar Laraba, inda ya ce shugabannin PDP ne suka haddasa matsalolinsu, ba Tinubu ko jam’iyyar APC ba.

Kotu ta daure kocin kwallon kafa a Kano shekara 8 saboda aikata luwadi NAJERIYA A YAU: Yadda Cire Darasin Lissafi Zai Taimakawa Dalibai Shiga Jami’a

A cewarsa, jam’iyyar PDP “ta mutu tun tuni,” kuma ba ya cikin waɗanda za su nemi farfaɗo da ita.

Ya ƙara da cewa yawancin gwamnonin da suka rage a PDP na shirin komawa jam’iyyar APC mai mulki.

“Ba daidai ba ne a zargi Tinubu saboda ficewar Gwamnan Jihar Enugu, Peter Mbah, da Gwamnan Jihar Bayelsa, Douye Diri, zuwa APC,” in ji Fayose.

“Su da kansu suka yanke shawara saboda PDP ta rasa shugabanci da tsari.”

Fayose, wanda ya mulki Ekiti sau biyu ƙarƙashin jam’iyyar PDP, ya ce jam’iyyar ta kasa koyon darasi daga kurakurenta na baya, kuma ya sa ta zama mai rauni.

Ya kuma zargi wasu shugabannin PDP da yin siyasa don amfanin kansu maimakon ci gaban jam’iyyar gaba ɗaya.

Maganganunsa na zuwa nedaidai lokacin da ake cece-ku-ce a Najeriya kan yiwuwar komawa tsarin jam’iyya ɗaya, yayin da wasu jiga-jigan jam’iyyun adawa ke ci gaba da komawa APC gabanin zaɓen 2027.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Ɗora Laifi Fayose Sauya Sheƙa Siyasa

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamnan Enugu Peter Mbah da kwamishinoninsa sun koma APC

Gwamna Peter Mba na Jihar Enugu da kwamishinoninsa da sauran mukarrabansa sun sauya sheka daga Jam’iyyar PDP zuwa APC mai mulki.

Da yake sanar da hakan a ranar Talata a garin Enugu, Gwamna Mbah ya jaddada aniyarsa ta kare muradun jihar, tare da bayyana kwarin gwiwa cewa APC za ta ba wa jihar karin damar hadin gwiwa domin samun ci-gaba.

Mbah, wanda ya samu rakiyar magabacinsa, tsohon Gwamna Ifeanyi Ugwanyi, da ’yan  majalisar dokokin jihar da takwarorinsu na Majalisar Dokoki ta Kasa ya ce sun yi ittifafkin komawa APC ne domin kara hidimta wa al’ummar jihar da kuma kare manufofinta na ci gaba.

“Bayan tsawon lokaci ana ta nazari, a yau dai, mun yanke shawarar sauya sheka daga PDP zuwa APC. Wajibi ne mu ci gaba a kan muradunmu na ci gaba.

’Yan Majalisar Tarayyar Kaduna 3 sun sauya sheka daga PDP Sakin Maryam Sanda shi ne ƙololuwar zalunci —Dangin Bilyaminu

“Na fahimci cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu, abonkin tafiya ne ta fuskar manufa, kuma jajirtaccen mutun ne mai hangen nesa da ke daukar matakan da za su amfane mu a na gaba,” in ji shi.

Ya ci gaba da cewa, “Wannan shawara ce a muka dauka a dunkule — ’yan majalisar dokokin jiha da majalisar dokoki ta kasa da Majsaliar Zartaswa ta jiha daukacin shugabannin kananan hukumomi da masu rike da mukaman siyasa da kimanin kashi 80 na shugabannin jam’iyya.”

Duk da cewa ya bayyana godiya ga PDP da gudummawarta a lokacin zabensa, amma ya koka da cewa “yawanci ba a sauraron muryarmu” idan wani sha’ani ya taso da ya shafi yankin Kudu maso Gabas.

Ya bayyan kwarin gwiwa cewa hadewarsa da APC zai taimaki ci-gaban Jihar Enugu da ma Najeriya baki daya.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamnan Edo Ya Umarci Kwamishinoni Su Riƙa Sanya Hular Tinubu
  • Sauya Sheƙa: Diri Da Wasu Na Guje Wa Matsalolin Da Suka Ƙirƙiro – Dickson
  • Kotu ta daure kocin kwallon kafa a Kano shekara 8 saboda aikata luwadi
  • Tinubu na ƙoƙarin mayar da Najeriya mai jam’iyya ɗaya — ADC
  • Gwamnan Bayelsa ya fice daga jam’iyyar PDP
  • Gwamnan Enugu Peter Mbah da kwamishinoninsa sun koma APC
  • Amnesty International Ta Soki Tinubu Kan Yi Wa Masu Laifin Take Haƙƙin Ɗan Adam Afuwa
  • Dan Majalisar Tarayyar Kaduna ya bar Jam’iyyar PDP
  • Rikicin kabilanci: Mutane 2 sun mutu, wasu 7 sun jikkata a Jigawa