Bugu da kari, Xi Jinping ya yi wa jam’iyyar WPK fatan samun karin nasarori, yana mai fatan abotar Sin da Korea ta Arewa za ta dore har abada. (Fa’iza Mustapha)

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin An Jinjinawa Tallafin Kamfanonin Sin Ga Tsarin Bunkasa Masana’antun Senegal October 9, 2025 Daga Birnin Sin Masu Kallon Fina-Finai Na Sin Sun Gamsu Da Fina-Finan Da Aka Gabatar A Lokacin Hutun Bikin Murnar Ranar Kafuwar Sabuwar Kasar Sin Ta 2025 October 9, 2025 Daga Birnin Sin Sin Na Ci Gaba Da Goyon Bayan Kawo Karshen Rikicin Gaza October 9, 2025.

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Ko sisi ba a biya ’yan bindiga ba kafin su saki ɗaliban da suka sace – Gwamnan Kebbi

Gwamnan Jihar Kebbi, Nasiru Idris, ya ce ko sisi gwamnati ba ta biya waɗanda suka yi garkuwa da ɗalibai mata 25 na sakandaren gwamnati ta Maga da ke jihar ba.

Ya bayyana hakan ne a taron manema labarai da aka gudanar a fadar gwamnatin jihar a ranar Talata, inda ya tabbatar da kubutar da ɗaliban da aka sace a farkon makon nan.

Kotu ta yanke wa mutum 5 hukuncin rataya a Oyo saboda aikata kisan kai An sako ɗalibai 25 da ’yan bindiga suka sace a Kebbi

Ya ce, “An karɓo ɗalibanmu da aka yi garkuwa da su a Maga. Shugaban ƙasa ya ba jami’an tsaro umarni su gano inda yaran suke, kuma su kubutar da su. Muna tabbatar wa iyayen yara da al’ummar Kebbi cewa ’ya’yansu sun dawo lafiya.

“Muna godiya ga shugaban ƙasa da jami’an tsaro, musamman sojoji, ’yan sanda, da Civil Defence da suka yi aiki tukuru har aka kubutar da yaran cikin ƙoshin lafiya,” in ji Gwamnan.

Idris ya jaddada cewa gwamnatin Kebbi ba ta biya kuɗin fansa ba, “Mu, a matsayin gwamnati, ba mu ba da ko sisi ba. A binciken da muka yi, babu wanda ya biya kuɗin fansar yaran.”

A ranar Litinin din da ta gabata ce ’yqn bindiga suka sace ɗaliban su 25 daga makarantar bayan sun kashe mataimakin shugaban makarantar.

Sai dai daga bisani ɗaya daga cikin ɗaliban ta gudo ’yan kwanaki bayan sace su.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • El-Rufai ya koma jami’yyar haɗaka ta ADC
  • An janye ’yan sanda 11,566 daga gadin manyan mutane a faɗin Nijeriya
  • Karamar Hukumar Birnin Kudu Ta Kashe Sama da Naira Miliyan 5 Don Tallafawa Shirin AGILE
  • Palasdinawa Sun Karbi Gawawwakin Shahidai 15 Daga ‘Yan Mamaya
  • Abubuwa 20 da ya kamata ku sani game da Sheikh Dahiru Bauchi
  • Reuters: Kungiyar Likitoci Ba Da Iyaka Ba Ta Fice Daga Asibitin Darfur Bayan Bude Wa Ma’aikatanta Wuta
  • Ko sisi ba a biya ’yan bindiga ba kafin su saki ɗaliban da suka sace – Gwamnan Kebbi
  • Kotu ta yanke wa mutum 5 hukuncin rataya a Oyo saboda aikata kisan kai
  • ’Yan bindiga sun sake kai hari a Kwara, sun sace mutum 11
  • An haramta cin naman Kare da Kyanwa a Indonesia