2027: Atiku, Jonathan da Obi ba za su iya kayar da Tinubu ba — Kalu
Published: 8th, October 2025 GMT
Tsohon Gwamnan Jihar Abiya, kuma Sanata mai wakiltar Abiyanta Arewa, Orji Uzor Kalu, ya ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu ne, zai sake lashe zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Ya bayyana hakan a shirin siyasa na gidan talabijin na Channel a daren ranar Lraba.
An kashe ɗan shekara 13 da shanu 36 a wani sabon hari a Filato ’Yan sanda sun kama ɗan bindiga a kan iyakar Najeriya da KamaruKalu, ya ce babu wanda zai iya kayar da Tinubu a tsakanin Goodluck Jonathan, Atiku Abubakar, ko kuma Peter Obi.
Kalu, wanda ke ɗan jam’iyyar APC, ya ce gwamnatin Tinubu ta samu nasarori wajen farfaɗo da tattalin arziƙi.
A cewarsa, irin tagomashin da Tinubu ya shimfiɗa zai sa ’yan Najeriya su sake zaɓarsa a karo na biyu.
A gefe guda Kalu ya gargaɗi tsohon Shugaban ƘasaJonathan da kada ya tsaya takara, inda ya ce dokar ƙasa ta hana shi sake tsayawa takara.
Jonathan, ya shugabanci Najeriya daga shekarar 2010 zuwa 2015, bayan rasuwar tsohon shugaban ƙasa Umaru Musa Yar’Adua.
Wasu masana doka suna cewa kundin tsarin mulki bai ba shi damar sake tsayawa takara ba.
Kalaman Kalu na zuwa ne daidai lokacin da harkokin siyasar Najeriya suke ƙara ɗaukar zafi yayin da ake shirye-shiryen tunkarar zaɓen 2027.
Jam’iyyar APC mai mulki tana ƙoƙarin kare matsayinta, yayin da jam’iyyun adawa irin su PDP da LP da jam’iyyar haɗaka ADC ke ƙoƙarin farfaɗowa bayan shan kaye a zaɓen 2023.
A zaɓen 2023, Tinubu ya lashe shugaban ƙasa ƙarƙashin jam’iyyar APC, inda ya doke Atiku Abubakar na PDP da Peter Obi na LP.
Dukkaninsu sun soki sakamakon zaɓen ta hanyar kai ƙara kotu, amma Kotun Ƙoli ta tabbatar da nasarar Tinubu.
Yanzu ’yan Najeriya na jiran ganin ko jam’iyyun adawa za su iya haɗa kai don ƙalubalantar APC a 2027, ko kuma Tinubu da jam’iyyarsa za su yi nasara duk da matsalolin tattalin arziƙi da tsaro da ake fuskanta a ƙasar.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Zaɓen 2027
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamna Uba Sani Ya Gana Da Ministan Ayyuka Domin Ganin An Kammala Aikin Titin Abuja Zuwa Kaduna
A cikin nuna jajircewa da hadin kai tsakanin gwamnati jiha da ta tarayya, Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, a ranar Juma’a ya gana da Ministan Ayyuka, Sanata David Umahi, CON, domin yin cikakken bitar aikin titin Abuja–Kaduna–Abuja
Taron, wanda aka gudanar a birnin Abuja, ya nuna irin salon jagorancin Gwamna Uba Sani na jajircewarsa wajen tabbatar da kammala wannan muhimmin titi wanda ke da matuƙar tasiri ga tattalin arzikin ƙasa.
Tattaunawar ta mayar da hankali ne kan yadda za a hanzarta kammala ɓangaren Abuja–Jere da Kaduna, wanda ke da muhimmanci ga miliyoyin ‘yan Nijeriya da ke amfani da shi kullum wajen sufuri, kasuwanci da hulɗar zamantakewa.
Gwamna Uba Sani ya jaddada cewa wannan titin ba na yankin Arewa kadai ba ne, ya bayyana shi a matsayin jijiyar ƙasa da ƙasa ne wadda ke haɗa yankuna daban-daban tare da ƙarfafa haɗin kai da bunƙasar tattalin arziki.
Ya kara da cewa titin Abuja- Kaduna da Kano na ɗaya daga cikin manyan ayyukan gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu a ƙarƙashin Manufar Sabon Fata na (Renewed Hope Agenda), wadda ke nufin sabunta manyan gine-ginen ƙasa da inganta tattalin arziki.
Yace “Wannan titi ba hanya ce kawai ba inda yace wata hanya ce ta tattalin arziki wadda ke haɗa mutane, kasuwanni, da dama a fadin Arewacin Nijeriya da ma bayan haka,”
A nasa jawabin, Sanata Umahi ya yaba wa Gwamna Uba Sani bisa yadda yake kaiwa da komowa domin kare muradun al’ummar Kaduna, tare da tabbatar da cewa gwamnatin tarayya ta kuduri aniyar kammala aikin cikin lokaci. Ya bayyana cewa an umarci kamfanonin da ke aikin da su rika aiki sau biyu a rana domin hanzarta cigaba ba tare da rage inganci ba.
Ministan ya kara da cewa amfani da fasahar siminti mai ɗorewa wanda zai tabbatar da cewa titin zai dawwama tare da rage kudin gyara nan gaba.
Kamfanonin da ke aikin sun yi alkawarin ƙara gaggautawa musamman a yankin Jere dake jihar Kaduna, inda ake sa ido sosai kan ci gaban aiki. Gwamnatin Jihar Kaduna ta kuma tabbatar da ci gaba da haɗin kai da Ma’aikatar Ayyuka ta Tarayya domin magance ƙalubalen da ke iya janyo tsaiko.
PR: Shettima Abdullahi