Sojojin Yemen Sun Nutsar Da Jirgin Ruwan “Eternity” Dake Hanyar Zuwa HKI
Published: 9th, July 2025 GMT
Sojojin Yemen sun sanar da nitsar da jirgin ruwa “Eternity’ wanda yake hanyar zuwa tashar jiragen ruwan HKI ta Eliat, bayan da matukinsa ya ki jin girgadin da aka yi masa.
Janar Yahya Sari ne ya bayyana cewa; Jirgin ruwan ya ki jin gargadin da aka yi masa na hana kowane jirgi wucewa zuwa tasoshin jiragen ruwan HKI.
Sanarwar sojojin kasar ta Yemen ta kunshi cewa, sun yi amfani da karamin jirgin ruwa maras matuki da kuma wasu makamai masu linzami guda shida domin dakatar da jirgin ruwan.
Sai dai, tun da fari sojojin na Yemen sun tseratar da matukin jirgin da ma’aikatan da suke cikinsa, tare da ba su kulawa ta kiwon lafiya.
Janar Sari ya ce; Suna daukar wannan irin matakin ne domin taimakawa Falasdinawa da ake zalunta, tare da jaddada cewa za su ci gaba da daukar wannan irin matakin har zuwa lokacin da za a kawo karshen killace Gaza da kisan kiyashin da ake yi musu.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Sojojin Mamayar Isra’ila Sun Kai Hare-Haren Wuce Gona Da Iri Kan Lardin Hodeidah Na Kasar Yemen
Sojojin gwamnatin yahudawan sahayoniyya sun kai hare-hare kan tashar jiragen ruwa na Hodeidah a kasar Yemen
Jiragen yakin haramtacciyar kasar Isra’ila sun kai farmaki kan tashar ruwan Hodeidah da ke yammacin kasar Yemen, biyo bayan barazanar da sojojin kasar suka yi a yammacin jiya Lahadi.
Majiyar Yemen ta fada a yammacin jiya Lahadi cewa: An ji karar fashewar abubuwa masu yawa a tashar jiragen ruwa na Hodeida, sakamakon farmakin da jiragen saman yakin haramtacciyar kasar Isra’ila suka kai a yankin.
A cewar majiyoyin cikin gidan Yemen, sama da fashe fashe 20 ne aka samu a Hodeidah sakamakon hare-haren da jiragen saman yakin Isra’ila suka kai.