Aminiya:
2025-12-03@08:00:28 GMT

Wasu jiga-jigan ADC za su dawo jam’iyyarmu — Shugaban Jam’iyyar APC

Published: 18th, October 2025 GMT

Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya bayyana cewa wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar ADC, za su koma APC a mako mai zuwa.

A makonnin da suka gabata, ’yan siyasa da dama daga jam’iyyun adawa suna sauya sheƙa zuwa APC, yayin da ake shirin tunkarar babban zaɓen shekarar 2027.

HOTUNA: Al’ummar Jihar Neja sun yi addu’o’in neman zaman lafiya Ta’addanci: An fi kashe Musulmi a kan Kiristoci a Najeriya — Jakadan Amurka

Idan ba a manta ba, Gwamnan Jihar Enugu, Peter Mbah, ya koma APC, sannan Gwamnan Jihar Bayelsa, Douye Diri, shi ma ana sa ran zai sanar da sauya sheƙarsa a hukumance nan ba da jimawa ba.

Yilwatda, yayin ganawarsa da mambobin APC a Jos, Jihar Filato, ya ce: “A mako mai zuwa zan karɓi wasu fitattun mutane daga ADC. Wasu daga cikinsu sun bar PDP sun koma ADC, amma yanzu za su dawo APC.”

Ya ƙara da cewa, yawancin waɗanda za su koma jam’iyyar “sun riga sun kammala gwajin lafiyarsu” kuma za a tarbe su a hukumance a mako mai zuwa.

“A cikin makonni biyu masu zuwa, za mu kuma bayyana wani babban ɗan siyasa da ya kammala gwajin lafiyarsa. Za mu karɓe shi a hukumance nan gaba kaɗan,” in ji shi.

Shugaban jam’iyyar ya bayyana APC a matsayin “amaryar siyasa ta yanzu”, inda ya ce ’yan siyasa da yawa na rubibin shiga jam’iyyar.

Ya ce akwai sanatoci, gwamnoni, da ’yan majalisa da dama da ke shirin komawa APC.

“APC jam’iyya ce mai maraba da kowa,” in ji shi.

“Ba sai ka kasance daga cikin waɗanda suka kafa jam’iyyar ba kafin ka samu ci gaba a cikinta. Ni shaida ne a kan hakan. Da zarar ka shiga, kana da cikakken haƙƙi da damar da kowa yake da ita. Wannan shi ne tsarin jam’iyyarmu.”

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: yan siyasa sauya sheka

এছাড়াও পড়ুন:

Yawan Yahudawan Da Suke Ficewa Daga HKI Sun Nininka Har Sau 100%

Hukumar kididdiga ta HKI ta basa sanarwan cewa yawan yahudawa da suke ficewa daga haramtacciyar kasar .

Tashar talabijin ta Almayadeen na kasar Lebanon ta nakalto hukumar na bada labarin cewa a shekara ta 2010 yawan masana wadanda suke da shahadar Jami’a ya karu ha rya kai kashi 46% sannan wannan adadin ya cilla sama a shekara ta 2023 bayan fara yakin tufanul aksa zuwa kashi 60.4 %.

Har’ila yau kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya bayyana cewa a cikin yan shekarun da suka gabata, yahudawa masu ilmin Jami’a da dama sun bar kasar, saboda yana yaki wanda baya karewa a kasar.

Hukumar kididdiga na HKI a cikin yan kwanakin da suka gabata ta yada rahoto dangane da hijiran yahudawa, musamman daga cikin masu ilmi, wanda ya ga masu shigowa kasar sun ragu matuka a kan wadanda suke ficewa zuwa wasu kasashen duniya don neman inda ake zaman lafiya.

Bisa tsohon tsarin kididdiga na HKI, duk wani bayahude wanda ya share shekara guda a kasashen waje bai shiga HKI ko da nay an kwanaki ba to ana daukarsa a matsayin wanda yayi hijira daga kasar.

Amma a sabon tsarin gwamnatin yahudawan, duk wani bayahude wanda yayi kwanaki 275, wato kasa da shekara guda a kasashen waje, ko da yana zuwa kasar nay an kwanaki za’a lissafa shi daga cikin wadanda suka kaura daga kasar.

Bisa tsohon tsarin mutane dubu 16 suke ficewa daga kasar ba tare da sake dawowa ba, a ko wace shekara. Amma a cikin sabon tsarin an nuna cewa wannan adadin ya karu zuwa mutane dubu 36 a ko wace shekara ne suke ficewa ba tare da sun dawo ba. Daga fara yakinnTufanul Aksa a ranar 7 ga watan Octoban shekara ta 2023 zuwa yanzu adadin yahudawa masu ilmi, wadanda suka hada da likitoci, inginiyoyi da sauransu ne suka fi ficewa daga kasar don duk inda suka je a duniya zasu sami aikin yi.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Gaza: Fiye da Falasdinawa 350 ne sukayi shahada a hare-haren Isra’ila tun bayan tsagaita wuta December 1, 2025 Hamas : Isra’ila na jinkirta aiwatar da mataki na biyu na yarjejeniyar tsagaita wuta December 1, 2025 Nijar : zamu sayar da uranium dinmu ga wanda muka ga dama_ Janar Tiani December 1, 2025 Tawagar ECOWAS za ta je Guinea-Bissau, bayan juyin mulkin soji December 1, 2025 Ministan Harkokin Wajen Turkiya Ya Isa Birnin Tehran Kuma Ya Gana Da Takwaransa Na Iran December 1, 2025 Pezeshkian: Makiya na neman kawo cikas ga ci gaban kasashen Musulmi December 1, 2025 Maduro Ya Gargadi Amurka Game Da Hankoron Mamaye Rijiyoyin Mai Na Venezuela December 1, 2025 Zanga zanga Ta Barke A Isra’ila Yayin Da Natanyaho Ke Neman Afuwa Kan Batun Cin Hanci Da Rashawa December 1, 2025 Mataimakin Ministan Harkokin Wajen Kasar Saudiya Ya Gana Da Ministan Harkokin Wajen Kasar Iran. December 1, 2025 Lebanon: Sakon Kungiyar Hizbullah Ga Paparoma December 1, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Nigeria Ta Bai Wa Dan Takarar Shugabancin Kasar Guine Bissau Mafakar Siyasa
  • An aiwatar da sauye-sauye a wasu muhimman kwamitocin Majalisar Dattawa
  • Shugaba Tinubu Ya Nada Janar Christopher Musa Sabon Ministan Tsaro
  • Tinubu ya naɗa Janar CG Musa sabon Ministan Tsaron Nijeriya
  • An kama ’yan bindiga 4 a Kano
  • Yawan Yahudawan Da Suke Ficewa Daga HKI Sun Nininka Har Sau 100%
  • MAAUN: Ƙungiyar iyaye ta musanta zargin ƙara ƙudin yaye ɗalibai a jami’ar
  • Gwamnatin Kano Ta Kara Jaddada Dokar Haramcin Yin Haya da Babur a Jihar
  • Olisa Metuh ya sauya sheƙa zuwa APC, ya ce PDP ta manta da shi
  • Jihar Jigawa Ta Mayar da Rarar Kudi Sama da Naira Miliyan 50 Ga Maniyyatan Aikin Hajjin 2026