Mai Tsoron Ta Mutu, Shi Yake Maho
Published: 9th, July 2025 GMT
Karuwar tasirin da kasar Sin ke yi a fagen ci gaban kimiyya da fasaha a duniya ba barazana ba ce, sai dai wata dama ce ta kawo ci gaba mai gamewa. Diamond ya kara da cewa, “Kasancewar na yi aiki kafada da kafada da wasu jami’o’i da cibiyoyin kasar Sin na tsawon shekaru masu yawa, na yi amanna da yadda kasar Sin ta dukufa ga samar da kimiyya da fasaha mai bude kofa ga duk duniya bisa adalci.
Kazalika, masanin kimiyya, mamba a makarantar nazarin kimiyya da fasaha ta Afirka, Farfesa Felix Dapare Dakora, ya nuna yadda kasar Sin ke karfafa shigar kasashe masu tasowa cikin harkokin kimiyya a duniya. Yana mai cewa, “A halin yanzu, an gode da samuwar shirye-shiryen da kasar Sin ke mara musu baya a karkashin dandaloli kamar BRI, inda masana kimiyya daga kasashe masu tasowa ke samun damammakin da ba a taba ganin irinsu ba domin bayar da gudummawa da kuma zama a kan gaba.”
Jagorancin da kasar Sin ke yi wajen karfafa hadin gwiwa da kasashe masu tasowa ya bai wa kasashen damar fahimtar cewa lallai hadin kai shi ne karfin da ake bukata, kuma ana iya magance galibin matsalolin da suka zama karfen kafa sakamakon matakan masu shamakancewa, tare da tabbatar da cewa ba a bar kowace kasa a baya ba.
A kullum dai, mai burin ganin ci gaban wasu ba zai taba rasawa ba, kana mai tsoron ta-mutu kuma, zai ci gaba da yin maho! (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: da kasar Sin ke
এছাড়াও পড়ুন:
Hizbullah Ta Yi Allawadai Da Harin HKI A Kasar Yemen
A yau Litinin ne kungiyar ta Hizbullah ta fitar da sanarwa wacce ta kunshi yin Allawadai da harin ta’addancin da HKI ta kai wa kasar Yemen, wanda ya shafi tasoshin jiragen ruwa da muhimmacin cibiyoyin kasar.
Bayanin na Hizbullah ya kuma ce; Makiya suna tsammanin cewa ta hanyar wannan irin harin na wuce gona da iri za su yi hana Yemen ci gaba da matakin da take dauka na daukaka wajen taimakawa Gaza, ta daina kai hare-hare masu tsanani da take kai musu.
Haka nan kuma Hizbullah ta ci gaba da cewa: Har yanzu ‘yan sahayoniya sun kasa fahimtar dabi’ar mutanen Yamen masu hakuri da juriya akan tafarkin jihadi, domin akida ce, cewa gaskiya ita ce wacce ta cancanci a yi biyayya a gare ta, haka nan kuma kare wadanda aka zalunta.”
Kungiyar ta Hizbullah ta kuma kara da cewa; Matsayar da mutane Yemen jagorori da al’umma suke dauka, ya samo asali ne daga koyarwar Imam Hussain ( a.s) wanda ba yi sassauta akan gaskiya ba, wajen kalubalantar dawagitai.”
Kungiyar ta Hizbullah ta kara da cewa; Abokan gaba ba za su cimma manufarsu ba, kuma kamar yadda a baya Amurka ta ci kasa akan Yemen, ita ma Isra’ila makomarta kenan.