Manyan Kalubalen Da Sabon Shugaban INEC Zai Fuskanta
Published: 17th, October 2025 GMT
A taron majalsar zartarwar, Shugaban kasa Bola Tinubu ya bayyana cewa zabinsa na Amupitan ya yi ta’allaka ne a kan rashin nuna son kai na siyasa, gaskiya da kyakkyawan tarihinsa.
Mambobin majalisar, ciki har da shugabanni na yanzu da na baya, sun amince da nadin, suna bayyana Farfesa Amupitan a matsayin mutum mai gaskiya.
Bayan amincewar majalisar, ana sa ran shugaba zai mika sunan Amupitan zuwa majalisar dattawa don tantancewa da tabbatarwa bisa ga tsarin kundin mulkin Nijeriya.
Farfesa Amupitan, mai shekaru 58, dan asalin kauyen Ayetoro Gbede a cikin karamar hukumar Ijumu ta Jihar Kogi. Ya kasance farfesa ne a bangaren shari’a a jami’ar Jos ta Jihar Filato, shi ne mataimakin shugaban jami’a. Haka kuma, shi ne shugaban kwamitin majalisar gudanarwa na jami’ar Joseph Ayo Babalola da ke Jihar Osun.
Jam’iyyun siyasa sun yi kira ga Farfesa Amupitan da ya dawo da amincewar jama’a ga tsarin zaben Nijeriya ta hanyar gaskiya, rashin son zuciya, da gyara tsarin hukumar.
A martani jam’iyyar hadaka ta ADC ta gargadi sabon shugaban INEC, da ya kasance mai biyayya ga mutanen Nijeriya ba wai ga bukatun siyasa ba. Wannan na zuwa ne yayin da jam’iyyar PDP ta yi kira gare shi da ya fifita tsarkake tsarin zabe ta hanyar sauye-sauye domin dawo da amincewar jama’a ga hukumar.
Sai dai jam’iyyar APC mai mulki ta nuna gamsuwa da nadin Amupitan, inda ta bayyana cewa an zabe shi ne bisa cancanta kuma dole ne ya nuna adalci, gaskiya, da himma wajen ci gaba da aiwatar da gyare-gyaren zabe da ake yi.
A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, sakataran yada labarai na kasa na jam’iyyar ADC, Bolaji Abdullahi, ya yi kira ga sabon shugaban INEC da ya sanya aminci ga mutanen Nijeriya maimakon na gwamnatin APC mai mulki. Abdullahi ya jaddada bukatar dawo da amincewar jama’a ga tsarin zaben kasa, yana mai cewa jam’iyyar hadaka ta shirya bai wa sabon shugaban INEC hadin kai. Jam’iyyar tana fatan Amupitan zai yi aiki mafi kyau a zaben 2027.
A halin da ake ciki, mataimakin shugaban matasa na kasa na jam’iyyar PDP, Timothy Osadolor, ya yi kira ga Amupitan da ya aiwatar da gyare-gyare da za su karfafa dimokuradiyyar Nijeriya.
A bangarensa, darakta halda da jama’a na APC, Bala Ibrahim, ya yaba da nadin, inda ya bayyana cewa nadin Farfesa Amupitan ya dogara ne kan cancanta.
Sai dai kuma ‘yan adawa sun kafa wa sabon shugaban INEC sharudda kan gyaran zabe da gaskiya da bin doka yayin da ya shiga ofisi.
A martaninsa kan nada Amupitan, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP a zaben 2023, Peter Obi, da jam’iyyar NNPP sun yi fatan alheri tare yin kira a gare shi ya yi taka tsantsan kan nadin da aka yi masa.
Sakataren yada labarai na kasa na Jam’iyyar NNPP, Ladipo Johnson, ya yi kira ga Amupitan da ya gina jagorancinsa a kan bin doka kuma ya dauki darasi daga kurakuran da aka samu a zaben 2023.
ShareTweetSendShare MASU ALAKAকীওয়ার্ড: kasa na Jam iyyar kasa na jam iyyar Farfesa Amupitan
এছাড়াও পড়ুন:
Dantawaye Ya Karɓi Ragamar Aiki A Matsayin Sabon Kwamishinan Ƴansandan Abuja
Abin da ya rage yanzu shi ne za a zuba ido don ganin irin sauyin da zai kawo na tsaro a birnin tarayyar, sakamakon taɓarɓarewar tsaro da ya addinin garin.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA