2025-10-22@08:22:24 GMT
إجمالي نتائج البحث: 467

«jam iyya mai mulki»:

    “Sanata Wadada yana cikin rijistarmu tun da farko, kawai mun sake ba shi sabon katin zama mamba ne. Don haka, barka da dawowa gida,” in ji shi. Dakta Bello ya ce APC za ta ci gaba da karɓar duk wanda ke son dawo wa jam’iyyar kuma yana kishin ƙasar nan. A nasa ɓangaren, Sanata Aliyu Wadada ya ce dawowarsa jam’iyyar APC kamar komawa gida ne, domin yana daga cikin wanda suka kafa APC a Nasarawa. “Ina cikin jam’iyyar SDP, amma ban daina goyon bayan ci gaban APC ba. Ba mu bar jam’iyyar gaba ɗaya ba, kawai mun ɗan huta na wani lokaci ne. Yanzu mun dawo,” in ji shi. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Siyasa Tinubu Ya Taya Kwankwaso Murnar Ranar...
    Wakilin Amurka a kasar Syria Tom Barak ya bayyana a wannan Litinin cewa, shirin shugaban Amurka Donald Trump mai dauke da abubuwa 20 na dakatar da yakin zirin Gaza ya haifar da wani sabon yanayi na siyasa, wanda hakan ya sa batun kulla alaka tsakanin kasashen larabawa da Isra’ila ya kara samun karbuwa fiye da kowane lokaci. Barak ya bayyana a wani sakon da ya wallafa a shafukan sada zumunta cewa, “hanyar samun zaman lafiya a yankin ta bayyana karara duk kuwa da kalubalen da ake fuskanta, musamman dangane da warware matsalar Hamas.” In ji shi. Ya kara da cewa: “Saudiyya na gab da shiga yarjejeniyar kulla alaka da Isra’ila a hukumance, yayin da ta yi hakan, sauran kasashe za...
    Wakilin Amurka na Musamman a kasar Siriya ya matsa kaimi domin ganin kasashen Saudiyya da Lebanon da kuma Siriya sun kulla alakar jakadanci da haramtacciyar kasar Isra’ila Wakilin Amurka na musamman a Siriya Tom Barrack, ya gabatar da manufofinsa na sake fasalin yankin Gabas taTsakiya a siyasance bayan kawo karshen yakin Gaza. A cikin dogon hangen nesa, wanda ya wallafa a shafinsa na Twitter, Barrack ya yi ikirarin cewa abu mafi muhimmanci shi ne samar da zaman lafiya a yankin, da kwance damarar Hizbullah, da shigar da kasashen Labanon da Siriya cikin yarjejeniyoyin kyautata alaka da haramtacciyar kasar Isra’ila. Ya kara da cewa Saudiyya ma tana dab da kyautata alakarta da haramtacciyar kasar Isra’ila. Barrak ya bayyana cewa: Taron Sharm...
    Darakta Janar na Hukumar Makamashin Nukiliya ta Duniya (IAEA) Rafael Grossi ya bayyana kwarin gwiwar cewa, za a iya warware takkadama kan shirin Iran na makamashin nukiliya ne ta hanyar diflomasiyya kadai. Grossi ya bayyana hakan ne a wata hira da jaridar Neue Zeitung ta kasar Switzerland a jiya Lahadi. Shugaban hukumar ta IAEA ya ce, masu binciken ba su sami wata shaida da ke nuna cewa Iran ta boye wani adadi na sinadarin uranium da aka inganta ba. Ya kara da cewa, “Yawancin abubuwan da aka samu na Iran an adana su ne a wuraren da aka sani a Isfahan da Fordow, da kuma wani lokaci a Natanz.” in ji shi. Grossi ya bayyana kwarin gwiwa cewa “za a...
    Kasar Saudiyya ta rage yawan guraben kujerun aikin hajjin da take ware wa Najeriya daga 95,000 zuwa 66,910 daga shekarar 2026. Aminiya ta ruwaito cewa a baya Najeriya ta shafe tsawon shekaru uku tana samun guraben na 95,000 a yayin Aikin Hajjin. ’Yan bindiga sun kashe jami’an tsaro 8 a harin kwanton ɓauna a Zamfara An ceto mutane 3 da aka yi garkuwa da kama wasu a Bauchi A cewar Hukumar Aikin Hajji ta Ƙasa (NAHCON), wannan sauyi ya biyo bayan gazawar Najeriya wajen cika guraben da aka ware mata a hajjin shekarun 2024 da 2025. Wata sanarwa da, Mataimakiyar Darakta a Sashen Yaɗa Labarai ta hukumar, Fatima Sanda Usara, ta sanya wa hannu, ta ce hakan na nufin za...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Xi Jinping Ya Yi Kira Da a Kara Horar Da Kwararrun Masana A Fannin Aikin Gona October 16, 2025 Daga Birnin Sin Shugabannin Kasashe Da Dama Sun Yaba Wa Sin Kan Gudummawar Da Ta Bayar A Fannin Tabbatar Da Daidaiton Jinsi October 16, 2025 Daga Birnin Sin Ɗaga Matsayin Dangantakar Zambia Da Sin Ya Haifar Da Manyan Nasarori October 16, 2025
    Hukumar kula da gidaje ta jihar Kano ta fara wani gagarumin aikin tsaftar muhalli kashi na biyu a birnin Kwankwasiyya, inda ta kara azama wajen gina tsaftataccen muhalli, lafiya da kuma dorewar muhalli a birane.   Da yake jawabi yayin aikin, mukaddashin Manajan Daraktan Kamfanin, Engr. Isyaku Umar Kwa, ya bayyana cewa kashi na biyu ya mayar da hankali ne kan inganta harkar sharar gida, da inganta tsarin tattara shara, da kuma kawata wuraren jama’a a fadin birnin na Kwankwasiyya.   A cewarsa, aikin na da nufin tabbatar da tsaftar tituna, wuraren shakatawa, da wuraren jama’a tare da inganta alkinta muhalli.   Engr. Kwa ya bayyana cewa an tsara wannan shiri ne domin karfafawa mazauna garuruwan Kwankwasiyya da Bandirawo da...
    Jam’iyyar ADC ta ce sauya sheƙar da wasu gwamnonin jihohi suka yi zuwa jam’iyya mai mulki ya nuna yadda Shugaba Bola Tinubu, ke ƙoƙarin mayar da Najeriya ƙasa mai jam’iyya ɗaya. A wata sanarwa da Bolaji Abdullahi, mai magana da yawun jam’iyyar na ƙasa, ya fitar, ya ce jam’iyyun adawa ba su damu da abin da ya kira “cin amanar siyasa” da gwamnonin suka yi ba. Gwamna Inuwa ya naɗa sabbin shugabanni a ma’aikatar lafiya ta Gombe Ba za mu yi sulhu da ’yan bindiga ba sai sun yi tuba na gaskiya — Radda Ya ce zaɓen 2027 ba zai zama takara tsakanin jam’iyyu kawai ba, sai dai ya zama gwagwarmaya tsakanin talakawan Najeriya da gwamnatin da ta jefa rayuwar...
    Tsohon ɗan majalisar wakilai, Farouk Lawan, ya ce afuwar shugaban ƙasa ya yi masa, ta ba shi kwarin guiwar yin wata sabuwar tafiyar siyasa. Ya bayyana cewa ya bar tafiyar Kwankwasiyya ne saboda jagorancinta ya yi watsi da shi lokacin da ya fi bukatrsu. ’Yan bindiga sun kashe mutum 1, sun sace dabbobi a Katsina Kaso 92 cikin 100 na ’yan Najeriya ba su iya wanke hannu ba — UNICEF Lawan, wanda ya wakilci mazabar Bagwai/Shanono a Jihar Kano, yana cikin mutane 175 da Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya yi wa afuwa a ranar 9 ga watan Oktoba. An kama shi a shekarar 2021 bayan samun sa  da laifin karɓar cin hanci a 2012, domin cire sunan wani kamfani daga jerin...
    Iran ta kai hari a wani sansanin sojan Isra’ila na sirri da ke karkashin wata hasumiya a Tel Aviv Yankin Gray, wani dandali ne na bincike, ya bayyana samuwar wani maboyar sirri na sojan Isra’ila da ke karkashin wani hasumiya a Tel Aviv, wanda ake kyautata zaton yana cikin wadanda aka kaiwa hari da makami mai linzami na Iran yayin harin da aka kai ranar 13 ga watan Yuni. Bisa binciken da aka gudanar, dandalin ya gano wurin da wani wurin karkashin kasa da aka fi sani da “Site 81”, wani rukunin jami’an leken asiri na hadin gwiwar sojojin Amurka da Isra’ila da ke karkashin rukunin gidaje na Da Vinci a wata unguwa mai yawan jama’a a tsakiyar birnin Tel...
    Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana dalilin da ya sa Iran ba za ta halarci taron na Sharm el-Sheikh ba Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya bayyana dangane da rashin halartar jamhuriyar Musulunci ta Iran zuwa taron na Sharm el-Sheikh cewa, ba za su iya tunkarar wadanda suka kaddamar da hare-haren wuce gona da iri kan al’ummar Iran da kuma ci gaba da yi musu barazana da kuma sanya musu takunkumi ba. Araqchi ya rubuta a shafinsa na yanar gizo a dandalin X da sanyin safiyar yau litinin cewa: “Iran ta nuna matukar jin dadin ta ga gayyatar da shugaba Sisi ya yi wa Iran na halartar taron na Sharm el-Sheikh. Duk da Muradin Iran din na tattaunawa...
    “Ta yaya Jonathan zai zama barazana? Mun doke shi a baya lokacin da PDP take kan mulki.   “Idan mutum yana ganin cewa PDP ita ce kololuwar jam’iyya a Nijeriya, kuma ya sha kaye a lokacin da yake ganiyarsa, ina ganin sai makiyinsa ne kawai zai tilasta masa ya kara tsayawa takara a zaben 2027,” in ji shi.   Tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa ya ce a yanzu haka Jonathan ya kasance dan siyasa mai daraja, yana mai cewa komawa fagen siyasa na iya rage masa kima da kuma zubar masa da darajar da yake da shi a idon duniya.   Ya jaddada cewa Jonathan ya samu damar nuna cewa mulki bai tsole masa ido ba, domin haka ne...
    “Muna kira ga majalisar kasa da ta yi la’akari da shirin gyaran tsarin kudurorin zabe cikin gaggawa. Amincewa da dokar cikin lokaci yana da muhimmanci ga shirinmu na gudanar da zabe a 2027.   “Rashin tabbas game da tsarin doka na zabe na iya kawo matsaloli masu yawa ga ayyukan hukumar INEC yayin da lokacin zabe ke karatowa,” in ji shi.   Shugaban INEC ya bayyana cewa hukumarsa ta aiwatar da shawarwarin da aka mika mata kai tsaye a rahoton EU na zaben 2023.   “An dauki mataki kan wasu bangarori na shawarwarin da ake bukatar hukumar ta aiwatar da su. Haka kuma, ana daukar mataki kan shawarwarin da suka shafi fannoni da dama wadanda ake bukatar hadin gwiwa tsakanin...
    Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya umarci Hukumar Aikin Hajji ta Ƙasa (NAHCON) ta sake rage kuɗin aikin Hajjin shekarar 2026 nan take, kuma ta fitar da sabon farashin cikin kwana biyu. Wannan na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan hukumar ta sanar da rafin kimanin N200,000 a kan farashin da maniyyata suka biya a bara. Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ne ya isar da umarnin shugaban kasa yayin wani taro da ya yi da shugabanni da mambobin hukumar NAHCON a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, a ranar Litinin. Shettima ya buƙaci a samu hadin kai tsakanin jami’an jihohi da na tarayya, ciki har da gwamnoni, wajen fitar sabon farashin da ya dace da yanayin tattalin arzikin ƙasar. An fara...
    Burgediya JanarEsma’il Qa’ani babban kwamnadan dakarun “Qudus'” IRGC a nan Iran ya bayyana cewa kungiyar Hamas ta boye ranar fara yakin tufanul Aksa har shugaban kungiyar Shahid Isma’il Haniyya da shahida Nasarallah duk basu san da lokaci fara yakin ba, sai suka ji an fara. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto Janar Qa’ani yana fadar haka, a jiya jumm’a a hirar da aka yi da shi a tashar talabijin ta cikin gida a nan Iran. Ya kumakara da cewa a lokacinda aka fara yakin shugaban kungiyar ta Hamas yana kan hanyarsa ta zuwa kasar Iraki, yana dawowa ne ya ji labarin fara shi. Janar Qa’ani ya kara da cewa, amma  duk da haka, shahida Nasarallah ya zauna...
    Turkiyya ta mayar da martani ga shugaban Amurka cewa: Ba za ta daina sayen iskar gas daga kasar Rasha ba Ministan makamashi da albarkatun kasa na kasar Turkiyya Alparslan Bayraktar ya tabbatar a wata hira da yayi da gidan talabijin a jiya alhamis cewa: Kasarsa ba ta da niyyar yin watsi da sayen iskar gas da take daga Rasha. “Ministan a wata zantawa da tashar CNN Turk ya bayyana cewa: Game da Turkiyya ba za ta iya ce wa ‘yan kasarta ku yi hakuri, iskar gas ta kare ba. Ya kara da cewa: “An tabbatar da tsaron iskar gas tana tabbata ne ta  hanyar yin amfani tilas da wadannan hanyoyin, ba tare da nuna bambanci ba a lokacin hunturu mai...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    “Ina kira ga kowane ɗan Nijeriya da ya rungumi zaman lafiya, kwanciyar hankali, da haɗin kai a gidajenmu, al’ummominmu, da fadin ƙasarmu. Tare, cikin haɗin kai da ƙauna, za mu iya gina Nijeriya ta mafarkinmu. Barka da ranar ‘Yancin Kai!” in ni Shettima.   Akan hakan, Shettima ya jinjinawa ƙoƙarin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu wanda ya samar da abubuwan ci gaban ƙasa, inda ya ƙara da cewa, idan aka ƙara haƙuri abubuwa za su yi kyau a Nijeriya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Mataimakin shugaban kasar Iran ya bayyana cewa; Yakin kwanaki 12 da aka kaddamar kan Iran, gwaji ne na karfinta a fagen kimiyya da fasaha Mataimakin shugaban kasar Iran na farko Mohammad Reza Arif ya bayyana cewa: Wani bangare na ci gaban Iran a fannin kimiyya da fasaha na da nasaba da mayar da takunkuman da aka kakaba mata zuwa ga damammaki da bunkasa ci gabanta. Ya yi bayanin cewa: “Yakin kwanaki 12 da gwamnatin Sahayoniyya da Amurka suka kakaba wa Iran, wani gwaji ne kan karfin kimiyya da fasaharta. Ya ce: Iran ta fi karfi tare da mai da hankali a bangarorin kimiyya da fasaha.” Arif ya jaddada cewa: Al’ummar Iran suna bin tafarkin shahidai da kuma ci gaba da...
    Malaman Kwalejin Kimiyya da Ƙere-ker ta Nuhu Bamalli da ke Zariya a Jihar Kaduna sun tsunduma yajin aiki. Ƙungiyar Malaman Kwalejin Kimiyya da Ƙere-kere (ASUP) reshen makarantar ta fara yajin aikin ne daga yau Talata, 39 ga Satumba, 2025. Ƙungiyar ta fara yajin aikin ne bayan zaman da ta yi da wakilan gwamnatin jihar, inda Babban Sakataren Gwamnatin Jihar, ya buƙaci su ƙara haƙuri, yana mai alamta cewa Gwamna Uba Sani ya ba da izinin biyan buƙatunsu. Sanarwar da Kwamared Usman Shehu Suleiman ya sanya wa hannu ta ce, “Daga Talata , 30 ga Satumba 2025 mu fara yajin aiki har sai abin da hali ya yi.” An shiga taron gaggawa kan takun saƙar PENGASSAN da Matatar Dangote ASUU ta...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi kira ga makarantun horar da ‘yan jam’iyya da su taka rawar gani wajen kyankyashe hazikai, tare da gabatar da shawarwari ga JKS.   Xi, wanda shi ne sakataren kwamitin kolin JKS, kuma shugaban hukumar zartarwar rundunar sojojin kasar Sin, ya yi kiran ne cikin wani umarni da ya gabatar ga makarantun koyar da jagoranci na ‘ya’yan jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin. (Mai fassara: Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Yayin da aka ce jam’iyyun siyasa a jamhuriya ta farko, sun fi karkata kan yanki, an yi yunkurin kafa jam’iyyun kasa a jamhuriya ta biyu da gangan. A wancan jamhuriyar (1979–1983), manyan jam’iyyun siyasar Nijeriya su ne GNPP, NPN, NAP,NPP, PRP, da kuma UPN. Duk da cewa, jam’iyyun sun banbanta a akida; amma ana ganin jam’iyyun UPN da PRP, a matsayin na masu fafutuka da kuma jajircewa, domin kuwa jam’iyyar UPN ta tsaya tsayin-daka wajen aiwatar da manufofinta. An gina tsarin jam’iyyar bisa manyan manufofi hudu kamar haka: ilimi kyauta tun daga makarantar reno har zuwa manyan makarantu, harkar kiwon lafiya kyauta, hadin gwiwar karkara da ci gabanta da kuma samar da cikakkun ayyukan yi masu dorewa. Wadannan alkawura, an...
    Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya ƙaryata rahotannin da ke cewa ya aike wasiƙar neman shiga wata jam’iyya ta daban. A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Kwankwaso ya ce babu gaskiya a labaran, kuma ya shawarci jama’a da su yi watsi da su. ’Yan bindiga sun kashe mutum 5 a Masallaci a Zamfara Ganduje ya gindaya wa Kwankwaso sharadin shiga APC “Mun samu bayanin wasu rubuce-rubucen da ke yawo a Intanet cewa mun miƙa wasiƙar neman shiga wata jam’iyya a ƙasar nan. “Muna so mu fayyace wa jama’a cewa ba mu taɓa miƙa irin wannan wasiƙa ga kowace jam’iyya ba. “Saboda haka mun shawarci jama’a da su riƙa neman duk wani bayani game da...
    Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya ƙaryata rahotannin da ke cewa ya aike wasiƙar neman shiga wata jam’iyya ta daban. A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Kwankwaso ya ce babu gaskiya a labaran, kuma ya shawarci jama’a da su yi watsi da su. ’Yan bindiga sun kashe mutum 5 a Masallaci a Zamfara Ganduje ya gindaya wa Kwankwaso sharadin shiga APC “Mun samu bayanin wasu rubuce-rubucen da ke yawo a Intanet cewa mun miƙa wasiƙar neman shiga wata jam’iyya a ƙasar nan. “Muna so mu fayyace wa jama’a cewa ba mu taɓa miƙa irin wannan wasiƙa ga kowace jam’iyya ba. “Saboda haka mun shawarci jama’a da su riƙa neman duk wani bayani game da...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esmail Baghaie yayi tir da shugaban kasar Amurka Donal Trump bayan ya bayyana cewa Amurka tana son ta sake shiga tattaunawa da Iran kan shirinta na makamashin nukliya. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Baghaie yana fadar haka a shafinsa na X ya kuma kara da cewa shugaban ya yi wannan tayin a farkon shigabarsa fadar white house kuma munga matijar wanda itace yakin kwanaki 12 a cikin watan yunin da yagabata. A jawabinsa a babban zauren MDD shugaba Trump ya bayyana  yadda jiragen yakin kasar samfurin B2 suka sauke boma-bomai har paund 30,000 a kan cibiyoyin makamashin Nukliyar kasar a Natanz da fordo da kuma Esfahan da nufin wargaza su....
      Bako wacce ta bayyana hakan bayan ta duba ɗaya daga cikin cibiyoyin CBT, ta ce, ana gudanar da jarrabawar a cibiyoyi uku da aka keɓe, da suka haɗa da Jami’ar Jihar Kaduna a shiyya ta 2), Kwalejin Ilimi ta Tarayya, Zariya (Shiyya ta 1) da Jami’ar Jihar Kaduna ta Kafanchan (shiyya ta 3). Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
      A halin yanzu dai Humaid yana daya daga cikin Limamai tara na Masallacin Harami na Makkah. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya yaba da buɗe ofishin Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan a Majalisar Dattawa, inda ya ce haɗin kai ya yi nasara a kan zalunci. A ranar Talata ne Majalisar ta buɗe ofishinta, bayan rufe shi da aka yi tun daga 6 ga watan Maris, 2025, lokacin da aka dakatar da ita na tsawon watanni shida saboda zargin karya ƙa’idojin majalisar. Darajar Naira ta ƙaru bayan CBN ya rage kuɗin ruwa Mawaki Davido ya ba matarsa kyautar motar miliyan 240 Ko da yake Kotun Tarayya ta yanke hukunci a ranar 4 ga watan Yuli cewa dakatarwar “ta yi tsauri kuma an yi ta ba bisa ƙa’ida ba.” Da yake mayar da martani, Atiku ya ce sake buɗe...
    Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya yi Allah wadai da hare-haren da Amurka da Isra’ila suka kai a watan Yuni a kan kasar. A lokacin da yake jawabi a taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 80 ya shaidawa mahalarta taron Majalisar Dinkin Duniya a birnin New York a yau Larabar cewa, hare-haren wani babban rauni ne ga zaman lafiya a yankin. Shugaban ya ce hare-haren, wadanda suka afkawa garuruwa, gidaje, da ababen more rayuwa na Iran, yayin da ake ci gaba da tattaunawar diflomasiyya, “babban cin amanar diflomasiyya da raunana kokarin da ake yi na samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali ne.” Pezeshkian ya zargi Washington da Tel Aviv da ruguza tattaunawar da gangan da karfin soji. Shugaban na...
    A ranar Talata, 1 ga Rabi’ul Thani 1447H, daidai da 23 ga Satumba 2025, Allah Ya yi wa Babban Mai Bayar da Fatawa na kasar Saudiyya, Sheikh Abdul Aziz Al-Sheikh, rasuwa. An yi jana’izarsa a Masallacin Imam Turki bin Abdullah da ke birnin Riyadh a ranar Talata bayan sallar La’asar, wanda Yarima Mai Jiran Gado, Muhammad bin Salman ya jagoranci manyan malamai da jami’an gwamnati da dubban mutane. Haka kuma, an yi masa Salatul Gaib a Masallacin Ka’aba da ke Makkah da kuma Masallacin Annabi Muhammad (SAW), da kuma sauran daukacin masallatan da ke kasar bisa umarnin masarautar UNGA: Yau Shettima zai gabatar da jawabin Najeriya a MDD Yarima Salman ya jagoranci jana’izar babban mai ba da fatawa na Saudiyya...
    Yarima mai jiran gado na Masarautar Saudiyya, Sheikh Muhammad bin Salman, ya jagoranci sallar jana’izar fitaccen malamin addini, Sheikh Abdulaziz bin Abdullah bin Muhammad Al-Sheikh. Shafin Inside Haramain ya ruwaito cewa an gudanar da jana’izar ce a Masallacin Imam Turki bin Abdullah da ke birnin Riyadh. CBN ya rage kuɗin ruwa zuwa kashi 27 cikin 100 Kotu ta hana NUPENG rufe Matatar Ɗangote Aminiya ta ruwaito cewa za a yi masa Salatul Ga’ib a Masallacin Harami na Makkah da kuma Masallacin Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama da ke Madina. A wannan Talatar Allah Ya yi wa Babban Mai Ba da Fatawar na Saudiyya rasuwa yana da shekara 82. Fadar Masarautar ƙasar da kuma Shugaban Majalisar Malaman Masallata Haraman Makkah da...
    Allah Ya yi wa Babban Mai Ba da Fatawa na kasar Saudiyya, Sheikh Abdulaziz bin Abdullah bin Mohammed Al Al-Sheikh, rasuwa. Hukumomin ƙasar Saudiyya sun sanar da cewa Sheikh Abdulaziz bin Abdullah bin Mohammed Al Al-Sheikh ya rasu yana da shekara 82 a duniya. Fadar Masarautar ƙasar da kuma Shugaban Majalisar Malaman Masallata Haraman Makkah da Madina, Sheikh Abdul Rahman Sudais, sun gabatar da ta’aziyyar iyalai da ɗaliban mashahurin malamin. Za a gudanar da Sallar Jana’izarsa a Masallacin Imam Turki bin Abdullah da ke birnin Riyadh bayan Sallar La’asar. Kazalika za a yi masa Salatul Ga’iba a Masallacin Harami na Makkah da kuma Masallacin Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama da ke Madina.  
    Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama gungun wasu mutane da ake zargi da safarar mata zuwa kasar Saudiyya. Hisbah ta dakile yunkurin mutanen ne a yayin da suke kokarin safarar wasu mata hudu daga jihohin Kano da Jigawa da Yobe, ta hannun wakilansu da ke sassan kasashen Yammacin Afirka? Mataimakin Babban Kwamnand Hukumar, Dakta Mujahideen Aminudeen, ya ce masu safarar matan sun yaudarin matan da aka ceto cewa za su yi musu biza zuwa kasar Ghana inda daga nan za su wuce da su zuwa Saudiyya domin sama musu ayyukan yi. An kana daya daga cikin mutanen ne a ranar Lahadi, wanda hakan ya kai ga cafke shugabansu da ake kira Bashir Sani Ibrahim. Ballon d’Or: Wa zai lashe...
    Tsohon Shugaban Ƙasa, Goodluck Jonathan, ya ce duk wani shugaba da bai yi aiki yadda ya kamata ba, bai kamata a sake zaɓarsa ba. Ya yi gargaɗin cewa maguɗin zaɓe na ɗaya daga cikin manyan barazana ga dimokuraɗiyya a Afirka, kuma idan ba a gyara tsarin ba, ’yan kama-karya za su zama wajen zama. Yadda za ka dawo da kuɗinka da ka yi kuskuren turawa wa wani An tsinci gawar kwamandan hukumar NDLEA a otel a Kalaba Jonathan, ya yi wannan jawabi ne a taron shekara-shekara na Tattaunawar Gidauniyar Goodluck Jonathan da aka gudanar a Birnin Accra, na Ƙasar Ghana. Ya ce mutanen Afirka na son a yi amfani da ƙuri’unsu don su samu shugabanni da za su inganta ilimi,...
    Ministan tsaron kasar Pakitsan Khaje Asif ya fada a jiya Juma’a cewa, makaman Nukiliyar da kasarsa take da su, wani sashe ne na yarjejeniyar tsaro da su ka kulla da kasar Saudiyya. Haka nan kuma ya kara da cewa; Yarjejeniyar ta tsaro ce tsagwaronsa, kuma manufarta ita ce aiki tare a tsakanin kasashen biyu a wannan fagen. Asif wanda tashar talabijin din “Geo News” ta yi hira da shi ya kuma ce; Idan daya daga cikin kasashen ta fuskanci hari,to za mu mayar da martani na hadin gwiwa.” Ministan tsaron na kasar Pakistan ya kuma ce; Ba tare da ambaton suna ba,amma duk wanda ya kai harin wuce gona da iri, to zai fuskanci mayar da martani na hadin gwiwa....
    Sheikh Na’im Kassima wanda ya gabatar da jawabi a jiya  juma’a ya kuma kara da cewa; A halin yanzu kungiyar gwagwarmaya tana fuskantar matsanancin yanayi mai hatsari,tare da jaddada cewa; Wanzuwar HKI, manufarsa ita ce a samar da wani yanki na turai da Amurka a cikin wannan yankin domin hana al’ummar yankin ci gaba da bunkasa ta fuskokin ttatalin arzki, siyasa da al’adu da ci gaba. Babban magatakardar kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ya kira yi kasar Saudiyya da ta bude sabon shafin alakarta da kungiyoyin gwagwarmaya. Har ila yau Sheikh Na’im Kassim ya ce, HKI wani makami ne na kasashen turai da aikinsa shi ne yin kisan kare dangi akan duk wanda ya ki yin biyayya a gare su....
    Dubban ’yan Nijeriya ne ke zaune a ƙasar Saudiyya ba tare da takardun izinin zama ba, musamman a biranen Makkah da Madina. Rayuwarsu cike take da fargaba da rashin tabbas, a yayin da suke yin ayyukan hannu ko ƙananan sana’o’i ba tare da wata kariya ta doka ba. A yayin aiki Hajjin shekarar nan ta 2025, wakilimmu ya samu yin hira da wasu ’yan Nijeriya da ke zaune a can — waɗanda aka fi sani da Takari — inda suka bayyana masa yanayin rayuwarsu sa iliminsu da tsarin matsuguninsu da yanayin aikinsu da rayuwar ’ya’yansu da wasu ƙalubale na fargabar kame da rushe gidajenau, da ma ra’ayinsu kan komawa Nijeriya da sauransu. Ameera, wata ’yar Najeriya da ke zaune...
    Wasu kafafen diblomasiyya nakasashen yamma sun tabbatarwa wakilin tashar talabijin ta Al-mayadeen na kasar Lebanon kan cewa gwamnatin Amurka ce zata jagoranci kasashen yamma wajen tattaunawa da karar Iran. Majiyar ta kara da cewa turawan sun mika wuya ga takurawar washintong don jagorantar tattaunawa da JMI kan shirinta namakamashin nukliya da kuma batun yin watsi da sabon yarjeniyar da Iran ta kulla da hukumar IAEA a al-kahira a baya bayan nan. Banda haka suna son suyi amfani da tsarin Snapbackdon  kara takurawa JMI. Sannan kasashen turaiba zasu sararawa JMI ko kadan ba a takurawar da suke mata a tattaunawar. Duk da cewa yarjeniyar Al-kahiri wani bangaremai muhimmanci ne ga bukatun kasashen Turai daga Tehran, amma har yanzun akwai sabbin sharuddan...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran ya yi kira ga kwamitin tsaro na MDD da ya shiga tsakaninta da kasashen turai guda 3 don tabbatar da cewa sun zabi diblomasiyya da Iran mai makon fito na fito da ita. Tashar talabijan ta Presstv daga nan Tehran ta nakalto ministan yana fadar haka a jiya Alhamis ya kuma kara da cewa Iran ta gabatar masu da hanyoyin warware matsaloli tsakaninsu da JMI kuma masu yiyuwa, amma da alamun sun fi son fito na fitoda JMI, dangane da tsarin nan na Snapback dangane da yarjeniyar Nukliya ta JCPOA ta shekara ta 2015.  Aracgchi ya bayyana haka ne jim kadan kafin kwamitin yafara zama don tattauna batun tsarin na tsapback a jiya alhamis ....
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Da safiyar yau 17 ga watan Satumba, aka bude dandalin tattauna batutuwan tsaro na Xiangshan karo na 12 da zai dauki kwanaki 3, daga raneku 17 zuwa 19 ga wannan nan, bisa jigon “daukaka tsarin duniya da inganta neman ci gaba cikin lumana”, a nan birnin Beijing. Tawagogi sama da 100 na gwamnatocin kasashe daban-daban da yankuna da wakilan kungiyoyin kasa da kasa ne ke halartar taron, inda yawan masu rajista ya wuce 1,800. Da safiyar yau, taron ya shirya tarukan tattaunawa guda 6 bisa jigon “ma’anar cimma nasarar yakin duniya na kin tafarkin murdiyya” da “madaidaitan hanyoyi da manyan kasashe za su bi na yin mu’ammala”, da “hanyoyin warware rikice-rikicen shiyya-shiyya”, da “cika shekaru 80 da kafuwar MDD: samun...
     Babban sakataren majalisar koli ta tsaron jamhuriyar musulunci ta Iran Dr. Ali Larijani ya bayyana cewa; Za a bunkasa aiki tare a tsakanin Iran da Saudiyya a fagagen tattalin arziki da kuma tsaro. Dr. Larijani ya bayyana hakan ne jim kadan bayan fitowar daga ganawar da ya yi da Yarima mai jiran gado na Saudiyya Mu8hammad Bin Salman. Bugu da kari Dr. Ali Larijani ya ce a yayin ganawarwa da Yarima mai jiran gado na Saudiyya Muhammad Bin Salman, sun tattauna hanyoyin bunkasa alakar kasashensu ta fuskoki mabanbanta, da kara girman wannan alakar ta fuskar tattalin arzki da tsaro fiye da yadda take a yanzu.” Haka nan kuma ya ce, za a yi aiki domin kawar da dukkanin abubuwan da...
    Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya janye dokar ta-ɓaci da ya ayyana ta tsawon watanni shida a Jihar Ribas. Tinubu, ya ayyana dokar tun a ranar 18 ga watan Maris, 2025, saboda rikicin siyasa da ya haifar da tsaiko a harkokin mulki tsakanin ɓangaren Zartarwa da Majalisar Dokokin jihar. NECO ta saki sakamakon jarabawar 2025 Saudiyya ta saki ’yan Najeriya 3 da ta kama kan zargin safarar miyagun ƙwayoyi A jawabin da ya gabatar a Fadar Shugaban Ƙasa a ranar Laraba, Tinubu ya ce matakin dokar ta-ɓacin ya cimma manufarsa, kuma ba za a tsawaita ba ƙarewar wa’adin da aka gindaya. “Ina farin ciki yau game da bayanan da ke hannuna, an samu yanayin fahimta a tsakanin dukkanin masu ruwa...
    Hukumomin a Ƙasar Saudiyya, sun saki wasu ’yan Najeriya uku da aka kama a Jeddah kan zargin safarar miyagun ƙwayoyi. Waɗanda aka saki sun haɗa da Hajiya Maryam Hussain Abdullahi, Hajiya Abdullahi Bahijja Aminu, da Malam Abdulhamid Saddieq. Tinubu bai shirya gudanar da sahihin zaɓe ba a 2027 – Buba Galadima Gwamnati ta fara duba yara marasa galihu kyauta a asibitin Aminu Kano Sun shafe makonni huɗu a tsare kafin aka tabbatar da cewa ba su da laifi. A wajen taron manema labarai a Abuja, mai magana da yawun Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi (NDLEA), Femi Babafemi, ya ce sakin ya biyo bayan tttaunawa da Shugaban NDLEA, Janar Mohamed Buba Marwa (mai ritaya), tare da Hukumar Hana...
    Hukumar NDLEA ta bayyana cewa wata ƙungiyar masu safarar miyagun ƙwayoyi ce a filin jirgin sama na Kano ta boye jakunkunan ƙwayoyi a cikin kayan matafiyan. An kama shugaban ƙungiyar, Ali Abubakar Mohammed (wanda aka fi sani da Bello Karama), tare da wasu abokan aikinsa. Hukumar ta ce mutanen ukun ba su da laifi kuma an zalunce su ne kawai. An saki su ne bayan bincike da kuma ƙoƙarin diflomasiyya na tsawon makonni. Lamarin ya tayar da hankali kan tsaro a filayen jirgin sama a Nijeriya da yadda masu aikata laifuka ke amfani da fasinjoji marasa laifi. Hukumar ta ce za a ɗauki ƙarin matakai don hana faruwar irin wannan lamari. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun...
    Kasashen Iran da Saudiyya sun bukaci hadin kan hadin kan Musulmi game da halin da ake ci a yankin Wannan bayannin ya fito ne a yayin ganawar sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran Ali Larijani da yarima mai jiran gado na kasar Saudiyya Mohammed bin Salman a birnin Riyadh inda suka tattauna kan dangantakar dake tsakanin kasashen biyu da kuma halin da ake ciki a yankin. Ganawar dai ta nuna wani muhimmin mataki a huldar diflomasiyya ta tsakanin Tehran da Riyadh. Larijani ya tafi Saudiyya ne bisa gayyatar da ministan tsaron kasar ya yi masa, inda ya jagoranci tawagar da ta hada da mataimakin sakataren harkokin kasa da kasa Ali Bagheri Kani da mai ba da shawara kan harkokin...
    Hukumar NDLEA ta bayyana cewa wata ƙungiyar masu safarar miyagun ƙwayoyi ce a filin jirgin sama na Kano ta boye jakunkunan ƙwayoyi a cikin kayan matafiyan. An kama shugaban ƙungiyar, Ali Abubakar Mohammed (wanda aka fi sani da Bello Karama), tare da wasu abokan aikinsa. Hukumar ta ce mutanen ukun ba su da laifi kuma an zalunce su ne kawai. An saki su ne bayan bincike da kuma ƙoƙarin diflomasiyya na tsawon makonni. Lamarin ya tayar da hankali kan tsaro a filayen jirgin sama a Nijeriya da yadda masu aikata laifuka ke amfani da fasinjoji marasa laifi. Hukumar ta ce za a ɗauki ƙarin matakai don hana faruwar irin wannan lamari. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun...
    Tsohon Shugaban Ƙasar najeriya, Goodluck Jonathan, ya isa birnin Accra, na Ƙasar Ghana, domin halartar taron Democracy Dialogue na 2024 da Gidauniyarsa ta shirya tare da hadin gwiwar gwamnatin kasar. Taron na bana, mai taken “Dalilan Da Ke Sa Dimokuraɗiyya Ta Mutu”, zai hada shugabanni da masana don tattauna ci gaba, kalubalen, da makomar dimokuradiyya a Yammacin Afirka ke fuskanta. Jonathan ya ce yana fatan wannan tattaunawa za ta karfafa dimokuraɗiyya a yankin tare da kawo zaman lafiya, tsaro da kyakkyawan shugabanci. Taron Democracy Dialogue ya zama muhimmin dandali a kowace shekara a Yammacin Afirka don tattauna makomar dimokuradiyya, inda a baya ya kan jawo ’yan siyasa, kungiyoyi, da abokan hulda na kasa da kasa.  A wannan karon ana sa...
    Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Saudiyya na iya taka muhimmiyar rawa wajen hadin kan kasashen musulmi Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya jaddada cewa: Gwamnatin sahayoniyya ba za ta kuskura ta kai hari ko kai wa wata kasa ta Musulunci hari ba matukar kasashen musulmi suka hade kansu; kuma Saudiyya za ta iya taka muhimmiyar rawa a tafarkin hadin kan kasashen musulmi. A yayin ganawarsa da yarima mai jiran gado na Saudiyya Mohammed bin Salman a gefen taron Doha, Pezeshkian ya bayyana jin dadinsa da yadda dangantakar dake tsakanin kasashen biyu ke kara bunkasa, yana mai cewa: Zurfafa da karfafa hadin gwiwar dake tsakanin kasashen Iran da Saudiyya zai kare muradun kasashen biyu, da kuma muradun al’ummomin kasashen biyu,...
    Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Ta’addancin yahudawan sahayoniyya kan Qatar zalunci ne ga diflomasiyya Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya bayyana cewa: Harin wuce gona da iri kan kasar Qatar, wani hari ne da kungiyar yahudawan sahayoniyya ta shirya kai wa, da nufin dakile yunkurin diflomasiyya na kawo karshen kisan kiyashin da ake yi a Gaza. Shugaba Pezeshkian ya bayyana hakan ne a jiya Litinin a yayin taron gaggawa na shugabannin kasashen kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC da kungiyar hadin kan kasashen Larabawa dangane da harin da gwamnatin mamayar Isra’ila ta kai kan Qatar. Shugaban ya kara da cewa, wannan cin zarafi na diflomasiyya ya wuce matsayin laifi kawai; ya zama sanarwar aikin rashin kunya da ya...
    Ministan harkokin wajen Iran ya gana da takwarorinsa na Qatar, Turkiyya, Pakistan da Lebanon a Doha fadar mulkin kasar Qatar Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya gana da takwaransa na Qatar a gefen taron ministocin harkokin wajen kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC a birnin Doha. Doha ta sanar da cewa, fira ministan kasar Qatar kuma ministan harkokin wajen kasar ya yi nazari kan al’amuran yankin na baya-bayan nan yayin ganawarsa da ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi. A yayin wannan taro, harin da yahudawan sahayoniyya suka kaddamar a birnin Doha shi ne babban abin da ake tattaunawa akai. Araqchi yayi Allah wadai da harin da gwamnatin mamayar Isra’ila ta kai, yana mai tabbatar da goyon bayan Jamhuriyar...
    Adadin mutanen da suka yi shahada sakamakon kisan kiyashin da ‘yan sahayoniyya suke yi a Gaza ya doshi 65,000 Adadin mutanen da suka yi shahada sakamakon yakin da yahudawan sahayoniyya suka kakaba wa Falasdinawa a yankin Zirin Gaza ya karu zuwa shahidai 64,871 da kuma jikkatan wasu 164,610 tun daga ranar 7 ga watan Oktoban shekarar 2023. Bisa kididdigar baya-bayan nan da ma’aikatar lafiya ta Falasdinu ta fitar a zirin Gaza a ranar Lahadin da ta gabata, mutane 12,321 ne suka yi shahada yayin da wasu 52,569 suka samu raunuka tun bayan da gwamnatin mamayar Isra’ila ta sake komawa yaki kan Falasdinawa a ranar 18 ga watan Maris. A cikin sa’o’i 24 da suka gabata, Falasdinawa 68 ne suka yi...
    Amurka ta bayyana cewa: Harin da Isra’ila ta kai wa Qatar ba ya barazana ga kawancenta haramtacciyar kasar Isra’ila da Amurka Sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio ya fada a ranar Asabar din nan cewa: Harin da haramtacciyar kasar Isra’ila ta kai a Doha babban birnin kasar Qatar a makon jiya ba zai shafi dangantakar Amurka da Isra’ila ba, duk da rashin gamsuwar da shugaba Donald Trump ya yi da yakin da gwamnatin mamayar Isra’ila ke ci gaba da yi da kungiyar Hamas a Gaza. Kafin ya tashi zuwa birnin Tel Aviv na Isra’ila, Rubio ya jaddada cewa, gwamnatin Amurka na ci gaba da tallafawa yahudawan sahayoniyawa, yana mai cewa a wasu lokuta ana samun aukuwar lamarin da kan iya...
    Wakilin dindindin na Turkiyya a Majalisar Dinkin Duniya Ahmet Yıldız ya yi kakkausar suka kan harin da Isra’ila ta kai Doha, yana mai kiransa da “ta’addanci” da kuma wani yunkuri na tada zaune tsaye a yankin yammacin Asiya Da yake magana a madadin kungiyar hadin kan kasashen musulmi (OIC) yayin wani zama na musamman na kwamitin sulhu na MDD da aka gudanar a ranar Alhamis, Yıldız ya yi tir da harin a matsayin wani bangare na tsare-tsare na Isra’ila da kuma kokarin dakile zaman lafiyar yankin. An kira taron na musamman ne a matsayin martani ga harin da Isra’ila ta kai kan wasu manyan jami’an Hamas a babban birnin Qatar.. Sanarwar ta yi Allah wadai da kakkausar murya kan wannan...
    Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya tarbi tagwayen da aka haifa manne da juna, inda aka raba su da juna ta hanyar yi musu tiyata a Ƙasar Saudiyya. Tagwayen waɗanda ’yan asalin Najeriya ne, sun iso filin jirgin sama na Malam Aminu Kano, inda tawagar Saudiyya ta tarbe su. Ambaliya: SEMA ta raba kayan tallafi ga gidaje 90 a Gombe ’Yan bindiga sun harbi fasinjoji 2, sun sace makiyaya a Neja An yi musu tiyata a Asibitin Ƙwararru na Yara King Abdullah da ke Riyadh, bisa umarnin Sarki Salman bin Abdulaziz Al-Saud da Yarima Mohammed bin Salman. Hassana da Husaina sun tafi Saudiyya tun a watan Oktoban 2023, inda likitoci suka gano cewa suna manne da juna ne ta...
    Mai ba da shawara ga Jagora kan harkokin kasa da kasan ya jaddada ccewa; Dole ne duniya ta daina yin shiru game da zaluncin ‘yan sahayoniyya Ali Akbar Velayati mai ba da shawara ga jagora kan harkokin kasa da kasa ya yi Allah wadai da wuce gona da irin da yahudawan sahayoniyya suka kai a kasar Qatar, yana mai cewa: Dole ne duniya ta daina yin shiru kan zaluncin yahudawan sahayoniyya saboda ba su san iyaka kan laifukansu ba. Velayati ya bayyana a shafinsa na twitter game da harin da gwamnatin ‘yan sahayoniyya suka kai wa kasar Qatar yana mai cewa: Keta dokokin kasa da kasa da keta alfarmar kasashe ya zama al’ada ga ‘yan sahayoniyya, kuma dole ne duniya...
    Jagoran juyin juya halin Musulunci ya jaddada yin kira ga al’ummar Musulmi cewa: Wajibi ne kasashen musulmi su yanke alakarsu da ‘yan sahayoniyya Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya jaddada cewa: Dole ne kasashen musulmi su yanke duk wata huldar kasuwanci da siyasa da gwamnatin ‘yan sahayoniyya azzaluma tare da mayar da ita saniyar ware. Jagoran juyin juya halin Musulunci ya jaddada cewa: Dole ne a fuskanci bala’o’in da muguwar gwamnatin ‘yan sahayoniyya ta haifar a Gaza. Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya yi tsokaci kan mummunan halin da ake ciki a zirin Gaza inda ya ce: Dole ne kasashen da suke gudanar da zanga-zangar a yau musamman kasashen musulmi su yanke duk wata huldar kasuwanci...
    Rundunar sojin Yeme ta sanar da kai hare-hare guda 8 da jirage sama marasa matuka ciki kan muhimman wurare a Isra’ila Dakarun sojin Yemen sun sanar da yammacin jiya cewa, sun kai wasu manya-manyan farmakin soji ta hanyar amfani da jiragen saman yaki  marasa matuka ciki guda takwas a kan wasu wurare da dama a yankunan Falasdinawa da aka mamaye. An kai hare-haren ne kan filin jirgin saman Ramon da muhimman wurare da na sojoji da suka hada da Negev, Umm al-Rashrash, Ashkelon, Ashdod, da Jaffa. Domin jaddada goyon baya ga al’ummar Falastinu da ake zalunta da ‘yan gwagwarmayarsu masoya, da kuma mayar da martani kan laifukan kisan kiyashi da kakaba yunwa da makiya yahudawan sahayoniyya suke aikatawa kan ‘yan...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran abbas Aragchi ya yi kira ga kasashen turai 3 EU a takaice su dawo kan hanyar diblomasiyya don warware rikicin shirin Nukliyar kasar Iran wanda ya zo cikin yarjeniyar JCPOA na shekara ta 2015.  Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Argchi yana fadar haka a yau Lahadi  a cikin wani rubutun da yayi a cikin Jaridar Guadian na kasar Burtania. Ministan ya kammala da cewa idan sun ki dawowa kasashen turai ne za’a ware nan gaba, don ba zasu taba cimma manufofinsu a kan Iran tare da sake maida takunkuman MDD kan kasar Iran ba. Tsarin Snpback dai wani tsari ne wanda zai bawa kasashe 6 wanda suke cikin yarjeniyar JCPOA danar...
    “Abin da Jibrin ya faɗa ba wai adawa da jam’iyya ba ne. Kowane ɗan siyasa yana da ‘yancin sauya jam’iyya. Ko Shugaba Bola Tinubu ya taɓa sauya jam’iyya kafin ya zama shugaban ƙasa,” in ji Doguwa. Ya kuma gargaɗi Dungurawa da ya daina korar ‘ya’yan jam’iyyar ba bisa ƙa’ida ba, inda ya ce za su kai ƙara kotu idan ɓangaren nasa ya ci gaba da yin haka. Wannan sabon rikici ya sake nuna yadda NNPP ke ƙara tarwatsewa a Kano tun bayan zaɓen 2023, inda har yanzu ake taƙaddama kan shugabanci. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin...
    Gwamnatin Saudiyya ta sanar da sanya tarar kuɗi kan masu aikata ayyukan da suka shafi rashin ɗa’a a cikin al’umma, musamman a lokutan salla, domin kare mutunci, tsaro da kuma zaman lafiya. Sabbin matakan, wanda za a fara aiwatarwa nan take, sun shafi masu sanya kaya marasa mutunci a bainar jama’a, da masu kunna kiɗa lokacin salla, da masu bahaya ko zubar da shara a wuraren da doka ta haramta. Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 13 a Borno Hisbah ta kama mai safarar mutane da mata 12 A cewar sabuwar doka, duk wanda aka kama da kunna kiɗa a lokacin salla zai biya tara ta Riyal 1,000 (kimanin Naira 390,000) a karon farko, kuma idan aka sake kama shi, tarar...
    Babban sakataren kwamitin kolin tsaron kasar Iran ya tattauna da takwaransa na Birtaniyya kan tattaunawar nukiliya da hanyoyin kawar da sabani tsakanin Iran da tawagar Turai Mai bai wa fira ministan kasar Birtaniya shawara kan harkokin tsaro, Jonathan Powell, ya tattauna kan farfado da shawarwarin makamashin nukiliyar da kuma warware hanyoyin da za a bi wajen kawo karshen rikicin a wata tattaunawa ta hanyar wayar tarho da Ali Larijani, babban sakataren kwamitin kolin tsaron kasar Iran. Bangarorin biyu sun tattauna batun sake farfado da shawarwarin makamashin nukiliyar da kuma neman hanyoyin da za a bi don magance matsalar makamashin nukiliyar Iran ta hanyar tattaunawa. A cikin wannan tattaunawa ta wayar tarho da aka gudanar a yammacin yau Alhamis, bangarorin biyu...
    Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran ya tattauna kan yadda ake gudanar da harkokin diflomasiyyar Iran a taron kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran kan harkokin shari’a da kasa da kasa, Kazem Gharibabadi, ya bayyana cewa: Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya yi kokarin diflomasiyya sosai a taron kungiyar hadin gwiwar Shanghai (SCO) da aka yi a kasar China. A yayin jawabinsa daban-daban a taron koli na Shanghai, kuma ya gabatar da tsare-tsare don kara kaimi ga kungiyar. Kazem Gharib-abadi ya bayyana muhimman batutuwan da suka shafi taron koli da tarurruka a wani sako da ya wallafa a dandalin sada zumunta na X, wanda ya ce: Shawarwari na shugaban kasa a taron koli na Shanghai...
    Cibiyar Ayyukan Daular Usmaniyya da ke Sakkwato ta bayyana aniyar karrama Mai Martaba Sarkin Zazzau, Malam Ahmed Nuhu Bamalli CFR, da lambar yabo ta musamman saboda rawar da ta ce yana takawa wajen ƙarfafa haɗin kai da raya zumunci tsakanin ’ya’yan Daular Usmaniyya. A cikin sanarwar da cibiyar ta fitar mai ɗauke da sa hannun shugabanta kuma Wazirin Sakkwato, Farfesa Sambo Wali Junaidu, ta ce za a karrama Sarkin tare da wasu fitattun ’yan Najeriya guda shida a babban taron shekara-shekara da cibiyar ke shiryawa. Gwamnatin Tarayya ta ɓullo da sabon manhajin karatun firamare da sakandire Manchester City ta ɗauki golan PSG, Gianluigi Donnarumma Taron zai gudana ne a ranar Alhamis, 11 ga watan Satumba, 2025, a Cibiyar Karatun Alƙur’ani...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Sau da dama ibti’lai kan faru da wasu mutane wanda ya kamata ace sun bi hanyoyi don a biya su diyya.   Sai dai masana na bayyana cewa sau da dama mutane basu san honyoyin da ya kamata subi don neman hakkokin su ba. NAJERIYA A YAU: Me Sakamakon Zaben Ribas Ke Nunawa Game Da Sulhun Wike Da Fubara? DAGA LARABA: Abin Da Ya Sa Wasu Maza Ba Sa Son Haihuwa Shirin Najeriya  A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan hanyoyin da mutane zasu bi don neman diyya idan an zalunce su. Domin sauke shirin, latsa nan
    Ya bayyana cewa, matan sun fito ne daga jihohin Kano, Katsina, Borno, Jigawa, da Zamfara, inda aka yi musu alkawuran samun ingantattun ayyukan yi a kasar ta Saudiyya.   An kama daya daga cikin wadanda ake zargi da safarar matan mai suna Mohammed Saleh mai shekaru 45 da haihuwa.   Babale ya ce, ana ci gaba da kokarin damke wasu da ake zargi da hannu wajen safarar mutanen. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Majalisar dokokin kasar Turkiyya ta yi tir da kissan kiyashin da HKI take aikatawa a Gaza sannan ta amince da hana jiragen fisinja na HKI wucewa ta sararin samaniyar kasar. Banda haka ta bukaci a kore daga Majalisar dinkin duniya. Majalisar ta bukaci a kula da hakkin Falasdinawa a fagen kasashen a kuma kawo karshen yakin da ke faruwa a gaza, a ranar jumma’a ce majalisar dojojin kasar ta Turkiyya ta amince da wadannan matakan, wadanda suka dakatar da harkokin kasuwanci kwata-kwata da HKI da hana sararin samaniyar kasar ga jiragen HKI. Ya bukaci dukkan shugabannin bangariri na majalisar su sanyawa dokar hannu don ya samu matsayin gwamnatin da mutanen turkiyya gaba daya. Kudurin ya bukaci a kafa kasar Falasdinu...
    Shugaban kasar Sin kuma babban sakataren kwamitin kolin JKS Xi Jinping, ya jaddada bukatar kara azamar inganta da’a a harkokin jam’iyya, da dorewa bisa turbar aiwatar da ka’idojin gudanar da kudurorin nan takwas, na shugabancin jam’iyyar kwaminis game da inganta da’a a harkokin jam’iyyar.   Xi Jinping, wanda kuma shi ne shugaban hukumar gudanarwar rundunar sojojin kasar Sin, ya yi tsokacin ne cikin wani umarni da ya bayar, ga wani taron tattaunawa don kara gina jam’iyyar kwaminis a yau Jumma’a a nan birnin Beijing. (Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Jami’in kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen ya jaddada cewa: A shirye suke su ci gaba da yaki na dogon lokaci da gwamnatin mamayar Isra’ila Jami’in kungiyar Ansarullah ta Mabiya Huthi ta kasar Yemen Mohammed al-Bukhaiti ya bayyana cewa: A shirye al’ummar Yemen su ci gaba da yaki na tsawon lokaci da gwamnatin mamayar Isra’ila, kuma suna farin ciki da arangama kai tsaye da haramtacciyar kasar Isra’ila. Ya kara da cewa, za a ci gaba da daukar matakan soji na goyon bayan Gaza muddin gwamnatin ta ci gaba da yakin da take yi a Gaza. Ya yi nuni da cewa harin da gwamnatin mamayar Isra’ila ta kai kan birnin Sana’a ba zai shafi goyon bayan da al’ummar Yemen ke yi ga...
    Wannan na zuwa ne bayan samun labarin kama wata mai suna Maryam Hussain Abdullahi a Saudiyya da zargin fataucin miyagun ƙwayoyi a daidai lokacin da take aikin Umara.   Da yake bayyana yadda aka bankaɗo harƙallar ta hanyar, wadda ke jefa mutanen da ba su ji, ba su gani ba cikin masifa, ya ce ‘yan uwan wadanda aka kama ne a Saudiyya ne suka kawo ƙorafi ga hukumar NDLEA cewa an kama ’yan uwan su a Saudiyya, inda cikin gaggawa hukumar ta ƙaddamar da bincike.   “’Yan Nijeriya da aka kama a Saudiyya su ne: Maryam Hussain Abdullahi da Abdullahi Bahijja Aminu da Abulhamid Sadiq waɗanda suka hau jirgin Ethiopian Airline mai lamba ET940, wanda ya bar Kano a ranar...
    Wasu daga cikin ’yan kasuwar sun yi kira ga gwamnati da ta sake duba matsayar ta, inda suka ce kasuwar ce tushen rayuwarsu da iyalansu, kuma rushe ta zai kara jefa su cikin talauci da rashin aikin yi. Haka kuma, sun yi barazanar kai ƙarar gwamnati kotu idan aka ƙi biyan su diyya, domin a cewarsu, an tauye musu haƙƙin kasuwanci da kuma dukiyar da suka shafe shekaru suna tarawa. Sai dai gwamnatin Legas ta ce irin waɗannan ayyuka na rusau na daga cikin shirinta na zamanantar da manyan kasuwanni, don su dace da tsarin birane na zamani da kuma kare muhalli. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da...
    Wasu daga cikin ’yan kasuwar sun yi kira ga gwamnati da ta sake duba matsayar ta, inda suka ce kasuwar ce tushen rayuwarsu da iyalansu, kuma rushe ta zai kara jefa su cikin talauci da rashin aikin yi. Haka kuma, sun yi barazanar kai ƙarar gwamnati kotu idan aka ƙi biyan su diyya, domin a cewarsu, an tauye musu haƙƙin kasuwanci da kuma dukiyar da suka shafe shekaru suna tarawa. Sai dai gwamnatin Legas ta ce irin waɗannan ayyuka na rusau na daga cikin shirinta na zamanantar da manyan kasuwanni, don su dace da tsarin birane na zamani da kuma kare muhalli. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da...
    shafin Jagoran juyin juya halin Musulunci a cikin harshen Yahudanci ya bayyana cewa: ‘Yan sahayoniyya sune wadanda aka fi kyamata a duniya Shafin Jagoran juyin juya halin Musulunci na yaren yahudanci a shafin sada zumunta na X ya rubuta cewa: Makiyar al’ummar Iran na kan gaba a yau ita ce, gwamnatin ‘yan sahayoniyya wacce ita ce mafi kyamata a tsakanin al’ummar duniya. Shafin yanar gizo na KHAMENEI.IR na yaren yahudanci ya wallafa wani kaso na jawabin Jagoran a jiya litinin a wajen taron juyayin shahadar Imam Ali dan Musa al-Rida Jagoran shiriya na Iyalan gidan Manzon Allah {s.aw}. Sanarwar ta kara da cewa: “Makiyar al’ummar Iran a yau, ita ce gwamnatin ‘yan sahayoniyya, wacce duniya ta fi kyama a duniya....
    Makami mai linzami na Yemen na fission ballistic shi ne babban mafarkin da ke firgita ‘yan sahayoniyya Jaridar Isra’ila, The Jerusalem Post, ta yi bayanin cewa: Harba makamai masu linzami na gungu fission ballistic daga Yemen yana kara yawan barazanar tsaro, tare da dagula Shirin kakkabo shi, kuma yana janyo wahalar murmurewa daga barnarsa. Jaridar ta ce amfani da makamai masu linzami na gungu fission ballistic da ‘yan Yemen suka yi a kan abokan gabar Isra’ila na wakiltar wani gagarumin ci gaba mai kunshe da damuwa, tare da lura da cewa wadannan makamai masu linzami suna mayar da tsarin kariya na makamai masu linzami na gargajiya irin su Arrow ko Sling na David marasa amfani saboda ba su da kayan...
    ’Yan Arewa a Kasuwar Alaba Rago, shahararriyar kasuwar ’yan Arewa a Jihar Legas sun roki gwamnatin jihar ta biya su diyya kan asarar da suka yi sakamakon rushe kasuwar da gwamnati nta yi. Sun bayyana cewa asarar da suka tafka ta haura Naira biliyan 20 bayan Gwamnatin Legas ta rusa masallatai sama da 40 da shaguna kimanin 3,000 a Kasuwar wadda suka kafa shekara 45 da suka gabata a jihar. A karo na biyu a ’yan kwanakin nan mahukunta a Jihar Legas suka rushe sassa da dama na kasuwar, wadda ta yi fice da kasuwancin kayan abinci da dabbobi da karafa da sauran kayan masarufi, wacce Hausawa suka kafa a shekarar 1979. A cikin watan Mayun 2024, jami’an hukumar ’yan...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Duk wanda ya shekara arbain zuwa sama ya san irin tarbiyyan da ya samo daga wurin iyayen sa a da baya can, irin mu’amalan dake tsakanin sa da iyaye har ma da shakuwan dake tsakanin ‘ya’ya da iyaye.   A yanzu kuwa abubuwa sun canza daga yadda aka san su, inda abubuwa suka rincabe sukayi wa iyaye yawa. Daya daga cikin manyan sauyin da aka samu sun hada da aikin gwamnati ko aikin wata da iyaye mata suke yi a wannan zamani wanda hakan a wasu lokuta ke barazana ga irin kulawan da ‘ya’ya suke samu. NAJERIYA A YAU: Ayyukan da fasahar AI za ta iya raba mutane da su a nan gaba...
    Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya isa kasar Saudiyya domin halartar wani babban taro na majalisar ministocin harkokin wajen kungiyar hadin kan kasashen musulmi. A yayin da yake jagorantar tawagar diflomasiyya ta kasar Iran, Araghchi ya isa birnin Jeddah na kasar Saudiyya a jiya Lahadi domin halartar taron kungiyar OIC da za a bude a wannan  Litinin bisa bukatar da  Iran da kuma wasu kasashe gabatar na yin hakan. A yayin taron na kwanaki biyu, mahalarta taron za su tattauna kan matsalolin  jin kai a zirin Gaza, da yiwuwar kawo karshen kisan kiyashin da Isra’ila ke yi wa al’ummar Palastinu, da kuma gurfanar da ‘yan sahayoniya masu laifi a gaban kotu. Kungiyar ta OIC ta ce taron zai mayar...
    A yau ne babbar jam’iyyar adawa ta PDP za ta gudanar da zama na 102 na Kwamitin Zartarwa na Ƙasa (NEC), inda ake sa ran ta yanke hukunci kan wasu jiga-jiganta da ake zargi da cin dunduniyarta, ciki har da Ministan Abuja Nyesom Wike da tsohon Gwamnan Jihar Binuwai, Samuel Ortom. Majiyoyi a jam’iyyar sun ce a yayin taron, za a gabatar da rahoton kwamitin ladabtarwa ƙarƙashin jagorancin Tom Ikimi, wanda ya ba da shawarar ɗaukar mataki a kan waɗanda ake zargi da yi wa jam’iyyar zangon ƙasa. Har ila yau, taron zai tattauna shirin gudanar da babban taron jam’iyya na ƙasa a Ibadan a ranakun 15 da 16 ga watan Nuwamba, inda za a zaɓi sababbin shugabanni. Kazalika rahoton...
    Ɗariƙar Tijjaniyya a Jihar Gombe, ta yi babban rashi bayan rasuwar ɗaya daga cikin fitattun malamanta, Sheikh Umar Bojude. Sheikh Bojude shi ne babban limamin Masallacin Juma’a na Alhaji Gidado Dalibi Yahaya (AG Dalibi). Japan za ta bai wa Najeriya rancen $190m don inganta wutar lantarki Rikici ya kunno kai a jam’iyyar ADC a Gombe Malamin ya rasu a ranar Lahadi, kuma an yi jana’izarsa a unguwar Jan Kai da misalin ƙarfe 5 na yamma. Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya aike da saƙon ta’aziyyarsa ta bakin Daraktan Yaɗa Labaransa, Isma’ila Uba Misilli. Ya bayyana rasuwar malamin a matsayin babban rashi ga ɗariƙar Tijjaniyya, iyalansa da kuma al’ummar jihar. “Ina miƙa ta’aziyyata ga iyalan marigayi, ɗariƙar Tijjaniyya, Fityanul Islam...
    Shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya yi ta’aziyya ga gwamnatin Jihar Kebbi da al’ummar jihar bisa rasuwar Sarkin Zuru, Mai Martaba, Manjo Janar Muhammadu Sani Sami (Gomo II). A cikin wata sanarwa da mai bai wa shugaban ƙasan shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai Bayo Onanuga ya fitar, ya bayyana rasuwar Sarkin  a matsayin “babban rashi ga ƙasa,” inda ya tuno irin hidimar da marigayin ya yi a matsayinsa na tsohon gwamnan soja na Jihar Bauchi da kuma  hidimarsa a matsayin basarake. Shugaba Tinubu ya lura cewa Najeriya za ta daɗe tana tuna gudummawar tsohon janar ɗin, wanda kuma ya yi yaƙi a matsayin ƙaramin hafsan soja lokacin Yaƙin Basasa. Shugaban ƙasa ya kuma yabawa jagorancin...
    Sarkin Zuru na Jihar Kebbi, ritaya Manjo-Janar Muhammadu Sani Sami, ya rasu yana da shekaru 81 a duniya. Kwamishinan Harkokin Ƙananan Hukumomi da Masarautu na Jihar Kebbi, Garba Umar-Dutsinmari, ne ya tabbatar da rasuwar mai martaba a cikin wata sanarwa da aka fitar a Birnin Kebbi ranar Lahadi. Ya bayyana cewa Sarkin ya rasu ne a daren Asabar a wani asibiti da ke birnin London bayan fama da jinya. Marigayin ya bar mata hudu da ‘ya’ya bakwai. A cikin sakon ta’aziyya, Gwamnatin Jihar Kebbi ta bayyana alhinin ta kan rasuwar Sarkin, tare da mika ta’aziyya ga iyalansa, Majalisar Masarautar Zuru, al’ummar Zuru da daukacin Jihar Kebbi. “Gwamnati na roƙon Allah Madaukakin Sarki da ya gafarta masa kurakuransa, ya kuma ba...
    Jakadan Iran a Saudiyya Alireza Enayati ya tabbatar da ci gaba da tuntubar juna tsakanin babban hafsan hafsoshin sojin Iran da ministan tsaron Saudiyya. A wata hira da kamfanin dillancin labarai na IRNA Alireza Enayati ya yi nuni da cewa, Saudiyya na kallon alakar ta da Iran a matsayin alaka mai matukar muhimamnci, kamar yadda ita ma Iran din take Kallon wannan alaka tsakaninta da Saudiyya.  Inda ya kara da cewa “Mun ga irin goyon bayan da Saudiyya ta bayar kan shawarwarin nukiliyar da aka yi a baya-bayan nan, wanda hakan abin yabawa ne.” Har ila yau, ya yi ishara da cewa, magance da kuma kula da al’amurran da suka shafi yankin gabas ta tsakiya abu ne mai yiyuwa idan...
    “Tsarin mulkin ADC ta bayyana cewa duk wanda ke neman zama shugaban jam’iyyar, dole ne ya kasance mamba nagari na jam’iyya. Wannan shi ne muhimman bukata ta asali wadda ba za a iya yin watsi da ita ko kauce mata ta kowace hanya ba. “A cewar tsarin mulkin ADC, hanyar da ta dace don cike gurbin jagoranci bayan tafiyar Cif Nwosu ita ce, ta hanyar taron kwamitin zartarwa na kasa.” Tsaagin jam’iyyar ta sake tabbatar da cewa Alhaji Nafiu shi ne halastaccen shugabanta na kasa tare da kira ga ‘ya’yan jam’iyyar da su ci gaba da kasancewa cikin kwanciyar hankali da hadin kai. Ya kuma bayyana kwarin giwa kan ikon hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) na kiyaye...
    Ina mika sakon gaisuwata zuwa ga Mahaifana, da ‘yan’uwana Fatima Muhammad, Sadiya Muhd, Tahir Muhammad, sai kawayena na tsohuwar makarantarmu da na unguwarmu kamai Zainab Abdulkadir, Shamsiyya Muhammad, Marakisiyya Shu’aib, da fatan sun yi Juma’a lafiyya. Saki daga Kassim Bello Muhammad Makarfi daga Jihar Kaduna Ina yi wa ‘yan’uwa musulmi na fadin duniya fatan alheri, da ilahirin ahalina na kusa da na nesa kamar su Amir Saleh, Amina Bello Makarfi, Sa’adatu Muhammad Kanwa, Kamal Sagir Garba, da dai sauransu. Da fatan sun yi juma’a lafiyya, Amin. Halima Galadima Bebeji daga jihar Kano Idna gaishe da Mahaifiyata Hajiyya Zahra’u Mamman, da mahaifina Alhaji Muhammad Galadima Babeji. Sai sakon gaisuwata zuwa ga al’ummar ‘DYZ Group’ kamar su Khadijah Ibrahim Umar Jambulo(Deeja J),...
    Jagoran kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen ya jaddada cewa: Makiya yahudawan sahayoniyya suna kai hari ga daukacin al’ummar Falasdinu ne Babban sakataren kungiyar Ansarullahi ta kasar Yemen Sayyed Abdulmalik Badr al-Din al-Houthi ya tabbatar da cewa: Makiya yahudawan sahayoniyya suna kai hari kan dukkanin al’ummar Falastinu ne, yana mai jaddada cewa: Makiyan ‘yan sahayoniyya sun aikata kowane irin laifi da kowane nau’i na wuce gona da iri kan al’ummar Falastinu a zirin Gaza. A jawabin da ya gabatar kai tsaye kan sabbin ci gaban da ake samu a hare-haren wuce gona da iri kan zirin Gaza da kuma ci gaban yanki da na duniya, Sayyed al-Houthi ya yi nuni da cewa, yawan hare-haren da gwamnatin mamayar Isra’ila ta kai cikin...
    Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Masana Iran da suka yi shahada a lokacin yaki babu laifin da suka aikata ban da hidima ga al’ummarsu Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya yi kakkausar suka kan shirun da masu da’awar kare hakkin bil’adama da zaman lafiya da tsaro suka yi dangane da laifukan gwamnatin ‘yan sahayoniyya, yana mai cewa: Masana kimiyyar Iran da suka yi shahada ba su aikata komai ba face hidimar al’ummar Iran a fadin duniya, amma gwamnatin ‘yan sahayoniyya ta kashe su. Masoud Pezeshkian ya halarci bikin karrama masana kimiyya da suka yi shahada a tsangayar koyar da fasahar nukiliya ta jami’ar Shahid Beheshti a safiyar ranar Talata, inda ya jinjinawa hotunan malaman kimiyya da suka yi shahada...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kaduna ta shawarci maniyyata aikin Hajjin shekarar 2026 da su fara shirin biyan kudaden ajiya. Kiran ya biyo bayan taron da Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Kasa (NAHCON) ta gudanar tare da hukumomin Alhazai na jihohi, inda aka bayar da shawarar ajiyar naira miliyan 8 da rabi ga masu niyyar zuwa aikin Hajji, kafin a sanar da hakikanin kudin aikin Hajjin shekarar 2026. A cikin wata sanarwa, mai magana da yawun hukumar, Yunusa Mohammed Abdullahi, ya shawarci wadanda ba su da fasfo da su gaggauta zuwa Hukumar Shige da Fice ta Kasa domin yin nasu, yana mai cewa shi ne ake amfani da shi wajen hada takardun tafiya. Najeriya ta sake samun kujeru...
    Chen Xiaoguang ya bayyana cewa, dabarun da aka saba amfani da su na yaki da sauro suna da tasgaro. Ya ce tarko da gidan sauro na kama sauro ne marasa shan jini, yayin da tsarin kama sauro cikin mazubi da ruwa, ke kama sauro masu jan jini da yin kwai.   Ya kara da cewa, abun da suka kirkiro na’ura ce dake gudanar da ayyuka biyu a lokacin da ake ciki, kuma tana da matukar inganci wajen sa ido da bibiyar sauro. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a...
    Kasashen Turai biyar na kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya sun ki amincewa da matakin mamaye Gaza Wakilin dindindin na Slovenia ya gabatar da wata sanarwa ga kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya a madadin Burtaniya, Faransa, Denmark, da Girka, yana mai cewa: “A matsayinsu na kasashen Birtaniya, Denmark, Faransa, Girka, da Slovenia, sun kira taron gaggawa na kwamitin tsaron Majalisar kan halin da ake ciki a Gaza. Suna Allah wadai da matakin da haramtacciyar kasar Isra’ila ta dauka na fadada ayyukanta na soji a Gaza. Ya kuma jaddada cewa: Hakan yana barazana tare da keta dokokin kasa da kasa, yana mai kiran gwamnatin mamayar Isra’ila da ta hanzarta janyewa daga wannan matsayi.  Ya jaddada cewa: Duk wani matakin mamaye yankunan Falasdinawa...
    Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi Allah wadai da matakin da haramtacciyar kasar Isra’ila ta dauka na mamaye zirin Gaza Ma’aikatar harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi Allah wadai da matakin baya-bayan nan da majalisar ministocin gwamnatin ‘yan sahayoniyya ta dauka na mamaye yankin zirin Gaza da korar al’ummarta, tare da la’akari da hakan a matsayin wani mataki na kammala shirin kisan gillar ga Falasdinawa da suke yi da kawar da asalin wanzuwar Falastinu. A cikin bayanin da ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta fitar dangane da abubuwan da suke faruwa a zirin Gaza da yankunan Falastinu da aka mamaye, ma’aikatar harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta bayyana matukar damuwarta da takaicin yadda ake ci gaba da...
    Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta bayyana cewa: Shirin gwamnatin mamayar Isra’ila shi ne shirin share al’umma Falasdinu daga kan doron kasa Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya bayyana cewa: Shirye-shiryen da gwamnatin ‘yan sahayoniyya take yi na mamaye yankin Zirin Gaza da kuma tilastawa al’ummar yankin gudun hijira wani karin shaida ne na musamman da wannan gwamnatin take da niyyar aikata kisan kiyashi a Falastinu da ta mamaye. Ismail Baqa’i ya bayyana shirin gwamnatin ‘yan sahayoniyya na mamaye garin Gaza da sojoji da kuma tilastawa mazauna yankin kauracewa gidajensu a matsayin wani shiri na kammala kisan gillar da  take yi wa al’ummar Falastinu, yana mai jaddada tofin Allah tsine da Allah wadai da wannan mummunan cin zarafi....
    Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya yi kira da a gaggauta janye shirin gwamnatin mamayar Isra’ila na mamaye Gaza Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya António Guterres ya soki shirin gwamnatin mamayar Isra’ila na kwace iko da birnin Gaza a jiya Juma’a, inda mai magana da yawunsa ya bayyana matakin a matsayin wani abu mai hadari. A nasa bangaren, Volker Turk, babban jami’in kare hakkin bil’adama na Majalisar Dinkin Duniya, ya yi kira a jiya Juma’a da a dakatar da shirin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila da ke da nufin wanzar da cikakken ikon soji a zirin Gaza ta hanyar mamaya. A cikin wata sanarwa da ta fitar sa’o’i kadan bayan da majalisar ministocin tsaron gwamnatin mamayar Isra’ila ta amince da kudurin...
    Fitattun matsayi na kasashen Larabawa da kungiyoyi sun yi Allah wadai tare da tofin Allah tsine da matakin gwamnatin mamayar Isra’ila na mamaye Gaza Kasashe da kungiyoyin Larabawa sun yi Allah wadai da matakin da majalisar ministocin gwamnatin mamayar Isra’ila ta dauka mai hatsari na sake mamaye yankin Zirin Gaza tare da tilastawa Falasdinawa kusan miliyan daya gudun hijira daga birnin Gaza da arewacin zirin Gaza zuwa kudancin kasar. A cikin sanarwar da suka fitar a jiya Juma’a, sun yi la’akari da wannan shawarar da kuma shirin da gwamnatin mamayar Isra’ila ke yi a matsayin mai hatsarin gaske da zai haifar da bala’in jin kai a zirin Gaza kuma ba za ta taimaka wajen kawo karshen rikicin ba, suna masu...
    “Su dai kawai abin da suke alfahari da shi, shi ne dukiya, yawan gidaje da jirage. Ba su san cewa mutane na kallonsu a matsayin ɓarayi ba.” Sanusi II, ya ƙara da cewa ba shugaban ƙasa ko gwamna kaɗai ke da laifi ba, hatta shugabannin addini da sarakuna ma sun ɓaci a yanzu. “Yawancin shugabanninmu sun shiga ruɗani, babu wanda ya tsira,” in ji shi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp