Jami’an Tsaro Sun Tarwatsa Masu Zanga-zangar #FreeNnamdiKanuNow A Abuja
Published: 20th, October 2025 GMT
Gamayyar Jami’an tsaron sun hada da Rundunar ‘yansandan Nijeriya (NPF) da Guards Brigade, DSS da NSCDC, inda suka tsaurara matakan tsaro a kusa da fadar shugaban kasa, tun ranar Lahadi.
Sun kafa shingaye a manyan hanyoyin da suka kai ga fadar shugaban kasa (Villa), Majalisar Dokoki ta kasa, hedikwatar Kotun daukaka kara, hedikwatar sojoji da kuma dandalin taro na Eagle Square.
এছাড়াও পড়ুন:
NAPTIP ta daƙile yunƙurin safarar mutum 7 daga Kano zuwa Saudiyya
Hukumar Hana Safarar Mutane (NAPTIP) shiyyar Kano, ta kama wani mutum da ya yi yunƙurin safarar wasu mata bakwai zuwa Saudiyya.
Jami’an NAPTIP sun kai samame wani gida a Kano a ranar 2 ga watan Nuwamba, 2025, bayan samun bayanan sirri, inda aka ɓoye matan da ake shirin safararsu.
Na gana da Tinubu kan Kanu ba batun sauya sheƙa ba — Gwamnan Abia ’Yan Najeriya suna da ƙwarin guiwa a kaina, ba zan ba su kunya ba — Ministan TsaroA cewar Mohammed Habib, Jami’in Hulɗa da Jama’a na NAPTIP a Kano, an ajiye matan a gidan ne yayin da ake shirin tura su Saudiyya domin yin aikatau.
Ya ce, “Bincike ya nuna cewa biyu daga cikin waɗanda aka ceto ’yan Nijar ne, yayin da biyar kuma ’yan Najeriya ne.”
Ya ƙara da cewa, “An kai matan Accra a Ghana, inda aka yi musu biza. Kuma duka aikin da za a musu bashi ne, inda kowacce za ta biya Naira miliyan 10, idan sun yi aikin wahala a Saudiyya .”
NAPTIP ta bayyana cewa an riga an kammala shirin tura matan filin jirgin saman Abuja a ranar 3 ga watan Disamba, 2025, wanda a nan aka shirya tafiyarsu Saudiyya.
Hukumar ta ce an kama mutum ɗaya, yayin da sauran waɗanda ke da hannu a lamarin suka tsere.
Jami’in, ya tabbatar da cewa hukumar na ci gaba da bincike domin kama sauran da suka tsere.