Iwobi Na Dab Da Kafa Tarihi A Gasar Firimiya
Published: 18th, October 2025 GMT
Ɗan wasan gaba na ƙungiyar Fulham, Alex Iwobi, na dab da kafa sabon tarihi a gasar Firimiya a matsayin ɗan wasan Nijeriya da ya fi buga wasanni a tarihin gasar. Idan Iwobi ya buga wasan da Fulham za ta kara da Arsenal a filin Craven Cottage yau Asabar, zai zama ɗan wasan Nijeriya na farko da ya kai buga wasanni 299 a Firimiya.
A halin yanzu, Iwobi ya buga wasanni 298, inda yake daidai da tsohon ɗan wasan Newcastle United, Shola Ameobi, wanda ya riƙe wannan tarihin tsawon lokaci. Wannan zai kasance babbar nasara ga Iwobi wanda ke da shekaru 29 a duniya, tun da ya fara wasansa na farko a Firimiya ranar 27 ga watan Oktoba, lokacin da Arsenal ta fafata da Swansea City.
Alex Iwobi Ya Kafa Tarihi A Gasar Firimiya Osimhen Na Dab Da Komawa Galatasaray Na DindindinIwobi, wanda ya fara wasansa a Arsenal, ya taka leda a ƙungiyoyin uku a gasar Firimiya — Arsenal, Everton, da kuma Fulham inda yake bugawa yanzu. A duk waɗannan ƙungiyoyi, ya zama ginshikin tawaga saboda bajintarsa da ƙwazo a fili.
Tun bayan zuwansa Fulham, Iwobi ya tabbatar da matsayin sa a ƙungiyar, yana taimakawa wajen inganta tsarin wasan ƙungiyar. Idan ya buga wasan yau, zai kafa tarihi a matsayin ɗan wasan Nijeriya da yafi taka leda a gasar Firimiya tun fara gasar a shekarar 1992.
ShareTweetSendShare MASU ALAKAকীওয়ার্ড: a gasar Firimiya
এছাড়াও পড়ুন:
Za a kafa kamfanin ƙera kayan sola a Kano
Gwamnatin Jihar Kano ta ce nan ba da jimawa ba za a fara ƙera fanel da sauran kayayyakin samar da wutar lantarki daga hasken ranar a jihar.
Hakan a cewar gwamnatin ya biyo bayan samun masu zuba jari a fannin na makamashi, bayan rattaba hannu kan yarjejeniya da kamfanoni biyu da suka shahara a fannin, wato Tricell Solar Solutions da IRS Green Energy..
’Yan sanda sun kama gungun masu fashi a kan hanyar Katsina zuwa Kano Ka da a ɗora wa Tinubu laifin rikicin da ke faruwa a PDP — FayoseAn kulla yarjejeniyar ne tare da haɗin gwiwar Hukumar Wutar Lantarki ta Karkara (REA) domin bayar da shawarwari na fasaha da daidaita ayyuka, a yayin taron Sabunta Makamashi na Najeria (NERIF) na 2025 da aka gudanar a ranar Talata a birnin Abuja, kamar yadda mai magana da yawun Gwamnan jihar, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya bayyana.
Ya ce shugaban hukumar Zuba Jari ta jihar (Kan-Invest), Naziru Halliru ne ya jagoranci ƙulla yarjejeniyar a madadin Gwamna Abba Kabir Yusuf.
Sansusi ya ce ƙulla yarjejeniyar na cikin manyan matakai da gwamnatin ke ɗauka domin faɗaɗa samar da makamashi mai tsafta da araha, bunƙasa masana’antu a cikin gida, da samar da ayyukan yi ga al’ummar jihar.
Sanarwar ta kuma ce a karkashin wannan tsarin, kamfanin IRS Green Energy zai gina masana’antar kera kayan amfani da hasken rana da ke da ƙarfin samar da 600MW a shekara, yayin da Tricell Solar Solutions zai kafa wata da ke da ƙarfin 500MW, lamarin da ya ce zai mayar da Kano cibiyar samar da sabon makamashi a yankin.