Aminiya:
2025-12-07@10:19:14 GMT

Gwamnan Gombe ya ƙaddamar da shirin tallafa wa karatun yara mata

Published: 17th, October 2025 GMT

Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya ƙaddamar da shirin AGILE na tallafin karatun yara mata da tallafin gyaran makarantu, domin inganta ilimi a faɗin jihar.

A wajen bikin da aka gudanar a Otal ɗin Custodian, Gwamna Inuwa, wanda Mataimakinsa Dakta Manasseh Jatau, ya wakilta, ya ce gwamnati na da niyyar kawar da duk wani abin da ke hana yara mata zuwa makaranta.

’Yan sanda sun ƙwato miyagun ƙwayoyi a Gombe Ba mu ji dadin yi wa mahaifinmu afuwa tare da riƙaƙƙun masu laifi ba – Iyalan Herbert Macaulay

Ya ƙara da cewa: “Idan ka ilmantar da ’ya mace, ka ilmantar da al’umma gaba ɗaya; idan ka karfafe ta, ka karfafu zuri’a baki ɗaya.”

Gwamnan, ya gode wa Bankin Duniya, Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, da Kwamitin AGILE saboda haɗin kansu wajen inganta ilimi a jihar.

Ya kuma tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da aiki tare da su domin ɗorewar shirin.

Kwamishiniyar Ilimi ta Jihar Gombe, Dokta Aishatu Umar Maigari, ta ce wannan shiri babban ci gaba ne wajen inganta makarantu da bunƙasa tsarin kula da su ta hannun SBMCs.

Ta buƙaci masu ruwa da tsaki su tabbatar da cewa an yi amfani da kuɗaɗen tallafin yadda ya kamata.

A nata ɓangaren, Kodinetar Shirin AGILE, Dokta Amina Haruna Abdul, ta ce dubban yara mata za su amfana da tallafin domin rage matsin tattalin arziƙi da ke hana su karatu.

Ta kuma yaba da jajircewar gwamnatin jihar, wajen tallafa wa ilimi, inda ta ce hakan zai ƙara wa yara mata ƙwarin gwiwa su ci gaba da neman ilimi a faɗin jihar.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: gwamnati Yara mata

এছাড়াও পড়ুন:

Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Jigawa ta Kare Kasafin Kudin 2026 a Gaban Majalisa

Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Jigawa ta ce za ta gudanar da aikin shigar da sabbin dokokin jihar cikin kundin bayanan dokoki da aka yi a jihar.

Babban Sakataren ma’aikatar, Barrister Lawan D. Baba, ya bayyana haka lokacin da ya ke kare kiyasin kasafin kudin sabuwar shekara ta 2026 a gaban kwamatin harkokin shari’a na majalisar dokokin jihar Jigawa.

Barrister Lawan D. Baba ya bayyana cewa ma’aikatar ta yi kiyasin kashe naira milyan 311 da dubu 847 a kasafin kudin sabuwar shekara.

Babban sakataren yace za su mayar da hankali ga batun kawar da jinkiri wajen gudanar da shari’o’i domin karfafa matakan samun shari’a cikin sauri ga al’ummar jihar.

A nasa jawabin, Shugaban kwamatin harkokin shari’a na majalisar dokokin jihar Jigawa kuma wakilin mazabar Hadejia, Barrister Abubakar Sadiq Jallo, ya jaddada bukatar wanzuwar dangantakar aiki tsakanin kwamatin da bangaren shari’a domin inganta aikin shari’a a kotu.

Kazalika, magatakardar Babbar kotun jihar da sakataren hukumar kula da ma’aikatan shari’a da kuma sakataren hukumar bada tallafin shari’a su ma sun kare na su kiyasin kasafin kudaden a gaban kwamatin.

 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Nakiya ta hallaka yara 4 a Borno
  • Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Jigawa ta Kare Kasafin Kudin 2026 a Gaban Majalisa
  • Mata ‘yar wasan harbi ta Iran ta isa wasan karshe na gasar cin kofin duniya a karo na 4
  • Limamin Tehran:  Idan Abokan Gaba Su Ka  Sake Yin Kuskure Akan Iran Za Su Sake Cin Kasa
  • Ina nan a PDP duk da sauya sheƙar ’yan majalisar Ribas — Wike
  • Na kashe N100bn a kan harkar tsaro a 2025 — Zulum
  • Gwamnatin Gombe da UNICEF sun tallafa wa yara masu fama ƙarancin abinci mai gina jiki
  • DSS ta kama likitan da ke duba ’yan bindiga a dazukan Kwara
  • Ziyarar Putin a Indiya alama ce da ke nuna cewa New Delhi na yin watsi da gargadin Trump?
  • NAPTIP ta daƙile yunƙurin safarar mutum 7 daga Kano zuwa Saudiyya