HausaTv:
2025-11-02@13:48:23 GMT

Jagora: Wajibi Ne Kasashen Musulmi Su Yanke Alakarsu Da Gwamnatin ‘Yan Sahayoniyya

Published: 8th, September 2025 GMT

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya jaddada yin kira ga al’ummar Musulmi cewa: Wajibi ne kasashen musulmi su yanke alakarsu da ‘yan sahayoniyya

Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya jaddada cewa: Dole ne kasashen musulmi su yanke duk wata huldar kasuwanci da siyasa da gwamnatin ‘yan sahayoniyya azzaluma tare da mayar da ita saniyar ware.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya jaddada cewa: Dole ne a fuskanci bala’o’in da muguwar gwamnatin ‘yan sahayoniyya ta haifar a Gaza.

Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya yi tsokaci kan mummunan halin da ake ciki a zirin Gaza inda ya ce: Dole ne kasashen da suke gudanar da zanga-zangar a yau musamman kasashen musulmi su yanke duk wata huldar kasuwanci da gwamnatin ‘yan sahayoniyya gaba daya, da ma yanke alakarsu ta siyasa, tare da mayar da ita saniyar ware.

Ya kara da cewa: A yanzu gwamnatin ‘yan sahayoniyya ta zama gwamnati mafi zama saniyar ware da kuma kyama a duniya, amma dole ne a rufe hanyoyin sadarwa da ita. Wannan wani nauyi ne da ya rataya a wuyan dukkanin gwamnatoci. Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya ci gaba da cewa: A ra’ayinsa, daya daga cikin muhimman abubuwan da suka shafi harkokin diflomasiyyar kasashen musulmi shi ne kira ga gwamnatoci da su yanke alakarsu da wannan gwamnati da farko a fagen kasuwanci, sannan a fagen siyasa.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Shugaban Kasar Iran Ya Jaddada Muhimmancin Shawarwarin Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci September 8, 2025 Admiral Sayyari: Dole Ne Jami’an Tsaron Iran Su Kasance Cikin Shirin Ko-Ta  Kwana September 8, 2025 Hamas Tana Maraba Da Duk Wata Shawarar Da Zata Kawo Karshen Ayyukan Ta’addanci Kan Gaza September 8, 2025 Dakarun Yemen Sun Kai Farmaki Kan Muhimman Yankuna Daban-Daban Na ‘Yan Sahayoniyya September 8, 2025 Isra’ila tace Ta Yi Kokarin Kashe Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci A Yakin Kwanaki 12 Da Iran September 7, 2025 Iran Ta Kirayi E3 Su Koma Kan Hanyar diblomasiyya September 7, 2025 Iran: Zahra Kiyani Ta Lashe Lambar Zinari A Gasar Wushu A Karon Farko September 7, 2025 Jiragen Yaki Marasa Matuka Na Yemen Sun Fada Kan Filin Jiragen Sama Na Ramon A Isra’ila September 7, 2025 Wilayati: Yanci da Tsaron Kasar Iraki Na Da Matukar Muhimmanci Ga Iran September 7, 2025 An Gudanar Da Zanga zangar Adawa Da Ziyarar Shugaban Amurka a Malaysia September 7, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: Jagoran juyin juya halin Musulunci kasashen musulmi su yanke yan sahayoniyya

এছাড়াও পড়ুন:

Madagascar Ta Sanar da Kafa Sabuwar Gwamnati Tare da Manyan ‘Yan Adawa

Madagascar ta sanar da kafa sabuwar gwamnati wadda ta kunshi fitattun ‘yan adawa guda uku a manyan mukamai na ministoci.

An gabatar da majalisar ministoci mai mambobi 29, wacce ta kunshi mata 10, a wani biki da aka gudanar a Fadar Gwamnatin Yavoloha da ke babban birnin kasar, Antananarivo.

Shugaban rikon kwarya Michael Randrianireina ya bayyana a lokacin bikin cewa manyan abubuwan da sabuwar gwamnatin ta sa gaba sun hada da yaki da rashin adalci, aiwatar da matakan tsuke bakin aljihu, da kuma samar da yanayin kasuwanci mai dorewa.

Ya kara da cewa kowane minista dole ne ya samar da sakamako mai kyau cikin watanni biyu, yana mai gargadin cewa rashin yin hakan a cikin wannan lokacin zai zama gazawa kuma zai iya haifar da maye gurbin minister a nan take.

An nada Christine Razanahasoa, tsohuwar Ministar Shari’a kuma tsohuwar Kakakin Majalisar Dokoki ta Kasa, a matsayin Ministar Harkokin Waje, kuma an nada Fanerisoua Irinavo, tsohuwar alkali wacce ta dawo daga gudun hijira daga  Faransa, a matsayin Ministar Shari’a.

An nada Hanitra Razavimanantsoa, ​​’yar majalisa daga jam’iyyar Tiaco Madagascar karkashin jagorancin tsohon shugaban kasar Marc Ravalomanana, a matsayin Ministar Kasa a ma’aikatar Sake Gina Kasa. Waɗannan mutane uku suna wakiltar muryoyin  manyan bangarorin ‘yan adawa a Madagascar.

Jagoran juyin mulkin, Michel Randrianireina, ya kwace mulki a ranar 14 ga Oktoba bayan tsohon shugaban kasar Andry Rajoelina ya tsere daga kasar a cikin jirgin saman sojojin Faransa bayan makonni na zanga-zanga.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Iran ta yi fatali da kalamman IAEA Kan Shirin Nukiliyarta October 30, 2025 Trump Ya Umarci Ma’aikatar Yakin Amurka Ta koma gwajin makaman nukiliya October 30, 2025 Isra’ila ta amince da fadada matsugunai a Yammacin Kogin Jordan October 30, 2025 Gaza: hare-haren Isra’ila sun kashe mutane 100 Cikin Kwanaki Biyu October 30, 2025 Sudan : Kasashen duniya na tir da cin zarafi a El-Fasher October 30, 2025 Iran Ta Jaddada Bin Hanyar Diflomasiya Ko Da A Lokacin Yaki Ne Amma Ba Zata Amince Da Bin Umarni Ba October 30, 2025 Qalibaf: Amurka Tana Yaudarar Duniya Da Zaman Lafiya, Alhalin Tana Ci Gaba Da Kai Harin Wuce Gona Da Iri October 30, 2025 Ci Gaba Da Killace Gaza Bayan Tsagaita Bude Wuta Ya Janyo Mutuwar Mutane 1000 A Yankin October 30, 2025 Kungiyar Rapid Support Forces Ta Sanar Da Kafa Kwamitin Bincike Kan Cin Zarafin Al’umma A El Fasher October 30, 2025 An Kafa Dokar Ta Baci A Darul-Salam Saboda Tarzoman Zaben Shugaban Kasa A Tanzania October 30, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • IAEA : Babu wata shaida da ke nuna cewa Iran na kera makaman nukiliya
  • Wasu Yan Ta’adda Sun Kashe Dakarun Sa Kai 2 A Kudu Maso Gabashin Iran
  • Iran Ta Gargadi Isra’ila Kuma Tasha Alwashin Kare Shirinta Na Nukiliya
  • Kamaru: Jagroan ‘Yan Hamayya Ya Yi Kira Da A Tsayar Da Harkoki A Fadin kasar
  • Iran ta damu da halin da ake ciki a yankin El Fasher na Sudan
  • Iran Ta Sanya  Da Ranar 30 Ga Watan Nuwamba A Matsayin Ranar Kasa Ta Tsibirai 3
  • Kasashen Pakistan Da Afghanistan Sun Tsawaita Yarjejeniyar Dakatar Da Bude Wuta
  • Madagascar Ta Sanar da Kafa Sabuwar Gwamnati Tare da Manyan ‘Yan Adawa
  • Iran ta yi fatali da kalamman IAEA Kan Shirin Nukiliyarta
  • Sudan : Kasashen duniya na Allah wadai da cin zarafi a lokacin kama El-Fasher