Pezeshkian : Hare-haren watan Yuni kan Iran cin amanar diflomasiyya ne
Published: 24th, September 2025 GMT
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya yi Allah wadai da hare-haren da Amurka da Isra’ila suka kai a watan Yuni a kan kasar.
A lokacin da yake jawabi a taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 80 ya shaidawa mahalarta taron Majalisar Dinkin Duniya a birnin New York a yau Larabar cewa, hare-haren wani babban rauni ne ga zaman lafiya a yankin.
Shugaban ya ce hare-haren, wadanda suka afkawa garuruwa, gidaje, da ababen more rayuwa na Iran, yayin da ake ci gaba da tattaunawar diflomasiyya, “babban cin amanar diflomasiyya da raunana kokarin da ake yi na samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali ne.”
Pezeshkian ya zargi Washington da Tel Aviv da ruguza tattaunawar da gangan da karfin soji.
Shugaban na Iran ya ce hare-haren sun kashe kwamandoji, mata, yara, masana kimiyya, da kuma masu fada aji na kasa, tare da lalata cibiyoyin da kasashen duniya ke sa ido.
A wani share na jawabinsa shugaban kasar ta Iran ya fadawa wakilan kasashen duniya cewa: “Kisan jami’an gwamnati, kai hare-hare kan ‘yan jarida, da kuma kashe mutane saboda iliminsu da kwarewarsu, babban take hakkin bil’adama ne da dokokin kasa da kasa.”
Ya kuma yi Allah wadai da “kisan kare dangi a Gaza”, barna da keta hurumin kasashen Lebanon, Siriya, Yemen da ake yi, da “yunwar da aka jefa mata da yara, ya kuma sake nanata cewa Iran ba ta neman mallakar makamin nukiliya kamar yadda jagororinta magabata suka bada fatawa.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Jami’an Tsaron Amruka Sun Kai Hari Ofishi Da Gidan John Bolton September 24, 2025 Larijani: Donald Trump Yana A Matsayin Makwafin Adolf Hitler September 24, 2025 Fiye Da Falasdinawa 900,000 Ne Su Ka Yi Hijira A Cikin Gaza September 24, 2025 Imam Khamenei: Hadin kan al’ummar Iran a yakin kwanaki 12 ya sanya makiya kunya September 24, 2025 Larijani: Iran na kare tsaron kasa da azama September 24, 2025 Jagora: Iran Ba Za Ta Taba Yin Watsi Da Inganta Sinadarin Uranium Ba September 24, 2025 Larijani: Iran Tana Nazarin Shawarwarin Turai Da Na Rasha Domin Kare Muradunta September 24, 2025 Araqchi; Iran Da Norway Sun Tattaunawa Batun kyakkyawar Alakar Da Ke Tsakaninsu September 24, 2025 Groosi: Masu Binciken Hukumar Kula Da Makamashin Nukiliya Suna Hanyar Zuwa Iran September 24, 2025 Kasashen Afirka Uku Sun Sanar Da Ficewa Daga Kotun Hukunta Manyan Laifuka Ta Duniya September 24, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Imam Sayyid Ayatollah Khamenei Zai Yi Jawabi Ga mutanen Iran A Cikin Makon Tsaro Da Ya Shigo
Jagoran juyin juya halin musulunci a nan Iran Imam Sayyid Aliyul Khaminae, zai gabatar da jawabi ga mutanen kasar Iran nan gaba kadan, saboda shigowar makin tsaro mai tsarki, inda ake saran zai tabo al-amura da suka shafi tsaron kasar da kuma siyasar kasa da kasa.
Makon tsaro dai shi ne makon da aka fara yakin tsaron kasar mai tsari wanda ya zama masomin yakin tsaron na shekaru 8 tare da gwamnatin Ba’ath ta kasar Iran karkashin shugabancin Saddam Hussain a lokacin An fara yakin ne a ranar daya ga watan Mehr shekara 1359 wato a shekara 1980 har zuwa shekara 1988.
Har’ila yau ana saran zai yi Magana kan sabbin al-amura da suke tasowa a cikin gida.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Lebanon: A yau Ne Aka Yi Jana’izar Shahidan Bitij Bail Wadanda HKI Ta Kai Ga Shahada A Ranar Lahadi September 23, 2025 Pezeshkiyan Ya Ce Tattaunawa Da Kasashe Masu Nuna Karfi Kan Wasu Ba Zai Taba Yi Yuwa Ba September 23, 2025 Sauye-Sauyen Siriya A hannun Amurka Da Aika’ida September 23, 2025 Jakadan Amurka Ya Amince Da Cewa Amurka Tana Nufin Hada Yaki Tsakanin Sojojin Lebanon Da Hizbullah September 23, 2025 ‘Yan Gwagwarmaya Sun Kashe Sojojin Mamaya Biyu A Wani Kwanton Bauna A Arewacin Gaza September 23, 2025 Kasar Afirka Ta Kudu Ta Jaddada Yin Kiran A Bai Wa Falasdinawa Kasarsu September 23, 2025 HKI Tana Ci Gaba Da Yi Wa Mutanen Gaza Kisan Kiyashi September 23, 2025 Nato Na Yin Taron Tattaunawa Keta Hurumin Samaniyar Kasar Estonia Da Rasha Ta Yi September 23, 2025 Dembele Ya Lashe Kyautar Ballon d’Or Ta Shekara Ta 2025. September 23, 2025 Hindi: Amurka Da Kasashen Yamma Ba Sa Son A Dakatar Da Bude Wuta A Gaza. September 23, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci