Ƴansanda Sun Kama Ɗan Jarida A Kano Bisa Zargin Ɓata Suna
Published: 19th, October 2025 GMT
Ƴansandan sun kuma yi kira ga ƴan jarida da su tabbatar da daidaito a rahotanninsu, tare da tuntuɓar sashin hulɗa da jama’a na yankin kafin yaɗa labaran da ke da sarƙakiya. AIG Garba ya gargaɗi ƴan jarida da su guji tsoma baki a cikin binciken da ke gudana, yana mai cewa “a bar doka ta yi aikinta.”
Sai dai sanarwar ba ta fayyace halaccin tsarewar farko da aka yi wa ɗan jaridar ba, ko kuma ko an kama shi ne ba tare da takardar izinin kame ba.
A halin yanzu, ƙungiyoyin kare ƴancin ƴan jarida da ƙungiyoyin farar hula da dama suna ci gaba da kira ga ƴansanda da su saki Ishaq tare da dakatar da duk wani yunƙuri na tsoratar da ƴan jarida daga gudanar da aikinsu cikin ƴanci.
ShareTweetSendShare MASU ALAKAকীওয়ার্ড: ƴan jarida da
এছাড়াও পড়ুন:
Jami’an tsaro sun kama ’yan bindiga 2, sun ƙone sansaninsu a Kogi
Jami’an tsaro a Jihar Kogi, sun kama wasu ’yan bindiga biyu da suka ji rauni tare da likitocin bogi da ke yi musu magani.
Hakazalika, sun lalata sansaninsu a lokacin da suka kai musu farmaki.
Ba mu ji dadin yi wa mahaifinmu afuwa tare da riƙaƙƙun masu laifi ba – Iyalan Herbert Macaulay Akwai yiwuwar matsin lamba ya sa Tinubu cire sunayen wasu da ya yi wa afuwa saboda cece-kuceMai bai wa Gwamnan Jihar Kogi, shawara kan harkar tsaro, Kwamanda Jerry Omodara (mai ritaya), ya bayyana cewa rundunar haɗin gwiwa da ta ƙunshi sojoji, mafarauta da ’yan sa-kai ne suka kai samamen a garin Aherin-Bunu da ke Ƙaramar Hukumar Kabba-Bunu.
A cewar Omodara, jami’an tsaron sun samu bayanan sirri cewa ana yi wa ’yan bindigar da suka ji rauni magani a wani gida.
Ya ce: “Mun samu bayanai cewa wasu ’yan bindiga biyu da suka ji rauni, ana musu magani a wani gida a Aherin-Bunu.
“Nan da nan muka tura jami’an tsaro, suka kama su tare da likitocin bogi da ke yi musu magani.
“Duk wanda aka kama yana taimaka wa ko yana haɗa kai da masu aikata laifi, za a hukunta shi ba tare da la’akari da muƙaminsa ba.”
Omodara, ya ƙara da cewa jami’an tsaron sun lalata sansanin ’yan bindigar, tare da ƙone wani wani waje da suke amfani da shi a matsayin asibiti da kuma gonakinsu.
Ya gargaɗi jama’a da su guji kowace irin alaƙa da masu laifi, inda ta jadadda cewa gwamnati ba za ta ƙyale duk mai tallafa wa miyagu ba a Jihar Kogi.