Aminiya:
2025-09-20@09:21:44 GMT

Takari: Rayuwar baƙin haure ’yan Najeriya mazauna Saudiyya

Published: 20th, September 2025 GMT

Dubban ’yan Nijeriya ne ke zaune a ƙasar Saudiyya ba tare da takardun izinin zama ba, musamman a biranen Makkah da Madina.

Rayuwarsu cike take da fargaba da rashin tabbas, a yayin da suke yin ayyukan hannu ko ƙananan sana’o’i ba tare da wata kariya ta doka ba.

A yayin aiki Hajjin shekarar nan ta 2025, wakilimmu ya samu yin hira da wasu ’yan Nijeriya da ke zaune a can — waɗanda aka fi sani da Takari — inda suka bayyana masa yanayin rayuwarsu sa iliminsu da tsarin matsuguninsu da yanayin aikinsu da rayuwar ’ya’yansu da wasu ƙalubale na fargabar kame da rushe gidajenau, da ma ra’ayinsu kan komawa Nijeriya da sauransu.

Ameera, wata ’yar Najeriya da ke zaune a Saudiyya ba bisa ƙa’ida ba, tana fara aikinta ne daga misalin ƙarfe 6 na yamma har zuwa 6 na safe. Bayan haka za ta koma ƙaramin ɗakin da take raɓe da mijinta da ’ya’yanta uku a saman wani tsauni. A kullum tana dawowa gida da abincin da za su ci kafin su kwanta.

A kowace rana tana tashi daga ƙarfe 7 na yamma zuwa wani layi kusa da Masallacin Harami inda take sayar da kaya ga alhazai — tafiyar kimanin awa ɗaya daga gidanta.

Duk da cewa mutane da dama suna ganin kasuwancinta tamkar na al’ada, ita da makamantanta na yawan fuskantar barazanar kamu da kora daga hukumomin Saudiyya.

Ba ita kaɗai ba ce. Dubban ’yan Najeriya na rayuwa a Makkah da Madina cikin irin wannan hali saboda rashin takardun zama — rayuwa cike da fargaba da rashin tabbas.

Rashin Takardu: Cikas ga ilimi da rayuwa

’Yan Najeriya da ke Saudiyya ba tare da izini ba ba sa iya shiga harkokin kasuwanci da walwala, kuma ba sa iya tura ’ya’yansu makaranta.

“Idan ba ka da takardu ba, ba za ka iya tura ɗanka makaranta ba. Yara suna girma ba tare da samun ilimi ba. Sai iyayen da suke da izinin aiki kaɗai ke iya tura ’ya’yansu makaranta, kuma ba su kai kashi 10 cikin 100 ba daga cikin ’yan Najeriya da ke Saudiyya,” in ji Ameera.

Ta ƙara da cewa ana buƙatar fiye da kimanin Naira miliyan 20 don samun izinin aiki a Saudiyya, kuma ko an samu, yara ba sa wuce makarantar sakandare. Lamarin da ke hana su samun ayyukan ofis masu daraja.

Huraira, maƙwabciyar Ameera, ta ce, “Yaranmu ba sa samun ilimi. Sai wasan ƙwallo a gida. Ba su da makoma face neman ayyukan da ba su da daraja.”

A wasu wurare iyaye sun kafa makarantar cikin gida mai karɓar kuɗin koyarwa, amma tsoron kora daga hukumomi ya hana malamai ci gaba da zuwa.

Adamu, wani ɗan Najeriya da ke zaune a Makkah, ya ce an rusa gidajen da ’yan Najeriya suka gina tun suna matasa.

“Ina biyan haya Riyal 200 kafin a rusa gidan. Yanzu kuwa ina biyan Riyal 1,000 (N420,000) da kuma Riyal 200 na wuta da ruwa,” in ji shi.

Yaran da ke irin waɗannan gidaje ba sa yawan fita saboda tsoron kama iyayensu. Har ma suna jin tsoro idan suka ga baƙuwar fuska.

Rayuwa cikin duhu da tsoro

Hassana da mijinta Abdul suna gudanar da kasuwanci a cikin wani ƙaramin ɗaki da ba zai iya ɗaukar katifa ba. Abdul na fita yana gayyatar mahajjata su sayi kaya, Hassana kuma na kula da tsafta da tsaron gidan.

“Mun fi shekara goma da fara zama a nan, kuma wannan kasuwancin ne ke tallafa mana har muke tura kuɗi gida Nijeriya. Amma ’ya’yanmu ba sa zuwa makaranta. Shi ya sa muke shirin komawa gida kawai,” in ji Abdul.

Magidancin, wanda ya shaida wa wakilinmu cewa an haife shi ne a Makkah shekaru 39 da suka gabata, amma bai taɓa zuwa makaranta ba, ya ƙara da cewa, “Ba na son ’ya’yana su yi irin wannan rayuwar. Mun zama ma’aikata marasa daraja duk da cewa a nan aka haife mu amma ba mu da takardun zama.”

Yawancin samari a yankin suna yin ƙwallon ƙafa dare da rana. Wani yaro mai shekara 14 ya ce, “Ina son zama ƙwararren ɗan ƙwallon ƙafa. Muna fita tun bayan sallar Asuba don atisaye.”

Ya ƙara da cewa an rusa makarantar unguwarsu da suke karatu a ciki, kuma ba su samu wani gurbi da zai maye gurbinta ba.

‘Saudiyya na amfani da ’yan Afirka’

Yusuf Lawan, wani mai aikin hannu, ya ce Saudiyya na ƙara ƙoƙarin korar baƙi. “Muna ta sauya gidaje saboda kada a gano mu, amma suna da ingantaccen tsarin leƙen asiri da ka iya gano mutum.”

Sai dai ya ce: “Su ne ke amfana da mu saboda ba su da wanda zai yi musu aikin hannu. Duk da haka ba sa biyan albashi mai kyau.”

‘Muna son komawa gida’

Ummu Suleym, wata mata da ta bar mijinta da yara a Nijeriya, ta ce, “Kullum cikin fargaba nake. Idan ba mu fito aiki ba, ba mu da abinci balle mu biya haya. Da zarar na tara kuɗi zan koma Nijeriya.”

Ta ƙara da cewa ƙaruruwan mata daga Najeriya na aiki a matsayin ’yan aikin gida a Saudiyya, kuma da yawa daga cikinsu na fuskantar mawuyacin hali.

Sifiyanu Abubakar ya ce ya shafe shekara 35 a Saudiyya tun yana ɗan shekara 21.

“Yanzu ina da shekaru 56 amma har yanzu ’ya’yana ba sa zuwa makaranta. Ina roƙon gwamnatin Nijeriya ta buɗe mana makarantu a nan ko ta tattauna da Saudiyya a ba mu dama.”

Yawancin waɗannan iyalan suna dogaro da aikin gini, ɗiban ƙarafa da wasu sana’o’in hannu da ba su da tabbatacciyar makoma.

Aisha, wata uwa, ta ce, “’Ya’yana biyu da aka haifa a Saudiyya ba su da ’yancin zama ’yan ƙasa.”

Muhammad Nasiru, jami’i a Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Nijeriya (NAHCON), ya ce, “Saudiyya na da manufofi masu kyau da suka amfanar da ’yan Afirka da ma duniya baki daya. Dubban mutane sun amfana da guraben karatu da tallafi daga Saudiyya.”

Ya ƙara da cewa akwai ’yan Najeriya da suka shiga rundunar soja da ’yan sanda a Saudiyya.

Matsalar ’yan Takari da alhazai

Rahotanni sun bayyana cewa ’yan Takari na taimakawa mahajjata wajen sayen kaya a unguwanni da tituna.

Sai dai wani mahajjaci daga Jihar Katsina, Imrana Hamisu, ya ce da yawa daga cikinsu suna damfarar mahajjata.

NAHCON ta ce tana wayar da kan mahajjata kada su yarda da kowa da kuɗinsu, musamman masu musayar kuɗi da masu sanya haƙoran zinariya.

A wani yunƙuri na rage masu shiga aikin Hajji ba bisa ƙa’ida ba, hukumomin Saudiyya sun bullo da tsarin katin NUSUK don tantance masu sahihin izini.

“Ko kafin mu bar Makkah zuwa Mina, ’yan Takari sun mamaye tantunan mahajjata na gaskiya da suka biya kuɗin su,” inji wani jami’in NAHCON.

Wannan ya nuna yadda sauye-sauye a Hajjin 2025 suka kawo ci-gaba wajen magance matsalolin da aka fuskanta a baya.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Najeriya Nijeriya Saudiyya Takari Najeriya da ke ƙara da cewa yan Najeriya Saudiyya ba

এছাড়াও পড়ুন:

An yanke wa Soja hukuncin kisa ta hanyar rataya

Wata babbar kotun sojin Najeriya da ke zamanta a sansanin sojoji ta Maxwell Khobe da ke garin Jos a Jihar Filato ta yanke wa wani soja mai suna Lukman Musa hukuncin kisa ta hanyar rataya.

An yanke wa Musa hukuncin kisa ne a ranar Alhamis bayan da aka same shi da laifuka biyu kan kisan gilla da aka yi wa wani direban babur mai ƙafa uku mai suna Abdulrahman Isa a garin Azare na Jihar Bauchi.

Wani ya sace munduwar Fir’auna a gidan tarihin Masar ’Yan sanda sun kama mutum 9 kan yin garkuwa da kansu

Daily Trust ta ruwaito cewa, an fara shari’ar Musa ne a farkon watan Agustan 2025 bayan kama shi biyo bayan binciken haɗin gwiwa da jami’an sojoji sashin harkokin da hukumomin yankin suka gudanar.

Al’amarin ya ja hankalin jama’a sosai saboda tsananin mugun halin da aka aikata da kuma yunkurin tauye amanar jama’a da sojan ya yi.

Shugaban Kotun Sojojin Najeriya ta 3, Birgediya-Janar, Liafis Bello ya ce an samu sojan da laifin kisan kai da kuma mallakar harsasai ba bisa ƙa’ida ba.

Kotun ta tabbatar da cewa, shaidun da aka gabatar a lokacin shari’ar sun nuna cewa, Musa ya haɗa baki da wani mai suna Mista Oba, domin su kai Isa gidansa da zargin taimaka masa wajen kwashe kayansa.

Ya ƙara da cewa Musa ya bugi Isa a kai da wani abu na katako, inda ya sume, kafin ya shaƙe shi ya mutu.

A ƙoƙarinsu na ɓoye laifin, Musa da abokinsa sun cusa gawar wanda aka kashe a cikin buhu tare da jefa ta a tsakanin ƙauyukan Shira da Yala a Jihar Bauchi.

“An sayar da babur mai ƙafa uku na Isa daga baya, wanda ya ƙara fallasa yadda aka tsara yadda lamarin ya faru,” in ji masu gabatar da ƙara na soji yayin shari’ar.

Hakazalika sun bayyana cewa a binciken da ake yi, an samu Musa da harsashi na musamman har guda 34 na nau’in 7.62mm ba tare da wata izinin doka ba.

Da yake yanke hukuncin, Birgediya Janar Bello ya bayyana abin da Musa ya yi a matsayin “abin kunya, rashin tausayi da kuma cin zarafi da rahin a ɗa’a da kimar sojoji.”

“Ka nuna rashin tausayi daga mai kare ’yan ƙasa zuwa mai kisan gilla, matakin da kuka ɗauka abin kunya ne kuma abin kunya ga Sojojin Najeriya,” in ji kotun.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Dokar Hana Ƙara Kuɗin Makaranta A Kaduna: Alheri Ce Ko Barazana Ga Makarantu Masu Zaman Kansu?
  • Sin Ta Fitar Da Takardar Bayani Game Da Bunkasa Ci Gaban Mata
  • Matasan Nijeriya sun koma yin ci-rani a Nijar da Chadi
  • Mutum 1,666 ne suka kashe kansu a Legas cikin shekaru biyar – ’Yan sanda
  • Akasarin masu kai mana hare-hare daga jihohin da suka kewaye mu suke – Gwamnatin Filato
  • Kotun Sojin Nijeriya Ta Yanke Hukuncin Kisa Kan Wani Soja Da Ya Kashe Ɗan Adaidaita
  • An yanke wa Soja hukuncin kisa ta hanyar rataya
  • Pezeshkian: Iran da Masar suna da tsohon tarihi a duniya
  • Saudiyya ta saki ’yan Najeriya 3 da ta kama kan zargin safarar miyagun ƙwayoyi