An kama sojoji 20 kan yunƙurin kifar da gwamnatin Tinubu
Published: 19th, October 2025 GMT
Bayanai daga rundunar sojin Najeriya na cewa an kafa wani kwamiti da ke binciken wasu jami’ai 20 da aka tsare bisa zargin yunƙurin kifar da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Jaridar Premium Times ta ruwaito wata majiyar soji da ke da masaniya kan lamarin tana cewa al’amarin ya faru ne a ƙarshen watan Satumba.
Majiyar ta ce ana zargin jami’an da shirya zubar da jini a juyin mulkin, kasancewar akwai sunayen wasu manyan jami’an gwamnati da aka shirya yi wa kisan gilla.
A cewar majiyar kamar yadda Premium Times ta ruwaito, daga cikin manyan jami’an gwamnatin waɗanda masu kitsa juyin mulkin suka shirya yi wa kisan gilla akwai shugaba Bola Tinubu da matamaikinsa, Kashim Shettima da kuma shugabannin Majalisun Tarayya, Sanata Godswill Akpabio da Abbas Tajudeen da sauransu.
Waɗanda ake zargin dai, bayanai sun tabbatar da cewa sun tsayar da ranar da za su kifar da gwamnatin farar hula, yayin da suke tuntuɓar juna a kai a kai.
Wannan yunƙuri na juyin mulkin ya haifar da firgici a tsakanin manyan jami’an gwamnati bayan da aka fallasa shi, duk da cewa babban hafsan sojin ƙasar ya sha ba wa gwamnatin Najeriyar tabbacin goyon bayan sojoji ga gwamnati.
An kuma ruwaito cewa saboda kaɗuwar wannan labari ne, gwamnati ta soke faretin cikar Nijeriya shekaru 65 da samun ’yancin kai na ranar 1 ga Oktoba, kasancewar bikin sojoji ne ke jan ragamarsa.
Majiyar ta ƙara da cewa, rundunar ta kafa wani kwamitin bincike da zai bibiyi abin da hukumomi suka bayyana a matsayin rashin ɗa’a da kuma saba ƙa’idojin aiki.
Wata majiya ta ce kwamitin ya shafe makon da ya gabata yana zaman bibiyar al’amarin, amma har yanzu ba a san inda aka kwana ba.
Duk da cewa hedikwatar tsaron ba ta tabbatar da yunƙurin juyin mulkin kai tsaye ba, amma kakakinta, Birgediya Janar Tukur Gusau, a ranar 4 ga watan Oktoba, ya ce ana binciken wasu sojoji 16 kan rashin ɗa’a da kuma saɓa ƙa’idojin aiki.
Sai dai sanarwar da Birgediya Janar Gusau ya fitar a ranar Asabar, ta ce raɗe-raɗin juyin mulki da ake ta yamaɗiɗi ba gaskiya ba ne.
“Rundunar sojin Najeriya na tabbatar da cewa rahoton na ƙarya ne baki ɗayansa,” a cewarsa.
“An dakatar da faretin Ranar ’Yanci ne saboda a bai wa shugaban ƙasa damar halartar wani taro a wajen Najeriya, da kuma mayar da hankali wajen yaƙi da ta’addanci da ’yan fashin daji.
“Binciken da ake yi wa jami’ai 16 kuma na yau da kullum ne da aka saba domin tabbatar da ɗa’a da ƙwarewar aiki. An kafa kwamatin bincike kuma za a sanar da sakamakon bincikensa.”
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Rundunar Sojin Nijeriya tabbatar da
এছাড়াও পড়ুন:
Rikicin Kungiyoyin Asiri Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Wani Matashi A Jihar Kwara
Daga Ali Muhammad Rabi’u
An samu mummunan rikici tsakanin mambobin ƙungiyoyin asiri wanda ya shafi tsofaffin daliban kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kwara da ke Ilorin, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutum ɗaya.
Rediyon Najeriya ya ruwaito cewa dalibin mai suna Oyelade Olawale wanda ya karanci aikin Injiniya a fannin Gine-gine, ya rasu ne a yayin wannan rikici na kungiyoyin asiri.
An samu labarin cewa an kama wasu daga cikin wadanda ake zargi da hannu a tarzomar da ta faru a Kwalejin.
A cikin wata sanarwa, Jami’ar Hulɗa da Jama’a ta Kwalejin, Halima Garba, ta tabbatar da mutuwar matashin da kuma kama wasu mutane da ake zargi da hannu a rikicin.
Sanarwar ta yi kira ga dalibai da al’umma su rika kai rahoton duk wani abin da suke zargin zai iya haddasa fitina ga hukumomin da suka dace domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a makarantar.