Aminiya:
2025-11-27@21:17:19 GMT

Babu wata jam’iyya dana ke shirin shiga — Kwankwaso

Published: 26th, September 2025 GMT

Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya ƙaryata rahotannin da ke cewa ya aike wasiƙar neman shiga wata jam’iyya ta daban.

A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Kwankwaso ya ce babu gaskiya a labaran, kuma ya shawarci jama’a da su yi watsi da su.

’Yan bindiga sun kashe mutum 5 a Masallaci a Zamfara Ganduje ya gindaya wa Kwankwaso sharadin shiga APC

“Mun samu bayanin wasu rubuce-rubucen da ke yawo a Intanet cewa mun miƙa wasiƙar neman shiga wata jam’iyya a ƙasar nan.

“Muna so mu fayyace wa jama’a cewa ba mu taɓa miƙa irin wannan wasiƙa ga kowace jam’iyya ba.

“Saboda haka mun shawarci jama’a da su riƙa neman duk wani bayani game da mu daga shafukanmu na gaskiya,” in ji shi.

Wannan na zuwa ne daidai lokacin da ake ta hasashen komawar Kwankwaso jam’iyyaar APC kafin zaɓen 2027.

Aminiya ta ruwaito cewa akwai alamun cewa Kwankwaso ya tattauna da Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, kan yiwuwar komawa jam’iyyar mai mulki.

Majiyoyi daga APC a Jihar Kano, sun yi iƙirarin cewa Kwankwaso ya aike wa sakatariyar jam’iyyar a Abuja wasiƙa, inda ya bayyana ƙudirinsa na sake shiga jam’iyyar.

Amma Aminiya ba ta tabbatar da wannan batu ba har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.

Sai dai wata majiya daga sakatariyar APC a Abuja, ta ce Kwankwaso da shugaban jam’iyyar na ƙasa sun daɗe suna tattaunawa kan shirin sauya sheƙarsa, kuma shirye-shiryen sun yi nisa.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Kwankwaso labaran ƙarya martani raɗi Sauya Sheƙa

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamnati Za Ta Biya Wasu Kudaden Ariyas Ga Masu Fensho Wannan Wata

 

An sake tabbatar wa ma’aikatan Gwamnatin Tarayya FG da suka yi ritaya cewa za a biya su wani bangare na kudaden ariyas a cikin wannan watan, kamar yadda hukumomin da abin ya shafa suka yi alkawari.

Mataimakin Sakataren ƙungiyar masu karɓar fansho ta ƙasa, Alhaji Ahmed Gazali, ya bayar da wannan tabbaci yayin da ake tattaunawa da shi ta wayar tarho daga Abuja.

Alh. Ahmed Gazali, ya yi bayanin cewas daraktan dake kula da kudade na ofishin akanta janar na tarayya ya tabbatar da daukan matakin hakan na biyan kudaden.

Ya bayyana fatan ganin kudirin FG na gaggauta biyan kudade, domin dakatar da duk wata zanga zanga wanda hakan bai dace ba ga ma’aikatan da suka yi ritaya domin bata martaban kasan nan.

Hakan kuma masu karban fensho a Radion Tarayya na kasa FRCN da Gidan talabijin na kasa NTA dake Kaduna sun nuna damuwarsu game da zargin da ake yi cewa ana kokarin wulakanta shugabannin kungiyar ma’aikatan da suka yi ritaya karkashin jagorancin kwamaret Munkaila Ogunbote.

DAGA SULEIMAN KAURA 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Wata mata ta kashe ’yar shekara 7 a Ribas
  • El-Rufai ya koma jami’yyar haɗaka ta ADC
  • An janye ’yan sanda 11,566 daga gadin manyan mutane a faɗin Nijeriya
  • Gwamnati Za Ta Biya Wasu Kudaden Ariyas Ga Masu Fensho Wannan Wata
  • Karamar Hukumar Birnin Kudu Ta Kashe Sama da Naira Miliyan 5 Don Tallafawa Shirin AGILE
  • Ma’aikatar Harkokin Wajen Falasdinu Ta Sanar Cewa Akalla Yan Mata 33000 Ne Isra’ila Ta Kashe A Gaza
  • Kotu ta yanke wa mutum 5 hukuncin rataya a Oyo saboda aikata kisan kai
  • UNIFIL: Isra’ila tana sabawa wa kudurorin MDD a cikin  Lebanon
  • An haramta cin naman Kare da Kyanwa a Indonesia
  • Gwamna Namadi Ya Kaddamar da Titi Mai Tsawon Kilomita 13 a ‘Yankwashi