Talauci ne babban maƙiyin ɗan Adam — Atiku
Published: 19th, October 2025 GMT
Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya bayyana talauci a matsayin babban abokin gabar ɗan Adam.
Ya ce ƙaruwar talauci a Najeriya na ci gaba da jawo rashin lafiya, jahilci, rashin tsaro, da rashin fata a tsakanin jama’a.
’Yan sanda sun tsare ɗan jarida kan zargin ɓata sunan hadimin gwamnan Kano Mahukunta sun kai samame wani gidan shan Shisha a KanoA wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook domin bikin Ranar Yaƙi da Talauci ta Duniya, Atiku, ya ce wannan rana tana tunatar da gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki muhimmancin ƙara ƙoƙari wajen yaƙar talauci
“Talauci ne babban abokin gabar ɗan Adam.
Ya bayyana cewa matsayin Najeriya a jerin ƙasashen da talauci ya fi ƙamari na nuna buƙatar ɗaukar matakan da za su mayar da hankali kan inganta rayuwar jama’a.
“Abin takaici ne samun kanmu cikin ƙasashen da talauci ya yi ƙatutu. Saboda haka ne nake ci gaba da fafutukar ganin an ɗauki matakau waɗanda za su taimaka wajen kawo ƙarshen talauci,” in ji shi.
Atiku, ya kuma roƙi Gwamnatin Tarayya da ta jihohi, ƙungiyoyi da shugabannin al’umma da su haɗa kai wajen yaƙar talauci daga tushe, ta yadda kowa zai taka rawa.
“A matakin gwamnati da kuma al’umma, dole ne yaƙin kawar da talauci ta isa kowane gida, unguwa da makaranta, domin a samar wa talakawa mafita,” in ji shi.
A baya-bayan nan, Atiku yana kira da kawo sauye-sauyen tattalin arziƙi da suka haɗa da samar da ayyukan yi, raba albarkatun ƙasa cikin adalci, da inganta ilimi da lafiya.
Atiku na ganin matakan su ne ginshiƙan da za su taimaka wajen kawo ƙarshen talauci a Najeriya.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Kira Najeriya Ranar Yaƙi D Talauci ta Duniya
এছাড়াও পড়ুন:
Masu Bincike Na Sin Sun Kera Wani Dan Karamin Mutum Mutumin Hannu Da Zai Taimaka Wajen Gwaje-wajen Kimiyya
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Xi Jinping Ya Yi Kira Da a Kara Horar Da Kwararrun Masana A Fannin Aikin Gona October 16, 2025
Daga Birnin Sin Shugabannin Kasashe Da Dama Sun Yaba Wa Sin Kan Gudummawar Da Ta Bayar A Fannin Tabbatar Da Daidaiton Jinsi October 16, 2025
Daga Birnin Sin Ɗaga Matsayin Dangantakar Zambia Da Sin Ya Haifar Da Manyan Nasarori October 16, 2025