A yayin da Najeriya ke karkata zuwa amfani da kayan tsaro na zamani na cikin gida domin ƙarfafa gwiwar jami’an tsaronta a fagen fama, wani ɗan Jihar Katsina ya fara ƙera motar yaƙi nau’in Track Armored Personnel Carrier (TAPC).
Jihar Katsina na daga cikin jihohin Arewa da suka fi fama da hare-haren ’yan bindiga, inda suka kashe dubban mutane tare da raba wasu da muhallansu gami da rusa harkokin tattalin arziki da na zamantakewa.
Ana cikin haka ne wani ɗan asalin yankin Kaita a jihar mai suna Injiniya Ibrahim Lawal Ɗankaba, ya fara yunƙurin ƙera motar yaƙi, wadda ya sanya wa suna Beguwa, a ƙoƙarinsa na tallafa wa yunƙurin gwamnati na daƙile ayyukan ’yan ta’addanci da suka daɗe suna ci wa al’umma jihar da maƙwabtansu tuwo a ƙwarya.
Ɗankaba ya shaida wa wakilimu cewa ya fara wannan yunƙuri ne tun fa arkon watan Satumba da ya gabata, inda yake amfani da fallayen tama da aka ƙera a cikin gida wajen ƙera sassan kariyar sulke na motar tsaron.
Ma’aurata 136 sun kashe juna a shekara 4 Ta’addanci: An fi kashe Musulmi a kan Kiristoci a Najeriya — Jakadan AmurkaYa ce, sassan na ƙarafa da aka ƙera a cikin gida, an tsara su da kyau ne, inda ake ta ɗora su a jikin motar sulken, wadda take da cikakkiyar sulke daga harsasai, kuma tana da na’urar sarrafa bindiga daga nesa da kuma lura da motsin abokan gaba.
Motar tana kluma ɗauke da kujeru domin ɗaukar mutane bakwai da a’urori na musamman kamar na’urar bindiga mai sarafa kanta da tsarin gano abubuwa (DPS) da kuma bel na ɗaukar kaya. Tana kuma ba wa jami’an tsaro kariya da kuma damar motsi cikin sauƙi a wurare masu haɗari.
Na’urar bindigarta an tsara ta ne domin bai wa jami’an cikin motar damar harbi ba tare da fuskantar barazanar abokan gaba ba. Haka kuma tana ba su damar tattara bayanan sirri da lura da motsin abokan gaba daga nesa, wanda ke taimakawa wajen yanke shawara ga manyan hafsoshi.
Ya ce, idan hukumomin da suka dace suka sahale amfani da Beguwa, za ta bawa wa jami’an tsaro kariya daga harbin bindiga da ababen fashewa ta yadda za a rage asarar rayuka da kuma ƙara ingancin aiki.
Motar tana amfani ne da taya irin na tankin yaƙi, wanda ke ba ta damar motsi cikin sauƙi a wurare masu wuyar sha’ani kamar dazuka, duwatsu da tabkuna. Haka kuma tana da tsarin da ke ba ta damar shiga kowane irin yanayi cikin sauƙi.
A yayin da injinta ke amfani da man fetur da gas (CNG) da dizel, wanda ke ba jami’an tsaro damar gudanar da aiki a ko’ina, tana da bisa da ya kai 600mm, wanda ke ba ta damar ƙetare yankunan da ke cike da ƙalubale.
Baya ga fagen yaƙi, motar na da matuƙar amfani wajen ɗaukar kaya saboda bel da ke jikinta. Tana iya ɗaukar kayan agaji, makamai da ma’aikatan lafiya zuwa wuraren da ake fama da rikici, wanda ke da matuƙar amfani wajen gudanar da aiki da kuma rage haɗarin kai kayan agaji.
Gwaji da kyakkyawan fataKo da yake wannan shi ne irinsa na farko a Jihar Katsina, Darakta kuma Shugaban Kamfanin Techno-Em Global Solutions Limited, Injiniya Ibrahim Lawal Dankaba, na fatan wannan fasaha ta cikin gida za ta yi abin da dakarun ƙasa suka daɗe suna ƙoƙarin cimmawa.
Dankaba ya ce suna gudanar da gwaje-gwaje a cikin gida domin tabbatar da cewa motar ta cika ƙa’idojin tsaro da na ƙera motoci. Ya ce motar na da ƙarfi da kariya daga harbi da abubuwan fashewa.
Yadda tunanin ya faroGame da dalilinsa na ƙera motar, Dankaba ya ce: “Ra’ayin ya samo asali ne daga yadda muka ga yadda ake fama da ta’addanci da sauran laifuka, muka yanke shawarar taimaka wa kanmu, al’umma da gwamnati wajen kare rayuka.
“Sojoji da ’yan sanda da mazauna yankuna suna bakin ƙoƙarinsu, amma muka ga cewa mu ma za mu iya bayar da gudunmuwa wajen magance matsalar. Don haka muka yanke shawarar ƙera wannan motar. Wannan mota tana da sauƙin motsi, tana iya shiga kowane irin yanayi; mota ce da ba ta damu da ko ƙasa ko yashi ko laka ba.
“Mun ƙera ta ne domin ta iya shiga kowane irin yanayi da ke yankin Sahel domin taimakawa wajen kare jiharmu da ƙasa baki ɗaya. Tana ɗaukar jami’ai har guda bakwai. Tana da bel na ɗaukar kaya wanda zai iya kai kayan agaji ko tallafi zuwa yankunan da ke da wahalar isa.”
Ya ƙara da cewa duk da cewa kamfaninsu ya yi amfani da fallayen tama wajen ƙera wannan samfurin, “Amma idan gwamnati ta amince da ita, za mu fara amfani da kayan kariya na musamman wajen ƙera sassan kariya da tayoyin ƙarfe.
“Ina tabbatar muku cewa motar ta fi sauƙin kuɗi fiye a kan ta ƙasashen waje, kuma idan gwamnati ta tallafa mana wajen samar da wasu, za mu ƙara samar da ayyukan yi ga matasa da kuma bunƙasa fasahar injiniyanci a gida,” in ji shi.
Da aka tambaye shi ko hukumomi sun amince da motar, Shugaban Kamfanin Techno-Em Global Solutions Limited ya ce: “Muna tuntuɓar Ofishin Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro domin samun izinin amfani da motar domin mu ci gaba da ƙerawa domin yaƙi da rashin tsaro a Katsina da ƙasa baki ɗaya.”
Ɗankaba ya ce kamfaninsu na da niyyar ci gaba da ƙera irin motocin domin shawo kan matsalolin da ke tattare da yanayin ƙasa, kuma a nan gaba “Muna fatan ƙera jiragen leƙen asiri da sauran na’urorin tsaro idan buƙatar hakan ta taso.”
Baya ga yadda aka ƙera jikin motar ta hanyar narka ƙarafa domin samun madaidaicin siffa, an ba da kulawa ta musamman ga sassan cikinta, ciki har da kariya ga injin, lagireto da sauran sassan da ke da alaƙa da lafiyar jami’an da ke cikin motar.
Ɗankaba ya ce sun sadaukar da wannan motar ga iyalan waɗanda suka rasa rayukansu a rikicin da ake fama da shi, yana mai cewa za ta taimaka wa gwamnati ta jiha da ta tarayya wajen kawo ƙarshen ta’addanci da dawo da zaman lafiya wanda shi ne ginshiƙin ci gaba mai ɗorewa.
Tallafa wa irin wannan fasaha na cikin gida zai tabbatar da ikon mallakar fasahar da ake amfani da ita wajen kare rayuka da dukiyoyi da muhimman ginegine da bayanan sirri da kuma hana yaɗuwar matsalolin da za su iya zuwa ɗaga kasashen waje.
Idan aka tallafa wa wannan ƙoƙari yadda ya kamata, zai iya haifar da al’adar ƙirƙire-ƙirƙire da samar da sabbin fasahohi da za su iya amfani a ɓangaren gwamnati da na kasuwanci, wanda hakan zai ƙara ƙarfin tsarin tsaro na jihar da kuma hana asarar kuɗaɗe.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: jami an tsaro ƙera motar
এছাড়াও পড়ুন:
Jihar Jigawa Ta Dukufa Wajen Gina Magudanan Ruwa Domin Kaucewa Ambaliya
An fara gina magudanan ruwa domin dakile afkuwar ambaliyar ruwa a kananan hukumomin Malam Madori da Kaugama dake jihar Jigawa.
Tawagar Injiniyoyin jihar karkashin jagorancin Daraktan kula da ambaliyar ruwa da zaizayar kasa, Injiniya Mukhtar Muhammad Usman sun ziyarci kananan hukumomin domin duba yadda aikin ke gudana.
Haka zalika Daraktan da mataimakin sa Injiniya Mahdi Isyaku da sauran ma’aikata ssn ziyarci wurin da ambaliyar ruwa tayi ta’adi a garin malam Madori.
A lokacin da tawagar ta fara auna fili da tona magudanun ruwan, daraktan ya ce an fara aikin tona magudanar ruwa mai tsawon kilomita 2 a matsayin wani ɓangare na aikin karkatar da ruwan da ya lalata wurare zuwa sabon wurin da aka tsara.
Yana mai cewar, har ila yau, ana gina wani magudanar ruwa mai tsawon mita 300 a unguwar Gandun Sarki, yayin da aka kammala wasu masu tsawon fiye da mita 390 a Kantamari da kuma mai tsawon sama da mita 500 a Zaburan dake karamar hukumar Kaugama.
Wakilin mazabar Mallam Madori a majalisar dokokin jihar, Alhaji Hamza Adamu Babayaro Malam Madori ya halarci bikin kaddamar da aikin magudanar ruwa mai tsawon mita 2,000 a unguwar Kampala don rage illar ambaliya a yankin.
Shi kuwa shugaban al’ummar Kampala, Ibrahim Zakar, yayi alkawarin samar da masauki ga ma’aikatan domin samun saukin gudanar da aiyukan su don kwalliya da biya kudin sabulu.
A jawabin sa Shugaban karamar hukumar Malam Madori, Alhaji Salisu Sani Garun-Gabas, ya yabawa Gwamna Umar Namadi bisa cika alkawarin da ya dauka a lokacin ziyarar da ya kai yankin, na dakile faruwar ambaliyar da ta lalata gidaje da dama a unguwar Kampala.
Salisu Garun Gabas, ya sami wakilcin mataimakiyar sa ,Hajiya Amina Haruna Dokaje, wacce ta jagoranci kaddamar da aikin tonan magudanar ruwa.
Usman Mohammed Zaria