Ɗaliban Fasaha Sun Ɓullo Da Dabarar Tsaro Ta Harkar Noma
Published: 18th, October 2025 GMT
NAPS, w da take wakiltar fiye da daliba miliyan a fadin Nijeriya 28.1 a makarantun fasaha , monotechnics da kuma Kwalejojin fasaha, sun gabatarwa Ministan da takarda inda suka nuna irin ci gaban da aka samu a ma’aikatar tsaron. Wadanda suka hada da yadda suke kokarin yaki da kungiyoyin ta’adda masu , ga kuma yadda suka karawa jami’an tsaro abubuwan jin dadi.
Kungiyar ta ce “Mun aminta da irin ci gaban da aka samu ma’aikatar wadanda kuma za a iya gani wajen yakin ta’addanci na hadin gwiwa har ma ana samun nasarar murkushe duk irn kokarin da su ‘yan ta’adda Oyegan shi ya bayyana hakan lokacin taron da aka yi da shi a hedikwatar ma’aikatar tsaro a Abuja.
Kungiyar ta dalibaiduk da hakan ta nuna rashin jin dadinta kan abubuwan da ake fuskanta kan karuwar rashin tsaro a makarantu,inda suka yi misali da abinda ya faru a makarantar fasaha ta gwamnatin tarayya da ke Bauchi, da sauran wuraren kwanan dalibai inda suka zama yadda ake ta kamawa da garkuwa da su da kuma kai masu hari.
Shugaban kungiyar NAPS ya yi kira da ma’aikatar da kara daura damara wajen harin ko yakin hadin gwiwa da samame da jami’an tsaro ke yi a asirce kusa da makarantu, domin, a tabbatar da lafiyar dalibai da kasancewarsu zama cikin kwanciyar hankali a fadin tarayyar Nijeriya.
“Sun ce a mtsayinsu na masu ruwa da tsaki a ci gaban kasa, dole su tabbatar da wuraren kwnan dalibai suna cikin lafaiya babu wasu abubuwan da za su kawo tashin hankali, domin wuri ne koyon ilimi da dabaru ba wurin da ‘yan ta’adda za suyi amfani da shi ba domin cimma burinsu na cutarwa kamar yadda jaddada,” .
A na shi jawabin Ministan tsaro ya nuna irin kokarin da su Shugabannin ita bkungiyar ta daliban take yi, na hada kai kungiyoyin dalibai da makarantu domin bunkasa lamarin daya shafi inganta lamarin daya shafi tsaro na kasa.
“Irin wannan kokarin da kuke yi da tunani abin a yaba ne, a matsayinku na dalibai. Wannan ma’aikata a shirya take wajn yin amfani da duk irin shawarar da aka bata domin bunkasa lamarin daya shafi ci gaban tsaron kasa cewar Minisata,’’.
ShareTweetSendShare MASU ALAKAএছাড়াও পড়ুন:
Ministan Tsaro Badaru Abubakar Ya Yi Murabus
Daga Bello Wakili
Ministan tsaron Najeriya, Alhaji Mohammed Badaru Abubakar, ya yi murabus daga mukaminsa nan take.
Sanarwar da mai ba Shugaban Ƙasa shawara kan yada labarai Bayo Onanuga ya fitar, ta ce wasikar da Badaru ya aika wa Shugaba Bola Tinubu mai dauke da kwanan watan 1 ga watan Disambar 2025, ta yi bayanin cewa, ya ajiye aikin ne saboda dalilan lafiya.
Sanarwar ta ce Shugaba Tinubu ya amince da murabus ɗin tare da gode wa Badaru Abubakar bisa irin gudummawar da ya bai wa ƙasa.
Ana sa ran Shugaba Tinubu zai sanar da Majalisar Dattawa sunan wanda zai maye gurbin Badaru nan da ƙarshen wannan makon.
Badaru Abubakar, mai shekara 63, ya taɓa zama gwamnan jihar Jigawa har sau biyu daga 2015 zuwa 2023. An kuma naɗa shi minista ne a ranar 21 ga watan Agustan 2023.
Murabus ɗinsa ya zo ne a daidai lokacin da Shugaba Tinubu ya ayyana dokar ta-baci kan harkokin tsaron ƙasa, kuma ana sa ran zai fayyace cikakkun matakan da za a ɗauka a nan gaba.