Kasar Sin Ta Gargadi Amurka Game Da Yunkurin Samarwa Yankin Taiwan Makamai
Published: 18th, October 2025 GMT
Kakakin ya kuma jaddada matukar adawa, da tanade-tanaden dokar, yana mai cewa, batun Taiwan shi ne jan layi na farko da ba za a iya tsallakewa ba a dangantakar Sin da Amurka.
Daga nan sai ya yi kira ga Amurka, da ta mutunta cikakkiyar manufar nan ta kasar Sin daya tak a duniya, da kuma sanarwa uku na hadin gwiwa da Sin da Amurka suka amincewa, ta yadda za ta cika alkawarin da ta dauka na kin goyon bayan duk wani yunkuri na neman ’yancin kan Taiwan, kana Amurka ta kaucewa mika sakwanni na kuskure ga ’yan aware masu rajin neman ’yancin kan yankin na Taiwan, ko shiga duk wata cudanyar ayyukan soji da yankin Taiwan na kasar Sin.
এছাড়াও পড়ুন:
Alkaluman Jin Ra’ayi na CGTN Sun Shaida Amincewar Al’umma Da Karfin Tattalin Arzikin Kasar Sin
Wani binciken tattara ra’ayoyi da aka gudanar a shekarar nan ta 2025, ya nuna kaso 72.6 bisa dari na masu bayyana ra’ayoyin sun gamsu da manufar Sin ta bude kofa, da kasuwarta mai amincewa da kyakkyawar takara. Kana kaso 79.8 bisa dari na ganin babbar kasuwar Sin ta samar da muhimman damammaki ga kasashensu na asali. (Saminu Alhassan)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA