Madagascar : An rantsar da Michael Randrianirina a matsayin shugaban kasar
Published: 18th, October 2025 GMT
A Madagaska jiya Juma’a ne kotun tsarin mulkin kasar ta rantsar da Kanar Michael Randrianirina a matsayin shugaban kasa.
Hakan na zuwa ne bayan majalisar dokokin kasar ta tsige shugaban kasar Andry Rajoelina bayan ya tsere daga kasar sanadiyyar zanga zangar data rikide zuwa bore wa gwamnatinsa saboda matsalar wutar lantarki da ruwan sha.
Tunda farko dai kanar Randrianirina ya kiyasta zai rike mulki na wa’adin watanni 18 zuwa 24 lokacin da za’a kai ga gudanar da zaben raba gardama na kundin tsarin mulkin kasar.
A ranar Talata da ta gabata ne, Randrianirina ya sanar da juyin mulkin kwace Mulki a kasar yana mai danganta hakan da rashin biyayya ga kundin tsarin mulkin kasar, da keta hakkokin bil’adama.
A kuma Talatar ne majalisar wakilan kasar ta jefa kuri’ar tsige shugaba Andry Rajoelina yayin wani zama na musamman, duk da cewa shugaba Rajoelina ya riga ya ayyana rushe majalisar.
A karshen watan Satumban da ya shude ne rikici ya barke a kasar, biyowa bayan tsanantar karancin wutar lantarki da ruwan fanfo.
An kuma samu tashe-tashen hankula yayin zanga-zanga, lamarin da ya rikide zuwa ga kiraye-kirayen shugaban kasar ya yi murabus, lamarin da ya tilata mas yin murabus.
Tuni Tarayyar Afirka (AU) ta dakatar da kasar ta Madagascar daga kungiyar bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a ranar Talata.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Al-Houthi: Matsin lamba bai hana Iran ci gaba da goyon bayan Falasdinu ba October 18, 2025 Marzieh Jafari Ta Dauki Lambar Yabo Ta Horar Da Mata Wasan Kwallon Kafa Ta Nahiyar Asia October 18, 2025 Iran: Kudurin Kwamitin Tsaro Kan Yarjeniyar JCPOA Ya Kawo Karshe A Yau October 18, 2025 Iran: Kauyuka 3 Sun Shiga Cikin Wuraren Bude Ido Na Duniya October 18, 2025 Aref: Kofar Tattaunawa A Bude Take, Amma Ba Zamu Amince Da Bukatun Da Basa Da Ma’an Ba October 18, 2025 Kenya Ta Yiwa Raila Odinga Jana’iza Ta Musamman October 18, 2025 Kwamandan Rundunar Kudancin Amurka ya sanar da murabus kan batun ayyukan soji a yankin Caribbean October 18, 2025 Janar Sulaimani: A Yayin Yakin Kwanaki 12 Iran Ta Tarwatsa Wasu Muhimman Wurare 21 Na Isra’ila October 17, 2025 Abokan Yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya Sun Ce: Sake Dawo Da Takunkumin Da Aka Kakaba Kan Iran Baya Kan Doka October 17, 2025 Iran Ta Yi Allah Wadai Da Wuce Gona Da Irin Isra’ila Kan Kudancin Kasar Lebanon October 17, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Shugaban venuzuwela Ya Gargadi Amurka Game Da Kokarin Da Take yi Na Karbe Ikon Kula Da Rijiyoyin Mai Na Kasar
Nicolas Maduro shugaban kasar Venzuwela yayi tir da barazanar da Washington ke ta nanatawa na yin amfani da karfin soji kan karakas, kuma yayi gargadi game da shirin Amurka na kwace ikon kila da rijiyoyin mai na kasar a hanyar amfani da karfin soji.
Maduro yayi wannan bayanin ne a cikin wata wasika da ya aikewa sakatare janar din hukumar kula da hakon manfetur ta duniya OPEC,
Kasar venuzuwela a hukumance ta bayyanawa hukumar cewa gwamnatin Amurka tana so kwace kula da rijiyoyin manta, mafi girma a duniya, ta hanyar yin amfani da karfin soja akanta da mutane da sauran humumomin kasar,
Haka zalika ya fadi a cikin wasikar cewa zai ci gaba da tsayawa kyam wajen kare arzikin makamashi da kasar ke da shi,kuma ba zai mika wuya ga duk wani bata suna ko barazana ba
Wannan wasika ta zo ne bayan da shugaban Amurka Donald Trump yayi barazana a ranar Asabar cewa za’a rufe dukkan sararin samaniyar kasar venuzuwela.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Zanga zanga Ta Barke A Isra’ila Yayin Da Natanyaho Ke Neman Afuwa Kan Batun Cin Hanci Da Rashawa December 1, 2025 Mataimakin Ministan Harkokin Wajen Kasar Saudiya Ya Gana Da Ministan Harkokin Wajen Kasar Iran. December 1, 2025 Lebanon: Sakon Kungiyar Hizbullah Ga Paparoma December 1, 2025 Ireland Ta Sauya Sunan Wurin Shakatawa Daga Na Shugaban “Isra’ila” Zuwa Na Shahidiyar Falasdinu November 30, 2025 Gaza: Sau 590 “Isra’ila” Ta Keta Tsagaiwa Wutar Yaki November 30, 2025 Washington Post: Shirin Trump Na Kai Sojojin Gaza Yana Fuskantar Matsala November 30, 2025 MDD: Kasar Somaliya Tana Fuskantar Mawuyacin Yanayi Saboda Fari November 30, 2025 An Yi Ganawa A Tsakanin Ministocin Harkokin Wajen Iran Da Turkiya November 30, 2025 An yi gangami a fadin duniya a zagayowar ranar Falasdinu November 30, 2025 Cinikin Kasashen Waje na Iran Ya Zarce Dala Biliyan 76.5 November 30, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci