An Kara Habaka Sabon Karfin Samar Da Kayayyaki Da Hidimomi Mai Dorewa a Cikin Watannin Tara Na Farkon Bana
Published: 17th, October 2025 GMT
Sabbin alkaluman da babbar hukumar kula da haraji ta kasar Sin ta bayar yau 17 ga wata sun nuna cewa, a cikin watannin tara na farkon bana, kamfanoni sun kara zuba jari wajen kirkire-kirkire, kuma sabbin masana’antu bisa manyan tsare-tsare sun ci gaba da habaka. Lamarin da ya shaida cewa, ana samun ci gaba cikin sauri wajen raya sabon karfin samar da kayayyaki da hidimomi mai dorewa ta kasar Sin.
Zhang Bin, darektan kwamitin jam’iyyar kwaminis ta Sin dake cibiyar nazarin dabarun tattalin arziki da hada hadar kudi ta kwalejin kimiyyar zamantakewar al’umma ta kasar Sin,ya bayyana cewa, bisa alkaluman da hukumar harajin ta fitar, ana iya ganin cewa, ana kara habaka sabon karfin samar da kayayyaki da hidimomi mai dorewa a kasar Sin, lamarin da zai taimaka sosai wajen bunkasuwar ci gaban tattalin arziki da zamantakewar al’ummar kasar.(Amina Xu)
ShareTweetSendShare MASU ALAKAকীওয়ার্ড: ta kasar Sin
এছাড়াও পড়ুন:
Matsayar Kasar Sin A Bayyane Take Dangane Da Batutuwan Cinikayya Da Tsagin Amurka
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Sin Ta Kara Wasu Wurare 22 Cikin Yankunan Dausayi Masu Matukar Muhimmanci A Kasar October 20, 2025
Daga Birnin Sin Sin Ta Yi Maraba Da Yarjejeniyar Tsagaita Bude Wuta Tsakanin Pakistan Da Afghanistan October 20, 2025
Daga Birnin Sin Gina Kasar Sin Ta Dijital Na Kara Gaba Zuwa Sabon Matakin Amfani Da Basira October 20, 2025