Dantawaye ya zama sabon kwamishinan ’yan sandan Abuja
Published: 17th, October 2025 GMT
Rundunar ’Yan Sandan Babban Birnin Tarayya, ta sanar da nadin CP Dantawaye Miller a matsayin sabon Kwamishinan ’Yan Sandan Abuja.
Ya karɓi ragamar aikin ne a ranar Juma’a, 17 ga watan Oktoba, 2025, daga hannun CP Ajao Adewale, wanda Babban Sufeton ’Yan Sanda na Ƙasa, Kayode Egbetokun, ya sauya wa wajen aiki.
A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, SP Josephine Adeh, ta fitar, sabon kwamishinan ya bayyana cewa zai ci gaba da inganta tsaro tare da bunkasa haɗin kai tsakanin ’yan sanda da al’ummar Abuja.
Ta ce CP Miller ya yi alkawarin samar da tsari domin tabbatar da kare rayuka da dukiyoyin mazauna Babban Birnin Tarayya.
Rundunar ta kuma roƙi al’umma da su ci gaba da bai wa ’yan sanda hadin kai domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a Abuja.
Adeh, ta bayyana Dantawaye Miller a matsayin gogaggen jami’in tsaro da ya shafe sama da shekaru 20 yana aiki a wurare daban-daban a faɗin ƙasar nan.
An haife shi a ranar 15 ga watan Oktoban 1971, a ƙaramar hukumar Kajuru ta Jihar Kaduna, kuma ɗa ne ga marigayi DCP Gajere Dantawaye.
Ya shiga aikin dan sanda a watan Mayu, 2000, inda ya fara aikinsa a Jihar Bayelsa a shekarar 2002.
A tsawon lokacin da ya shafe yana aiki, Miller ya riƙe muƙamai da dama, ciki har da mukamin babban mai tsaron tsohon gwamnan Bayelsa, kwamandan rakiyar tsohon mataimakin shugaban ƙasa.
Ragowar mukaman sun hada da jami’in tsaro na musamman a Ma’aikatar Man Fetur, da kwamandan MOPOL 24 da ke aiki a Fadar Shugaban Ƙasa.
Haka kuma, ya taɓa zama Mataimakin Kwamishinan ’Yan Sanda a Abuja, kwamandan yanki a Jihar Adamawa, Mataimakin Kwamishina a Jihohin Yobe da Edo, da Kwamishinan ’Yan Sanda mai kula da Fasahar Sadarwa a hedikwatar rundunar.
Kafin yanzu, shi ne Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kogi.
A ’yan watannin nan, an samu ƙarin matsalolin tsaro a Abuja duk da ƙoƙarin da ’yan sanda ke yi na dakile su.
Saboda haka, ana sa ran sabon kwamishinan, CP Dantawaye, zai kawo sabbin dabaru da shugabanci domin inganta tsaro a Babban Birnin Tarayya, Abuja
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Sanda Babban Birnin Tarayya CP Dantawaye sabon Kwamishinan
এছাড়াও পড়ুন:
’Yan sanda sun ƙwato miyagun ƙwayoyi a Gombe
Rundunar ’Yan sandan Jihar Gombe ta ƙara ƙaimi wajen yaƙi da ta’ammali da miyagun ƙwayoyi da sauran laifuka, inda ta gudanar da samame a wata maɓoya da ake zargi da aikata ayyukan ta’addanci da safarar ƙwayoyi a cikin jihar.
A wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, DSP Buhari Abdullahi ya fitar, ta bayyana cewa jami’an da ke ƙarƙashin Gombe Division ne suka gudanar da samamen da misalin ƙarfe 9:00 na dare a ranar Alhamis 10 ga Oktoba, 2025.
Dantawaye ya zama sabon kwamishinan ’yan sandan Abuja Wani mutum ya ƙona tsohuwar budurwarsa a OyoA cewar sanarwar, jami’an sun kai samamen wata maɓoya da ke bayan jerin shagunan Ƙaramar hukumar Gombe, (Local Government Shopping Complex), inda ake zargin wasu fusatattun matasa ke gudanar da ayyuka irin na ta’ammali da miyagun ƙwayoyi.
“Da zarar matasan suka hangi isowar jami’anmu, suka tsere suka bar kayan ƙwayoyi da sauran haramtattun abubuwan da aka haramta,” in ji DSP Abdullahi.
Daga cikin abubuwan da aka ƙwato akwai nau’ukan miyagun ƙwayoyi kamar Suck and Die, Tramadol da allurarai na Diazepam.
An tura kayan shaida ɗin zuwa ofishin ’yan sanda domin ci gaba da bincike.
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Gombe, CP Bello Yahaya ne ya tabbatar da ƙudirin rundunar na ci gaba da tabbatar da Gombe ta zauna lafiya an kuma tsarkake ta daga miyagun ƙwayoyi.
Ya kuma gargaɗi masu aikata laifuka da su daina irin waɗannan ayyuka ko kuma su fuskanci hukuncin doka.