‘Yan Siyasa 11 Da Suka Faɗa Dambarwar Takardar Shaidar Karatu Ta Bogi
Published: 19th, October 2025 GMT
Haka zalika, an yi zargin cewa; bai kammala karatun digirinsa na farko ba, sannan kuma takardar shaidar yi wa kasa hidima (NYSC) da ya mika wa majalisar dokokin kasar da shugaban kasa ta bogi ce.
Sai dai, ya zargi Gwamnan Jihar Enugu, Peter Mbah, da daukar nauyin zarge-zargen da ake yi masa na takardar shedar bogin, sakamakon dalilai na siyasa.
Da yake magana ta bakin mai magana da yawunsa, Dakta Robert Ngwu, ministan ya ce; zargin da suke na siyasa ne, inda ya yi zargin cewa; gwamnan yana shirin shiga jam’iyyar APC mai mulki ne, wadda shi Nnaji ke da karfi a cikinta.
Ya kara da cewa, “Mbah yana so ya fitar da Nnaji daga tsarin ne kwata-kwata, domin kuwa yana neman wa’adi na biyu a kan mulki, sannan kuma hanya daya tak da zai iya cimma hakan shi ne, fitar da Nnaji daga tsarin, sakamakon yana so ya koma APC, amma ya sani sarai cewa; Nnaji na nan, zai kuma iya ba shi matsala,” in ji Ngwu.
Kakakin ya jaddada cewa, ministan yana ci gaba da kasancewa a matsayin tsohon dalibin jami’ar, domin kuwa yana daya daga daliban a aka yaye a watan Yulin shekarar 1985. Ya ce, Nnaji ya kammala karatunsa na B.Sc. ‘Microbiology/Biochemistry’, wanda kuma yana nan a rubuce a kundin makarantar na shekarar 1985.
Ngwu, ya dora alhakin laifin rashin gaskiya a kan hukumomin jami’ar, inda ya nuna yatsa ga mataimakin shugaban jami’ar, wanda ya ce; dan jam’iyyar PDP ne, sannan kuma wanda Gwamna Mbah ke amfani da shi wajen bata sunan ministan.
Ministan ya bukaci mahukuntar makarantar, da su ci gaba da rike taken da ake yi mata tare da dawo da martabarta ta hanyar nisantar da kansu daga tsoma baki a kan harkokin da suka shafi siyasa.
Sai dai, Gwamna Mbah ya musanta zargin na daukar nauyin wannan batanci ga ministan.
Hukumomin UNN, a nasu bangaren, sun tabbatar da cewa; Nnaji dalibin makarantar ne a wancan lokaci, amma akwai kwas din da ya fadi, ya kasa komawa ya gyara, wannan dalili ne yasa bai iya kammala karatun nasa ba.
Da take mayar da martani a kan dambarwar, fadar shugaban kasar ta ce, za ta dauki mataki bayan kotu ta yanke hukunci kan shari’ar da aka shirya yi a ranar 10 ga watan Nuwamba.
Sai dai, duk da murabus din da ya yi daga majalisar ministocin, kungiyoyin farar hula da sauran ‘yan Nijeriya na yin kira da a gurfanar da shi a gaban kuliya, bisa aikata laifin amfani da takardun jabu.
Kemi Adeosun
Tsohuwar Ministar Kudi, Kemi Adeosun, ita ma ta shiga badakalar takardar shaidar bautar kasa (NYSC) a shekarar 2018. Ta gabatar da takardar shaidar kammala bautar kasa, domin samun damar zama kwamishina a Jihar Ogun a shekarar 2011, haka nan kuma ta sake gabatar da takardar ga hukumar DSS a shekarar 2015, a matsayin wadda za ta zama minista.
Har ila yau, matsalar, ta fara ne a 2018; bayan wata kafar yada labarai ta yanar gizo ta yi zargin takardar jabun, wanda hakan yasa ta yi murabus.
A cikin wasikar murabus din da ta aike wa shugaban kasa Muhammadu Buhari, ta bayyana cewa; an haife ta ne a Kasar Birtaniya, kana kuma ba ta saba da Nijeriya sosai ba, har sai da ta kai shekara 34.
A cewarta, a lokacin da ta gano cewa takardar shaidar kammala bautar kasa (NYSC), na da matukar muhimmanci ga wadanda suka kammala karatu su yi wa kasa hidima, sai ta bukaci “wasu makusantanta a bangaren aiki”, su taimaka mata da takardar da ake bai wa wadanda shekarunsu suka kai 30, tun da adaidai lokacin take wannan shekarun, amma daga karshe; sai suka ba ta na bogi.
“A bisa wannan shawara da kuma taimakon wadanda nake ganin amintattun aminaina ne, sai na tuntubi hukumar NYSC, domin neman sanin matsayina a kan al’amarin, daga nan ne kuma sai na karbi takardar shaidar da ake magana a kanta.”
“Ban taba yin aiki a matsayin ‘yar bautar kasa ba, ban taba ziyartar harabar gidan ba, ban san yadda ake gudanar da su ba, don haka; babu wani dalili da zai sa na gane cewa; takardar shaidar ta bogi ce.”
“Hakika, na gabatar da wannan takardar shaidar a Majalisar Dokokin Jihar Ogun a 2011 da hukumar DSS ta jiha da kuma Majalisar Dokokin ta Kasa,” in ji Adeosun.
Dino Melaye
Shi ma tsohon Sanatan da ke wakiltar mazabar Kogi ta Yamma, Sanata Dino Melaye, ya shiga cikin badakalar shaidar takardun na bogi a shekarar 2017.
Bayanai sun nuna cewa, Sanatan ya kammala karatunsa na B.A. ‘Geography’ daga jami’ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zariya.
Bincike ya nuna cewa, jami’ar tana ba da B.Sc ‘Geography’ ne kadai, ba B.A. ‘Geography’ kamar yadda shaidar takardun Sanatan suka nuna ba.
Badakkalar takardar shaidar Melaye, ta bayyana ne a watan Maris na 2017, lokacin da wata kafar yada labarai ta yanar gizo (Sahara Reporters), ta yi zargin cewa; Melaye bai kammala karatun digirinsa na farko a jami’ar ABU ba, sabanin ikirarinsa na karatun ‘Geography’ a jami’ar.
Dandalin ya kuma yi zargin cewa, dan majalisar ya bai wa shugaban sashin nasa na jami’ar cin hanci, domin hada baki da shi.
Har ila yau, dandalin yanar gizon na ‘Sahara Reporters’ ya ce; wasu malamai a sashen karatu na ‘Geography’ sun dage cewa, Sanatan bai kammala karatunsa ba, inda suka kara da cewa; babu sunansa a cikin jerin sunayen daliban da aka yaye, saboda bai ci kwasa-kwasai biyar wadanda suke cikin jerin tilas sai ya ci ba.
Nan da nan rahotan ya yadu, amma Sanata Melaye sai ya yi watsi da ikirarin tare da yin barazanar gurfanar da kamfanin yada labaran, idan har ba su tabbatar da zargin ba.
Haka zalika, takardar shaidar kammala bautar kasarsa ta NYSC mai dauke da kwanan wata na ranar 8 ga Yuliin 2001, dauke da “Melaye Daniel” ba Daniel Jonah Melaye ba, kamar yadda aka nuna a takardar shaida ta digirinsa.
Haka kuma, takardar shaidar kammala karatun da Jami’ar Jos ta ba shi, wanda ya kunshi Daniel Dino Melaye, yayin da sakamakon jarrabawar da ya yi na babbar makaranta a shekarar 1992 kuma, Melaiye Daniel Jonah tare da yin bata wajen rubuta Melaye.
Ademola Adeleke
Shi ma, Gwamnan Jihar Osun, Sanata Ademola Adeleke, ya fuskanci zarge-zarge da dama dangane da sakamakon takardun karatunsa.
Abokan hamayyarsa, musamman ‘yan jam’iyyar PDP guda biyu, Rasheed Olabayo da Oluwaseun Idowu, sun maka shi a gaban wata babbar kotu a Osogbo, bisa zarginsa da yin karya a sakamakon jarrabawar da ya yi na kammala makarantar sakandire (WASSCE), domin ya samu tikitin takarar gwamna na jam’iyyar PDP a 2018, wanda daga baya aka sake tafiya zagaye na biyu a zaben.
Adeleke ya samu shaidar kammala makarantar ‘Ede Muslim Grammar School’ a shekarar 1988 da ke Jihar Osun, a lokacin da ba a kirkiro jihar ta Osun ba.
Wata shaidar kammala makarantar wadda ke dauke da sa hannun shugaban makarantar a 2018 ta bayyana cewa, wannan sa hannun ne kan takardar tun shekarar 1988, wanda hakan ya kara ta’azzara zargin da ake yi a kansa.
A kotu, shaidu sun bayyana cewa; ba su ga Adeleke ya zauna ya rubuta jarrabawa ba. Sai dai, mai shari’a Dabid Oladimeji ya yi watsi da karar, inda ya ce; masu korafin ba za su iya tabbatar da zarge-zargen cewa na jabun ba ne.
Ebans Enwerem
Eban(s) Enwerem, tare da goyon bayan shugaba Olusegun Obasanjo, ya zama shugaban majalisar dattawa a dawowar mulkin dimokuradiyya a shekarar 1999.
Sai dai, an cire shi daga mukaminsa bisa zargin karyar suna da kuma shekarunsa watanni biyar kacal da fara shugabancin nasa.
Abokin hamayyarsa, Chuba Okadigbo shi ne ya samu nasara, inda ya tsinci dami a kala sakamakon matsalar da aka samu wajen rubuta sunansa, sunan Eban ne ko Ebans. Kazalika, sun yi zargin cewa; da gangan ya yi karyar takardunsa saboda wasu dalilai boyayyu.
Lamarin dai, ya fara ne bayan da Jaridar TELL ta ruwaito cewa; takardun Enwerem na makaranta akwai matsala.
Daga nan ne kuma, sai aka kafa kwamitin da zai binciki zargin; Enwerem ya dage cewa; kuskuren rubutu ne kawai.
Bayan nan ne, sai majalisar dattawan ta yi gaban kanta wajen tsige Enwerem, yayin da ya yi wa Shugaba Obasanjo rakiya zuwa filin jirgin sama, inda yake kan hanyarsa ta zuwa ziyarar diflomasiyya, Okadigbo kuma ya maye gurbinsa.
Salisu Buhari
Shi ma tsohon kakakin majalisar wakilai, Salisu Buhari ya fuskanci zargi kan jabun shaidar takardu.
A yunkurinsa na zama dan majalisar tarayya, ya yi ikirarin cewa; yana da shekaru 36 a duniya a shekarar 1999, duk da cewa; an haife shi ne a shekarar 1970.
Kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar na 1999 ya tanada, mafi karancin shekarun da ake bukata ga ‘yan majalisa a majalisar wakilai shi ne, shekara 30.
Kazalika, ya kuma yi ikirarin cewa; ya yi karatu a Jami’ar Toronto da ke Kasar Canada, sannan kuma ya kammala karatun nasa na digiri a fannin kasuwanci, amma jami’ar ta musanta hakan, inda ta kara da cewa; bai taba zama dalibin jami’ar ba.
Haka kuma, saboda karyar takardun shaidar samun gurbin shiga jami’ar ABU, Zariya da ya yi, ya sa aka kore shi, ya kasa shiga cikin jerin shirin masu zuwa bautar kasa (NYSC).
Gaskiyar al’amarin ta fito fili a shekara ta 2000, a lokacin da Buhari ya shaida wa al’umma cikin hawaye cewa, a yafe masa bisa wannan laifi da ya aikata.
“Ina neman afuwarku, ina neman afuwar al’umma, ina kuma neman afuwar ‘yan’uwa da abokan arziki a kan wannan laifi da na aikata, tsananin son ganin na hidimta wa kasa ne, ya jawo min aikata wannan abu da na aikata, don haka; ina fatan al’umma za ta yafe min, ta kuma ba ni damar sake hidimta wa wannan kasa,” in ji shi.
Stella Oduah
Rikicin Stella Oduah, ya fara daukar hankalin al’ummar kasar nan ne a watan Janairun 2014, a lokacin da ta rike mukamin ministar sufurin jiragen sama.
Bincike ya nuna alamu na rashin gaskiya a ikirarin da ta yi game da karatun da ta a kasashen waje, ciki har da shaidar digirin girmamawa da kuma cikin takardun da aka gabatar game da matsayinta na bautar kasa (NYSC).
Gangamin da aka yi na kalubalantar ta, ya tilasta mata yin murabus tare da kuma haifar da bincike da dama a kan nata. Kazalika, a ‘yan shekarun baya, lamarin binciken ya sake kunno kai.
A shekarar 2023, masu gabatar da kara sun shigar da Oduah a gaban kuliya, bisa tuhume-tuhumen da ake zargin ta aikata, sannan kuma wani al’amari na daban ya shafi wani lauya da ya shigar da kara da ke da alaka da NYSC, ta hanyar da ta jawo cece-kuce a hukumance.
Adams Oshiomhole
Tsohon Gwamnan Jihar Edo, kuma tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole, ya jima yana fuskantar kalubale daban-daban a kan takardun makarantarsa, tun farkon fara karatunsa, wadanda ake zargin cewa; jabu ne.
Wadannan rigingimu, sun fi fitowa fili a lokacin fadan shari’a kafin zabe, sannan kuma abokan adawar siyasarsa na sake tasowa da su lokaci bayan lokaci.
Abin da ya yi fice a cikin labarin Oshiomhole shi ne, yadda kotuna ke tafiyar da al’amuran: kotuna da kotunan daukaka kara, sukan gano cewa; an tsara shari’o’in ba daidai ba, ko kuma an yi su kafin zabe, wanda hakan ke nuna cewa; kotunan zaben ba su ne hanyar da ta dace a bi wajen yanke hukunci ba, lamarin da ya kai ga yanke shari’ar ko kuma yin watsi da su, bisa dalilai na shari’a maimakon cikakken bincike na gaskiya kan takardun.
Wani al’amari mai ban mamaki, wata kotu ta yi fatali da wata shari’ar takardar shaidar jabu da aka yi masa a kan cewa; al’amarin ya kasance gabanin zabe.
Godwin Obaseki
Rigimar da ke tsakanin Tsohon Gwamnan Jihar Edo, Godwin Obaseki, ta fito fili ne a lokacin da ya jagoranci zaben fidda gwani na jam’iyyar APC a shekarar 2020.
Kwamitin tantancewar jam’iyyar ya nuna rashin jituwa a cikin takardun da Obaseki ya gabatar, musamman a bangaren NYSC dinsa, inda daga karshe kwamitin tantancewar ya hana shi tsayawa takara a jam’iyyar ta APC.
Har ila yau, kotuna da hukumar INEC sun bayyana karara cewa; takardun nasa sahihai ne, ma’ana ba jabu ba ne, wanda a karshe wannan rigima ta zama wani dalili da ya sa Obaseki ya fice daga APC, ya tsaya (ya yi nasara) a karkashin tutar jam’iyyar PDP.
Sanarwar da hukumar NYSC ta yi na cewa, ta sake bayar da takardar shaidar gyara, wani muhimmin ci gaba ne da ya sauya salon siyasar baki-daya.
Ayo Fayose
Takardun shaidar karatun Tsohon Gwamnan Jihar Ekiti, Ayo Fayose sun ta shan suka a wajen adawa a zabuka daban-daban da aka gudanar. ‘Yan adawar, sun yi zargin cewa; ya mika takardar shaidar kammala babban diploma (HND) na jabu, a lokacin da yake neman komawa kujerar gwamna.
Zargin ya shiga gaban kotuna wajen gabatar da kararraki tare da kalubalantar sakamakon zaben.
Abin mamaki shi ne, yadda kotun koli a 2015 ta yi watsi da karar da ake zargin cewa; takardun shaidar karatun nasa na jabu ne, inda ta tabbatar da hukuncin da aka yanke tun a farko da ya bai wa Fayose damar tsayawa takara.
Buhari Da Tinubu Da Jonathan
Haka zalika, Shugaban Kasa Bola Tinubu, Tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan da kuma marigayi Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, a lokuta daban-daban, sun shiga badakalar matsalar shaidar takardun makaranta, duk da sunan siyasa.
Game da marigayi, Tsohon Shugaban Kasa Buhari, musamman gabanin zaben 2015, an yi zargin cewa; bai kammala karatunsa na sakandire ba, don haka; ba shi da takardar shaidar jarrabawar SSCE , mafi karancin cancantar zama shugaban Nijeriya.
Amma saboda kokawa da aka yi a kan gwamnatin PDP, sai ‘yan Nijeriya da dama; musamman magoya bayan ‘yan adawar, suka lashi takobin zabar Buharin, a cewarsu ko da kuwa takardar shaidar biyan kudin lantarki ya gabatar a matsayin shaidarsa, wanda a karshe kuma; shi ne wanda ya lashe zaben.
ShareTweetSendShare MASU ALAKAকীওয়ার্ড: takardar shaidar kammala ar takardar shaidar bai kammala karatun ya kammala karatun kammala karatunsa yi zargin cewa Gwamnan Jihar jam iyyar PDP a majalisar a jam iyyar da takardar bautar kasa tabbatar da
এছাড়াও পড়ুন:
Ƙungiyar NNYLF Ta Gargaɗi Atiku Da Sowore Kan Cinna Wutar Rikici A Nijeriya
Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, ya bi sahun dan rajin kare hakkin dan adam kuma tsohon dan takarar shugaban kasa, Omoyele Sowore, wajen yin kira ga gwamnatin tarayya da ta gaggauta sakin jagoran kungiyar Biafra (IPOB) Nnamdi Kanu.
A cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na D, Atiku, ya bayyana ci gaba da tsare Kanu a matsayin “rashin girmama bin doka a Nijeriya.”
Kanu dai, na fuskantar tuhumar ta’addanci ne da cin amanar kasa da kuma nuna tunzura a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja, wanda kuma a lokuta da dama yake musanta hakan. Har ila yau, ya kasance a tsare tsawon shekaru duk da hukuncin da kotu ta yanke na bayar da umarnin a sake shi.
Atiku, tsohon dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, ya bayyana cikakken goyon bayansa da fafutukar da Sowore ke yi na ga nin an saki Kanu.
Da yake yin jawabi a wajen taron, Kwamared Gamji ya bayyana cewa; “Mun zo nan ne, domin mu nuna fushinmu da rashin amincwar mu da kuma nuna wa duniya cewa, ba ma tare da ‘yan siyasa masu neman mulki ido rufe a Nijeriya, wadanda ke son yin amfani da tsare Nnamdi Kanu wajen tayar da zaune tsaye a kasar.
“Tsohon dan takarar shugaban kasa kuma mamallakin gidan jaridar Sahara Reporter, Mista Omoleye Sowore, da babanmu, tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, na shirin shirya wani gangamin taro, domin sakin Nnamdi Kanu.
Ya kara da cewa, mun ji wannan sanarwa tasu, sannan kuma ba ma tare da su. “Saboda son rai irin naku, kuna so ku yi amfani da jinin matasan Nijeriya, wajen cimma burinku,” in ji Gamji.
“Babban kuskuren da za su tafkawa shi ne, ranar da za su fito, ita ce ranar da matasa sama da miliyan 63, wadanda jiga-jigan matasan Arewa ne; su ma za su fito tare da rokon Shugaba Ahmed Bola Tinubu, da ya ci gaba da gudanar da kyawawan ayyukan da sanya a gaba.
Kwamared Gamji ya kara da cewa, “Za mu mamaye dukkannin titunan Abuja, daga ranakun 20, 21 zuwa 23 ga watan Oktoba, domin nuna goyon bayanmu ga Shugaba Tinubu”.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA