HausaTv:
2025-12-03@23:38:08 GMT

Kissoshin rayuwa: Sirar Imam Hassan(a) 158

Published: 19th, October 2025 GMT

158-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin alkur’ani mai girma ko cikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin dastane rastan na Aya. Shahid Murtadha Muttahari, ko cikin littafin Mathnawi na maulana jalaluddeen Rumi ko kuma cikin wasu littafan da fatan masu sauraro zasu kasance tare da a mu a cikin shirimmu na yau.

////…Madalla. Masu sauraro a cikin shirimmu da ya gabata a kuma cikin sirar Imam Al-Hassan (a) dan Fatimah (s) diyar manzon All..(s) da muke kawo mako, a cikin shirimmu da ya gabata. Mun yi bayanin yadda Ibn Abbas ya rubutawa Imam Alhassan(a) wasika inda a ciki ya gabatar da wasu abubuwa da dama daga cikin ya bayyana masa yadda zai nada shuwagabannin a ganinsa, amma malamai sun bayyana masa cewa ya yi kuskure, a inda yake ganin a yi amfani da masu Daraja kudi da daukaka a cikin al-umma don samun biyyar mabiyansu. Wannan addinin musulunci bai zo da shi ba, addinin musulunci baya daukan wani da Daraja fiye da wani sai da tsoron All..da kuma ayyukan Alkhairi da kuma cancanta.

Amma bada matsayinsa a cikin al-ummar, kamar shugaban wata kabila, ko mai kudi ne, ko kuma don ya fito daga wata gida mai Daraja ba.

Sannan munga Aliyu (a) a lokacinda shugabancinsa, ya wata makuraishiya ta zo wan isa(a) yana cewa yanzu zaka daidaitani a rabon dukiya da wannan kuyanga ta? Sai Imam Ali (a) ya dubeta, sai ya dauko kasa da hannunsa, yana jujjuyata yana cewa wannan kasat da na nauka ba fifiko tsakanin sashinsa da sace.

A nan yana nufin ke ma da kasannan Allah ya halicceki kuyangarki ma da wannan kasar aka halicceta da me kika fishi. Don ke bakuraishiya ce kinan son a fifitaki a kan bakar fata a misala, ? a wajen All..ba wanda ya fi wani sai wanda ya fi wani tsoron All..wato akwai yiyuwar wannan kuyangar taki ta fiki Daraja a wajen All…

Kamar yadda yadda hadisin manzon All..wanda kuma ya shahara yake cewa, {dukkaninku daga Adamu ne kuma Adamu daga turbaya aka halicce shi}.

Sannan ya yi maganar ya yaki Mu’awiya kada ya mika kai gareshi har zuwa abinda All..zai yi, ko kuma mutuwa ta rabasu.

Amma bayan wannan Imam Al-hassan (a) ya  rubutawa Mu’awiya wasika inda yake kiransa zuwa shiga cikin abinda mutane suka shiga, sannan ya aika wasikar ta hannun mutane biyu, daga cikin sanannun mutane masu Daraja a cikin al-ummar musulmi. Kuma sune. Alharithu dan suwaid Attamimi, bai ga manzon All..(s) amma ya ruwaito hadisai daga wasu sahabban, sannan ya isheka girmansa, cewa ya ruwaito hadisai daga Aliyu dan Abitalib (a), sannan malaman hadisi sunce shi amintacce ne. Thiqa.

Sai kuma Jundubil Azdi Al-amuri wanda ya kasance sahabin manzon All..(s), da kuma Imam Ali(a) shima ya ruwaito hadisai daga Imam Ali )a), shi ne rawaito hadisi wanda manzon All..(s) yake cewa {Haddin wanda yake sihiri shi ne duka da takobi}  malaman hadisi sun ce mutum ne mai gaskiya kuma Amintacce, kuma thiqa. ga sassin wasikar kamar yadda take:

{Daga bawan Allah Alhassan Amirul muminin zuwa ga Mu’awiya dan Abu Sufyan.

Bayan haka. Lalle Allah ya aiki Muhammad (s) rahama ga talikai, ya bayyana gaskiya da shi, ya murkushe shirka da shi, ya kuma daukaka larabawa a ko ina suke, sannan ya daukaka kuraishawa a kebe, yana cewa (Kuma Lalle shi (alkur’ani) daukakanka da mutanen ka)

A lokacinda Allah yayi masa wafati sai larabawa suka yi jayayya a kan shugabanci a bayansa, kuraishawa suka ce: mune danginsa da kuma waliyan al-amarinsa, kada ku yi jayayya da mu a cikin shugabancinsa, sai sauran larabawa suka amince suka bar wa kuraishawa, amma kuraishawa sun yi jayayya da mu a cikin abinda larabawa suka sakan masu, faufau kurai shawa basu yi mana adalci ba, duk da cewa wasunsu sun kasance hakika mun masu falala a addini da kuma sabika a cikin musulunci ne, kuma babu mamaki jayayya da kai Mu’awiya kake da mu a cikin shugabancin ba tare da gaskiyan da aka sanshi ba. Ko wani gurbi  na abin yabo mai kyau da kuke da shi a musulunci ba, to mahadarmu da ku a wajen Allah, muna rokon Allah ya kyautata mana, kada ya bamu wani abu a wannan  duniyar wanda zai tauye matsayimmu a wajensa a lahira.

Lalle a lokacinda Allah yayi Aliyu(a) wafati , musulmi sun dorani a kan shugabanci a bayansa, ka ji tsoron Allah ya Mu’awiya. Ka dubi al-ummar Muhammadu (s), ka yi abinda zai hana zubar da jininta, ya kuma kyautata al-amarinta. Wassalam }.

Akwai wata siga ta wannan wasikar, wanda ya fi wannan bayani, amma wannan ya wadatar.

Bayanin abinda wasikar Imam Al-Hassan (a) ga Mu’awiya dan Abusufyan ya kunsa shi ne kamar haka.

01-Imam Alhassan (a) ya bayyana matsayinsa, dangane da khalifanci a addinin musulunci, yana ganin ta a matsayin hakki ne daga hakkokin iyalan gidan manzon Allah(a) ko Ahlul baiti (a) ba wanda yake tarayya da su a cikinta har abada. Kuma wanda ya kwaceta daga hannunsu, ya zaluncesu ya kuma kwace hakkinsu.

Imam (a) ya kawo hujja kan hakkinsu, na khalifanci da yadda kuraishawa suka yi jayayya da sauran larabawa bayan wafatin manzon Allah (s) kan cewa sune kabilar manzon Allah (a) su suka fi kusa da shi, don haka su suka fi cancanta da gadon shugabancinsa, don haka sun bukaci larabawa, wanda kuma su ne Ansar wadanda suka hadu a sakifa suka fito da Sa’ad dan Ubada suna son nada shi khalifa, sai kurashawa suka zo suka shiga jayayya da su, daga karshe suka bar masau, Amma a cikin khuraishawan akwai wadanda suka fi kusa da manzon Allah (S) ai, kuma sune Ahlulbaiti(a).

Amma a lokacinda Ahlulbaiti wanda Aliyu(a) yake wakiltansu ya bukaci a bashi hakkinsa, tare da gabatar da hujja irin wacce suka gabatar suka kuma kwaceta daga hannun larabawa, kan cewa shi yafi kusa da manzon Allahn(a) sai Kurasihawa suka ki yi masa adalci kamar yadda larabawa suka yi mata adalci.

Sun kwace hakkin iyalan gidan manzon Allah (a) sun hana ta , kuma Allah ne mai hukunci a tsakaninsu a ranar kiyamah.

01-Imam (a) ya bayyana dalilin da ya sa suka janye daga hakkinsu, bayan an hanasu ita. Kuma shi ne tsoron batan da kuma wargajewar addinin da kuma lalacewarshi, idan basu janye daga neman hakkinsu ba. Sai suka janye saboda masalahar addini da kuma musulmi.

Dangane da wannan Mahaifinsa Imam Ali (a), ya kara bayyana haka, a cikin wasikar da ya Aikawa mutanen kasar Masar. Inda yake fada a wani bangare daga cikinta kamar haka.

{..a lokacinda ya wuce (s) musulmi sun yi jayayya a tsakaninsu kan shugabanci a bayansa, na ranste da Allah bai taba fadawa a cikin tunani ba, kuma kwakwalwata ba, kan cewa larabawa zasu kwace shugabanci daga Ahlulbaiti bayan manzon Allah (s) ba, bai taba zuwa mani kan cewa zasu nesantar da ni daga barinsa a bayansa ba, ban Ankara ba sai na ga mutane sun kwarara suna bai’a wani wane ba, sai na janye hannuna har sai da yadda mutane suna jada baya suna barin addinin musulunci, suna kira zuwa ga shafe addinin Muhammad (s) sai na ji tsoro idan ban taimakawa musulunci da musulmi ba, to kuwa zai ga tawaya da kuma rusawarsa, sai kuma ya zama musiba a kaina zai zama mafi girma daga kubutar shugabancinku, wanda idan na same shi bai fi jin dadin duniya na kwanaki kadan ne kawai, duk abinda yake ciki a kau, kamar yadda hasken ruwa mara gaskiya yake gushewa, ko yadda gajumare yake watsewa..}.

Masu sauraro a nan zamu dasa aya a cikin shirimmu nay au sai kuma wata fitowa idan All..ya kaimu. Wassalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatu.\

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Kissoshin rayuwa: Sirar Imam Al-Al-Hassan (a) 157 October 19, 2025 KissoshinRayuwa : Sirar Imam Al-Hassan(a) 156 October 19, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan(a) 155 October 19, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 154 October 19, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Alhassan (a) 153 October 19, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 152 October 19, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 151 October 19, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 150 October 19, 2025 Wata Kotun A Murka Ta Haramtawa HKI Kafa Na’urorin Leken Asiri A Wayoyi Masu WattsApp October 19, 2025 Sojojin Najeriya: Rahotanni Dangane Da Juyin Mulki Wa Shugaba Tinubu Ba Gaskiya Bane October 19, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: larabawa suka wadanda suka masu sauraro Masu sauraro kamar yadda

এছাড়াও পড়ুন:

CBN ya kara yawan kudin da mutum zai iya cirewa a mako zuwa N500,000

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya soke iyakance adadin kuɗin da mutum ko kamfani za su iya ajiyewa a banki sannan ya ƙara yawan kudin da za a iya fitarwa a mako da ₦100,000 zuwa ₦500,000.

Wannan na cikin wata sanarwa da Daraktar Sashen Tsarin Kuɗi da Dokoki ta bankin, Dr. Rita Sike, ta sanya wa hannu kuma ta fitar ranar Laraba.

Gobara ta kashe mata da miji da ’ya’yansu 3 a Katsina Mako mai Majalisa za ta kada ƙuri’a kan ƙudurin ƙirƙirar sabbin jihohi

A cewar bankin, an yi sauye-sauyen manufofin ne da nufin rage tsadar sarrafa kuɗi, magance matsalolin tsaro, da kuma dakile haɗarin safarar kuɗi ba bisa ka’ida ba da ke da alaƙa da dogaro da mu’amalar kuɗi kai tsaye.

CBN ya ce manufofin da suka gabata kan kuɗi an gabatar da su ne domin rage amfani da kuɗi kai tsaye da ƙarfafa amfani da hanyoyin biyan kuɗi ta intanet.

Sai dai, sauye-sauyen tattalin arziki da na gudanarwa sun sa dole a sake duba dokokin domin daidaita su da halin da ake ciki a yanzu.

Daga ranar 1 ga watan Janairun 2026, an soke iyakance adadin kuɗin da za a iya ajiye gaba ɗaya, kuma ba za a sake cajin kuɗin da ake ɗauka a kan ajiya mai yawa ba.

Sabbin dokokin sun jingine iyakance fitar kuɗi na mako gaba ɗaya ga mutum ɗaya zuwa ₦500,000, yayin da na kamfanoni ya koma ₦5m.

Kazalika, dokar ta ce fitar kuɗin da ya wuce waɗannan iyakokin zai jawo ƙarin caji na kaso cikin 100 ga mutum ɗaya da kuma kaso biyar cikin 100 ga kamfanoni, inda za a raba kuɗin da aka tara da bankuna bisa tsarin 40:60 tsakanin CBN da bankunan da abin ya shafa.

CBN ya kuma umarci bankuna da su tabbatar da cewa sun saka dukkan nau’o’in kuɗi a cikin na’urar ATM domin sauƙaƙa samun kuɗi.

Babban bankin ya kuma umarci bankuna da su rika gabatar da rahoton wata-wata ga Sashen Kula da Bankuna, Sashen Kula da Sauran Hukumomin Kuɗi, da Sashen Kula da Tsarin Biyan Kuɗi domin tabbatar da bin doka.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Rikicin Kungiyoyin Asiri Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Wani Matashi A Jihar Kwara
  • CBN ya kara yawan kudin da mutum zai iya cirewa a mako zuwa N500,000
  • Wani ya yi shigar mahaifiyarsa da ta mutu ya je karvar kuxin fanshonta
  • Sharhi:’HKI tana fama da karancin sojojin a dukkan rassan sojojin kasar’.
  • Tinubu ya naɗa Janar Christopher Musa sabon Ministan Tsaron Nijeriya
  • An yi garkuwa da manoma 11 a Kudancin Kaduna
  • Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 165
  • Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan 164
  • Yawan Yahudawan Da Suke Ficewa Daga HKI Sun Nininka Har Sau 100%
  • ’Yan bindiga sun sace fasto da matarsa  masu ibada a Kogi