ICC ta ki amincewa da daukaka karar Isra’ila
Published: 19th, October 2025 GMT
Kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa ta yi watsi da daukaka karar da Isra’ila ta shigar kan sammacin da ta fitar a baya na kama Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu da tsohon ministan tsaro Yoav Gallant. .
A watan Nuwamba ne, kotun ta fitar da sammacin bisa zargin aikata laifukan yaki da cin zarafin bil’adama a Gaza.
Sammacin ya fusata Isra’ila da Amurka, wadanda tun daga lokacin suka kakabawa manyan jami’an ICC din takunkumi.
Benjamin Netanyahu ya kira matakin a matsayin “mai nuna kyama ga Yahudawa.”.”
A cikin watan Mayu, Isra’ila ta bukaci kotun ta ICC da ta yi watsi da sammacin.
Kotun dai ta yi watsi da bukatar ne a ranar 16 ga watan Yuli.
Mako guda bayan haka Isra’ila ta nemi izinin daukaka kara kan hukuncin, amma alkalan kotun sun yanke hukunci a ranar Juma’a cewa “batun kamar yadda Isra’ila ta tsara, ba za a daukaka kara ba.”
“Saboda haka majalisar ta ki amincewa da bukatar,” in ji kotun ta ICC
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka MDD : “Zai dauki lokaci” kafin a rage yunwa a Gaza October 19, 2025 Kissoshin rayuwa: Sirar Imam Hassan (a) 159 October 19, 2025 Kissoshin rayuwa: Sirar Imam Hassan(a) 158 October 19, 2025 Kissoshin rayuwa: Sirar Imam Al-Al-Hassan (a) 157 October 19, 2025 KissoshinRayuwa : Sirar Imam Al-Hassan(a) 156 October 19, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan(a) 155 October 19, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 154 October 19, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Alhassan (a) 153 October 19, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 152 October 19, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 151 October 19, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: Isra ila ta
এছাড়াও পড়ুন:
Aljeriya: Taron Kasashen Afirka Kan Amincewa Da Mulkin Mallaka A Matsayin Laifi
Wakilan kasashen Afirka da suka hallara a birnin Algiers sun sabunta wani yunkuri don amincewa da laifukan ‘yan mulkin mallaka a hukumance, tare da ayyana mulkin mallaka a matsayin laifi kan bil’adama, da kuma tabbatar da an biya diyya bisa ga barna da cin zarafi da aka yi wa al’ummomin Afirka.
Taron, wanda aka gudanar a babban birnin Aljeriya, an gudanar da shi ne bisa wani kuduri na Tarayyar Afirka (AU) da aka amince da shi a farkon wannan shekarar wanda ke kira da a yi adalci wajen biyan diyya don magance illolin siyasa, tattalin arziki, da zamantakewa da suka faru sakamakon mulkin mallaka.
Ministan Harkokin Wajen Aljeriya Ahmed Attaf ya ce tarihin Aljeriya a karkashin mamayar Faransa ya sanya kasar ta zama muhimmin wuri na taron. Ya jaddada cewa dole ne a dauki diyya a matsayin wajibi na shari’a, ba wata alama ta alheri ko taimako ba.
Ya kuma jaddada cewa Afirka tana da ikon neman a amince da laifukan da aka aikata wa al’ummarta a lokacin mulkin mallaka,” wanda ke ci gaba da aifar da matsaloli da koma baya a bangarori daban-daban a nahiyar sakamakon illoli na mulkin mallaka.
Tsakanin 1954 da 1962, Aljeriya ta sheda daya daga cikin yaƙe-yaƙe mafi muni da kuma zubar da jini da aka yi tsakaninta da masu mulkin mallaka. An kashe dubban daruruwan mutanen kasar .
Attaf ya ce wahalhalun da Aljeriya ta fuskanta sun kasance “abin koyi ne amma mai wahala, kuma ya zama wajibi ya zama mafari na soma neman hakkokin da aka saryar na al’ummar Afirka sakamakon zalunci na ‘yan mulkin mallaka.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Lebanon: An Gudanar Da Taron Musulunci da Kiristanci a Beirut tare da halartar Paparoma December 2, 2025 Chuck Schumer: Trump Ba Shi da Ikon Kaddamar da Yaki Kan Venezuela December 2, 2025 Najeriya: Matatar Dangote Za Ta Mika Tataccen Mai Lita Biliyan 1.5 A Watan Disamba December 2, 2025 Ramaphosa ya yi watsi da barazanar Trump na ware Afirka ta Kudu daga G20 December 2, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 165 December 1, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan 164 December 1, 2025 Baqaei: Amurka Ce Babbar Barazana Ga Zaman Lafiya Da Tsaro A Duniya December 1, 2025 Paparoma Leo Na 14 Yana Ziyarar Aiki Na Kwanaki 3 A Kasar Lebanon December 1, 2025 Kamaru: Madugun Adawa Ya Rasu A Gidan Kaso December 1, 2025 Tawagar ECOWAS Ta Bar Guinea – Bissau bayan da shugaban kasar yayi barazanar korarsu Da Karfi December 1, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci