Grossi: Za a iya warware batun Shirin nukiliyar Iran ne kawai ta hanyar diflomasiyya
Published: 20th, October 2025 GMT
Darakta Janar na Hukumar Makamashin Nukiliya ta Duniya (IAEA) Rafael Grossi ya bayyana kwarin gwiwar cewa, za a iya warware takkadama kan shirin Iran na makamashin nukiliya ne ta hanyar diflomasiyya kadai.
Grossi ya bayyana hakan ne a wata hira da jaridar Neue Zeitung ta kasar Switzerland a jiya Lahadi.
Shugaban hukumar ta IAEA ya ce, masu binciken ba su sami wata shaida da ke nuna cewa Iran ta boye wani adadi na sinadarin uranium da aka inganta ba.
Ya kara da cewa, “Yawancin abubuwan da aka samu na Iran an adana su ne a wuraren da aka sani a Isfahan da Fordow, da kuma wani lokaci a Natanz.” in ji shi.
Grossi ya bayyana kwarin gwiwa cewa “za a gano wata hanyar diflomasiyya ta warware takaddamar da ke tattare da shirin nukiliyar na Iran.”
“Dawo da dukkan bangarorin da ke takaddama a kan teburin tattaunawa zai iya ceton mu daga wani hadari na barkewar wani sabon yaki a nan gaba, in ji Grossi.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Trump: Shuwagabanin Hamas ba su da hannu a kisan sojojin Isra’ila 2 a Gaza October 20, 2025 Iran Da Azerbaijan Suna Gudanar Da Atisayrn Hadin Guiwa Na Sojojin Ruwa A Tekun Caspian October 20, 2025 Gwamnatin Yamen Tana Tsare Da Ma’aikatan MDD 50 Ta Kuma Kwace Kayakin Aikinsu October 20, 2025 Gwamnatin Colombia Ta Bukaci Bayani Daga Amurka Kan Kashe Wani Dan Kasar A Tekun Carabian October 20, 2025 An Fara Kidayar Kuri’un Zabukan Kananan Hukumomi 16 Da Aka Yi A Libya October 19, 2025 Araqchi: Iran Da Kasashen China Da Rasha Suna Shirin Kawo Karshen Takunkuman Turai October 19, 2025 Miliyoyin Mutanen Amurka Sun Yi Zanga-zanagr Nuna Kin Jinin Donald Trump October 19, 2025 Sheikh Na’im Kassim Ya Mika Sakon Ta’aziyyar Shahadar Gumari Na Kasar Yemen Ga Sayyid Husi October 19, 2025 Sojojin HKI Sun Shiga Cikin Yankin Qunaidhara Na Kasar Syria October 19, 2025 Gaza: HKI Tana Ci Gaba Da Keta Yarjejeniyar Tsagaita Wuta October 19, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
NAPTIP ta daƙile yunƙurin safarar mutum 7 daga Kano zuwa Saudiyya
Hukumar Hana Safarar Mutane (NAPTIP) shiyyar Kano, ta kama wani mutum da ya yi yunƙurin safarar wasu mata bakwai zuwa Saudiyya.
Jami’an NAPTIP sun kai samame wani gida a Kano a ranar 2 ga watan Nuwamba, 2025, bayan samun bayanan sirri, inda aka ɓoye matan da ake shirin safararsu.
Na gana da Tinubu kan Kanu ba batun sauya sheƙa ba — Gwamnan Abia ’Yan Najeriya suna da ƙwarin guiwa a kaina, ba zan ba su kunya ba — Ministan TsaroA cewar Mohammed Habib, Jami’in Hulɗa da Jama’a na NAPTIP a Kano, an ajiye matan a gidan ne yayin da ake shirin tura su Saudiyya domin yin aikatau.
Ya ce, “Bincike ya nuna cewa biyu daga cikin waɗanda aka ceto ’yan Nijar ne, yayin da biyar kuma ’yan Najeriya ne.”
Ya ƙara da cewa, “An kai matan Accra a Ghana, inda aka yi musu biza. Kuma duka aikin da za a musu bashi ne, inda kowacce za ta biya Naira miliyan 10, idan sun yi aikin wahala a Saudiyya .”
NAPTIP ta bayyana cewa an riga an kammala shirin tura matan filin jirgin saman Abuja a ranar 3 ga watan Disamba, 2025, wanda a nan aka shirya tafiyarsu Saudiyya.
Hukumar ta ce an kama mutum ɗaya, yayin da sauran waɗanda ke da hannu a lamarin suka tsere.
Jami’in, ya tabbatar da cewa hukumar na ci gaba da bincike domin kama sauran da suka tsere.