Jihar Jigawa Ta Dukufa Wajen Gina Magudanan Ruwa Domin Kaucewa Ambaliya
Published: 17th, October 2025 GMT
An fara gina magudanan ruwa domin dakile afkuwar ambaliyar ruwa a kananan hukumomin Malam Madori da Kaugama dake jihar Jigawa.
Tawagar Injiniyoyin jihar karkashin jagorancin Daraktan kula da ambaliyar ruwa da zaizayar kasa, Injiniya Mukhtar Muhammad Usman sun ziyarci kananan hukumomin domin duba yadda aikin ke gudana.
Haka zalika Daraktan da mataimakin sa Injiniya Mahdi Isyaku da sauran ma’aikata ssn ziyarci wurin da ambaliyar ruwa tayi ta’adi a garin malam Madori.
A lokacin da tawagar ta fara auna fili da tona magudanun ruwan, daraktan ya ce an fara aikin tona magudanar ruwa mai tsawon kilomita 2 a matsayin wani ɓangare na aikin karkatar da ruwan da ya lalata wurare zuwa sabon wurin da aka tsara.
Yana mai cewar, har ila yau, ana gina wani magudanar ruwa mai tsawon mita 300 a unguwar Gandun Sarki, yayin da aka kammala wasu masu tsawon fiye da mita 390 a Kantamari da kuma mai tsawon sama da mita 500 a Zaburan dake karamar hukumar Kaugama.
Wakilin mazabar Mallam Madori a majalisar dokokin jihar, Alhaji Hamza Adamu Babayaro Malam Madori ya halarci bikin kaddamar da aikin magudanar ruwa mai tsawon mita 2,000 a unguwar Kampala don rage illar ambaliya a yankin.
Shi kuwa shugaban al’ummar Kampala, Ibrahim Zakar, yayi alkawarin samar da masauki ga ma’aikatan domin samun saukin gudanar da aiyukan su don kwalliya da biya kudin sabulu.
A jawabin sa Shugaban karamar hukumar Malam Madori, Alhaji Salisu Sani Garun-Gabas, ya yabawa Gwamna Umar Namadi bisa cika alkawarin da ya dauka a lokacin ziyarar da ya kai yankin, na dakile faruwar ambaliyar da ta lalata gidaje da dama a unguwar Kampala.
Salisu Garun Gabas, ya sami wakilcin mataimakiyar sa ,Hajiya Amina Haruna Dokaje, wacce ta jagoranci kaddamar da aikin tonan magudanar ruwa.
Usman Mohammed Zaria
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Jigawa Magudanan Ruwa magudanar ruwa
এছাড়াও পড়ুন:
Sin Tana Adawa Da Matakan Kuntatawa Na Amurka Kan Bangarorin Kasar Da Suka Shafi Harkokin Teku Da Jigila Da Ginin Jiragen Ruwa
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Kowacce Mace Tauraruwa Ce A Kasar Sin October 14, 2025
Daga Birnin Sin Shawarwarin Sin Sun Bude Sabuwar Hanyar Bunkasa Ci Gaban Mata A Duniya October 14, 2025
Daga Birnin Sin Al’ummun Kasashe Daban-Daban Sun Yabawa Shawarwarin Sin Dake Taimakawa Wajen Dunkulewa Don Hanzarta Ci Gaban Mata October 14, 2025