HausaTv:
2025-10-18@16:30:20 GMT

Madagascar : An rantsar Da Michael Randrianirina A Matsayin Shugaban Kasar

Published: 18th, October 2025 GMT

A Madagaska jiya Juma’a ne kotun tsarin mulkin kasar ta rantsar da Kanar Michael Randrianirina a matsayin shugaban kasa.

Hakan na zuwa ne bayan majalisar dokokin kasar ta tsige shugaban kasar Andry Rajoelina bayan ya tsere daga kasar sanadiyyar zanga zangar data rikide zuwa bore wa gwamnatinsa saboda matsalar wutar lantarki da ruwan sha.

Tunda farko dai kanar Randrianirina ya kiyasta zai rike mulki na wa’adin watanni 18 zuwa 24 lokacin da za’a kai ga gudanar da zaben raba gardama na kundin tsarin mulkin kasar.

A ranar Talata da ta gabata ne, Randrianirina ya sanar da juyin mulkin kwace Mulki a kasar yana mai danganta hakan da rashin biyayya ga kundin tsarin mulkin kasar, da keta hakkokin bil’adama.

 A kuma Talatar ne majalisar wakilan kasar ta jefa kuri’ar tsige shugaba Andry Rajoelina yayin wani zama na musamman, duk da cewa shugaba Rajoelina ya riga ya ayyana rushe majalisar.

A karshen watan Satumban da ya shude ne rikici ya barke a kasar, biyowa bayan tsanantar karancin wutar lantarki da ruwan fanfo.

An kuma samu tashe-tashen hankula yayin zanga-zanga, lamarin da ya rikide zuwa ga kiraye-kirayen shugaban kasar ya yi murabus, lamarin da ya tilata mas yin murabus.

Tuni Tarayyar Afirka (AU) ta dakatar da kasar ta Madagascar daga kungiyar bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a ranar Talata.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Iran Ta yi Tir Da Harin da Isra’ila Ta kai Kudancin Kasar labanon. October 18, 2025  Majalisar Dattawa Za Ta Gana Da Ministan Ilimi Kan Batun Yajin Aikin Asuu. October 18, 2025 Gaza ta bukaci a binciki Isra’ila kan sace sassan jiki a gawarwakin falasdinawa October 18, 2025 Madagaska : An rantsar da Kanar Randrianirina a matsayin shugaban kasa October 18, 2025 Al-Houthi: Matsin lamba bai hana Iran ci gaba da goyon bayan Falasdinu ba October 18, 2025 Marzieh Jafari  Ta Dauki Lambar Yabo Ta Horar Da Mata Wasan Kwallon Kafa Ta Nahiyar Asia October 18, 2025 Iran: Kudurin Kwamitin Tsaro Kan Yarjeniyar JCPOA Ya Kawo Karshe A Yau October 18, 2025 Iran: Kauyuka 3 Sun Shiga Cikin Wuraren Bude Ido Na Duniya October 18, 2025 Aref: Kofar Tattaunawa A Bude Take, Amma Ba Zamu Amince Da Bukatun Da Basa Da Ma’an Ba October 18, 2025 Kenya Ta Yiwa Raila Odinga Jana’iza Ta Musamman October 18, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Venezuela Ta Bada Sanarwan Sabbin Matakan Tsaro A Kan Iyakar Kasar Da Colombia

Shugaban kasar Venezuelan Nicolás Maduro ya bayyana sabbin matakan tsaro a kan iyakar kasar da kasar Colombia bayan da gwamnatin Amurka ta sabonta sabbin matakai na nuna adawa da gwamnatin kasar.

Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya bayyana cewa shugaban ya shelanta wannan sabbin matakan tsaro ne bayan da gwamnatin shugaba Trump ba bawa hukumar CIA izinin aiki tukuru don kifar da gwamnatin shugaba Madoro na kasar Venezuela.

Sabbin matakan tsaron dai sune kyautata tsaro a kan iyakar kasar da kasar Colombia wanda ya hada kan iyakoki da kasar a cikin Jihohin, Táchira, Apure, da kuma  Amazonas wadanda suke kan iyakoki mafi tsawo da kasashe makobta.

Yace tabbatar da taro a kan iyakokin kasar Colombia da wadan nan jihohi yana da matukar Muhimmanci. Yace mutanen kasar Venezuela mutanen ne wadanda suke son zaman lafiya da kuma mutunci da kuma kare mutuncinsu.

Jaridar NewYork Times ta Amurka ta nakalto shugaban kasar Amurka Donal Trump ya bawa hukumar leken asiri na kasar CIA a ranar talata kan cewa ta tsara masa yadda zai kwace kasar Venezuela daga hannun Nicolas Madoro daga ciki har da kai hare-hare kan kasar idan ya kama.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label Name* Email* Website Label Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Tarayyar Afirka AU, Ta Jingine Samuwar Madagaska Daga Cikin Kungiyar October 16, 2025 Iran Ta Jaddada Cewa: A Shirye Take Ta Tattauna Amma Ba Zata Amince Da Juya Akalarta Ba October 16, 2025 Kasashen Iran Da Tunusiya Sun Jaddada Karfafa Alaka A Tsakaninsu A Bangarori Da Dama October 16, 2025 Kasar Afirka Ta Kudu Ta Jaddada Aniyarta Ta Ci Gaba Da Shari’ar Neman Hukunta Isra’ila Kan Batun Gaza October 16, 2025 Gwamnatin Kamaru Ta Gargadi Dan Takarar Da Ya Shelanta Kansa A Matsayin Wanda Ya Lashe Zabe October 16, 2025 Ministocin Harkokin Wajen Kungiyar NAM Sun Nuna Goyon Bayansu Ga Venezuela October 16, 2025 Sojojin Pakistan Sun Tarwatsa Tankokin Yaki 6 Na Afghanistan A Rikicin kan Iyaka October 15, 2025 Tawagar Super Eagles Ta Nijeriya Ta Lallasa Benin Da ci 4-0 A Uyo October 15, 2025 Matakin Kasashen Yamma Na Maidowa Da Iran Takunkumi Ya Sabawa Doka. October 15, 2025 Kasar Indunusiya Ta Sanar Da Goyon Bayanta Ga Alummar Falasdinu October 15, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Madagascar : An rantsar da Michael Randrianirina a matsayin shugaban kasar
  • An rantsar da Randrianirina shugaban Madagascar
  • Kasar Yamen Ta Sanar Da Nadin Sabon Babban Hafsan Hafsoshin Sojin Kasar
  • Majalisar Dattawa Ta Amince Da Amupitan A Matsayin sabon Shugaban INEC
  • Shugaban Kasar Sudan Yana Ziyarar Aiki A Kasar Masar
  •  WJ: Amurka Tana Tara Rundunonin Yaki A Zagayen Kasar Venezuela
  • Madagaska : Ranar Juma’a za’a rantsar da Kanar Randrianirina
  • Venezuela Ta Bada Sanarwan Sabbin Matakan Tsaro A Kan Iyakar Kasar Da Colombia
  • Gwamnatin Kamaru Ta Gargadi Dan Takarar Da Ya Shelanta Kansa A Matsayin Wanda Ya Lashe Zabe