Sheikh Abdulaziz Al-Sheikh ya rasu yana da shekara 82
Published: 23rd, September 2025 GMT
Allah Ya yi wa Babban Mai Ba da Fatawa na kasar Saudiyya, Sheikh Abdulaziz bin Abdullah bin Mohammed Al Al-Sheikh, rasuwa.
Hukumomin ƙasar Saudiyya sun sanar da cewa Sheikh Abdulaziz bin Abdullah bin Mohammed Al Al-Sheikh ya rasu yana da shekara 82 a duniya.
Fadar Masarautar ƙasar da kuma Shugaban Majalisar Malaman Masallata Haraman Makkah da Madina, Sheikh Abdul Rahman Sudais, sun gabatar da ta’aziyyar iyalai da ɗaliban mashahurin malamin.
Za a gudanar da Sallar Jana’izarsa a Masallacin Imam Turki bin Abdullah da ke birnin Riyadh bayan Sallar La’asar.
Kazalika za a yi masa Salatul Ga’iba a Masallacin Harami na Makkah da kuma Masallacin Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama da ke Madina.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
An ƙone al’aurar ’yar shekara 5 saboda fitsarin kwance a Bauchi
Ana zargin wata matar aure, Rabi Nuhu da ke garin Magama Gumau a ƙaramar hukumar Toro ta Jihar Bauchi, da cin zarafin wata yarinya ’yar shekara biyar ta hanyar ƙone mata al’aura, saboda zargin tana yawan yin fitsarin kwance.
Wakilinmu ya gano cewa yarinyar marainiya ce wadda mahaifiyarta ta rasu kusan shekara ɗaya da ta gabata, inda take zaune tare da mahaifinta, Mohammed Umar, da matarsa.
CBN ya rage kuɗin ruwa zuwa kashi 27 cikin 100 Mahara sun kashe ɗan sanda sun ɗauke bindigarsa a TarabaWani mai fafutukar kare haƙƙin bil’adama a garin, Kabiru Abdulkadir, ya bayyana cewa sai bayan kwana biyar da ƙonewar ta faru ne al’amarin ya bayyana.
“Don guje wa matsala, mahaifin yarinyar ya sayi wata katifa ta daban domin ta riƙa kwanciya a kai, amma duk da haka matar tasa ba ta daina azabtar da yarinyar ba,” in ji Kabiru.
Aminiya ta ruwaito cewa, lamarin ya bayyana ne lokacin da yarinyar ta roƙi kawunta ya saya mata katifa, inda ta shaida masa cewa mamanta ta ƙona al’aurarta saboda yawan fitsarin kwance, dalili ke nan da ya yi wa ’yan sanda ƙorafi.
Kazalika, ana zargin cewa duk lokacin da matar ta samu sabani da mijinta, sai ta huce fushi a kan yarinyar.
Da yake jawabi, mahaifin yarinyar, Mohammed Umar, wanda ke aiki da wani gidan talabijin, ya tabbatar da cewa matarsa ta kan yi ƙorafi kan yawan fitsarin kwancen yarinyar, abin da ya sa ya saya mata katifa ta daban.
Umar ya ce: “A farko, da na ga ƙuna a jikinta, matata ta shaida min wai shayi mai zafi ne ya zubo a jikinta. A lokacin na gaskata hakan, har sai da na lura da ciwon yana ƙaruwa.”
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi, CSP Mohammed Wakil, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana cewa rahoto ya iso ofishin su da misalin ƙarfe 3:00 na ranar 13 ga Satumba, 2025.
Wakil ya ce yarinyar ta sami ƙonuwa a ƙasan cikinta, cinyoyinta, da kuma al’aurarta.
Ya ƙara da cewa, kwamishinan ‘yan sanda na jihar, Sani Omolori Aliyu, ya bayar da umarnin a gaggauta kama matar tare da miƙa ta zuwa sashen manyan laifuka domin gudanar da cikakken bincike.
Ya bayyana cewa da zarar an kammala binciken, za a gurfanar da ita a gaban kotu.