Jami’an tsaro sun buɗe wa masu zanga-zangar Nnamdi Kanu wuta a Abuja
Published: 20th, October 2025 GMT
Masu zanga-zangar neman a sako jagoran ’yan awaren Biafra, Nnamdi Kanu sun watse bayan jami’an tsaro sun yi amfani da harsasai masu rai domin tarwatsa su.
A safiyar Litinin ɗin nan nan ne masu zanga-zangar suka fito kan titunan Abuja, duk da umarnin kotu da ta hana su zanga-zangar a kuma da a Fadar Shugaban Ƙasa.
Zanga-zangar ta samu jagorancin dan gwagwarmaya kuma tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar African Action Congress (AAC), Omoyele Sowore, wanda shi ne mai jagorantar motsin #RevolutionNow.
Mutanen sun fara taruwa tun karfe 6:50 na safe a kusa da ofishin Ma’aikatar Harkokin Mata.
Shaidu sun ce jami’an tsawon haɗin gwiwar ’yan sanda, da sojoji da DSS da Sibil Difens (NSCDC) ne suka yi dirar mikiya wajen.
Jami’an tsaron sun fara tsaurara matakan tsaro tun ranar Lahadi a kusa da Fadar Shugaban Ƙasa da Majalisar Dokoki ta Ƙasa Kotun Daukaka Kara, da kuma Dandalin Eagle Square, bayan masu zanga-zangar sun dage cewa sai sun isa har fadar shugaban ƙasa domin miƙa buƙatunsu kan ci gaba da tsare Nnamdi Kanu.
Shaidun sun ce rikicin ya fara ne bayan Sowore da wasu masu zanga-zanga suka fara rera wakokin goyon bayan #FreeNnamdiKanuNow yayin da suke ƙoƙarin wucewa kusa da Kotun Ɗaukaka Kara. Nan ne jami’an tsaro suka fara buɗe wuta.
Da farko masu zanga-zangar sun ɗauka cewa jami’an tsaron na harba barkonon tsohuwa ne, amma daga bisani aka tabbatar cewa harsasai na gaske ne ke tashi daga wurare daban-daban.
“Kada ku harba mana da barkonon tsohuwa! Ku mutunta doka! Muna da ’yanxin yin zanga-zanga, mu ’yan Najeriya ne!” in ji Sowore cikin murya daya da sauran masu zanga-zangar.
Bayan wannan kalamai, sai aka fara harbe-harbe, wanda hakan ya sa jama’a suka fara gudu don tsira da rayukansu.
A lokacin da ake hada wannan rahoto, motocin sulke sojoji, ’yan sanda, da DSS suna nan a bakin aiki a muhimman hanyoyi kusa da tsakiyar birnin.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Jami an Tsaro masu zanga zangar jami an tsaro
এছাড়াও পড়ুন:
Mutum 6 sun rasu, 13 sun jikkata a hatsarin mota a Kogi
Aƙalla mutum shida ne suka rasu, yayin da wasu 13 suka jikkata, bayan wata bas ɗauke da nakasassu ta yi hatsari a kan hanyar Lokoja zuwa Okene.
Waɗanda abin ya shafa suna komawa Okene ne bayan halartar bikin Ranar Nakasassu ta Duniya ta 2025 a Gidan Gwamnatin Jihar da ke Lokoja.
Jirgin fadar shugaban ƙasa ya ƙi sayuwa wata 5 bayan saka shi a kasuwa ’Yan sanda sun kama mutum 28 kan zargin lalata mata da yara a YobeAn garzaya da waɗanda suka jikkata zuwa asibitoci daban-daban a jihar, inda suke ci gaba da samun kulawa.
Kwamishinan Harkokin Sadarwa na Jihar Kogi, Kingsley Femi Fanwo, ya ce wannan hatsari abun baƙin ciki ne ga gwamnati da jama’a.
Ya ce Gwamna Ahmed Usman Ododo ya umarci gwamnatin jihar da ta biya dukkanin kuɗin maganin waɗanda suka jikkata kuma ta tura jami’ai zuwa asibitoci don tallafa wa waɗanda abin ya shafa da iyalansu.
Fanwo ya ce: “Gwamnatin Jihar Kogi tana jimami sosai tare da iyalan waɗanda suka rasu guda shida, kuma za ta tallafa musu.”