Hamas ta yi Allah wadai da Isra’ila kan keta yarjejeniyar tsagaita bude wuta
Published: 19th, October 2025 GMT
Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta yi Allah wadai da Isra’ila kan keta yarjejeniyar tsagaita bude wuta, tare da yin Allah wadai da ci gaba da rufe mashigar Rafah a matsayin wani mataki na karan tsaye ga sulhun.
A cikin wata sanarwa da ta fitar, Hamas ta yi Allah wadai da matakin da firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya dauka na jinkirta bude mashigar Rafah tare da bayyana hakan a matsayin karya sharuddan tsagaita bude wuta da kuma kaucewa alkawurran da aka dauka ga masu shiga tsakani da masu bada garantin.
Kungiyar ta yi gargadin cewa rufewar yana kuma kawo cikas ga zuwan tawagogi na musamman domin zakulo gawarwakin da ke karkashin baraguzan gine gine da kuma gano wadanda suka mutu, ciki har da gawarwakin mutanen Isra’ila da aka yi garkuwa da su da za a mayar da su karkashin yarjejeniyar tsagaita bude wuta. Kungiyar masu fafutukar kare hakkin bil adama ta ce Isra’ila ta keta yarjejeniyar tsagaita bude wuta sau 47 tun bayan aiwatar da ita a makon jiya, inda ta kashe Falasdinawa 38 tare da jikkata wasu 143 na daban
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka An gudanar da zanga-zanga a sassa da dama na Amurka October 19, 2025 MDD : “Zai dauki lokaci” kafin a rage yunwa a Gaza October 19, 2025 ICC ta ki amincewa da daukaka karar Isra’ila October 19, 2025 Kissoshin rayuwa: Sirar Imam Hassan (a) 159 October 19, 2025 Kissoshin rayuwa: Sirar Imam Hassan(a) 158 October 19, 2025 Kissoshin rayuwa: Sirar Imam Al-Al-Hassan (a) 157 October 19, 2025 KissoshinRayuwa : Sirar Imam Al-Hassan(a) 156 October 19, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan(a) 155 October 19, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 154 October 19, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Alhassan (a) 153 October 19, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: yarjejeniyar tsagaita bude wuta Allah wadai da
এছাড়াও পড়ুন:
Gobara ta ƙone kasuwar katako a Abuja
Wata gobara ta tashi a ranar Laraba ta ƙone kasuwar katako da ke kusa da Jabi Masallaci a Abuja.
Gobarar ta lalata kaya da kayan gini na miliyoyin kuɗi, amma ba a yi asarar rai ba.
CBN ya kara yawan kudin da mutum zai iya cirewa a mako zuwa N500,000 Gobara ta kashe mata da miji da ’ya’yansu 3 a KatsinaKawo yanzu dak ba a san musababbin tashin gobarar ba.
Sai dai wasu rahotanni na cewa gobarar na iya farawa ne sakamakon matsalar wutar lantarki, wanda wani lokacin wayoyin wuta na faɗowa kan rumfunan kasuwa.
’Yan kasuwa da mazauna yankin sun yi ƙoƙarin kashe wutar, amma ta yaɗo cikin sauri saboda katako da sauran kayayyakin gini na da saurin kamawa da wuta.
Wasu gine-gine da ke kusa da kasuwar sun lalace, lamarin da ya tilasta wa jama’a gudu domin tsira da rayukansu.
Daga baya jami’an Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya sun isa wajen tare da kashe wutar.
Mutanen da abin ya shafa sun roƙi gwamnati ta taimaka musu, domin sun rasa duk abin da suka dogaro da shi wajen kula da rayuwarsu.