KissoshinRayuwa : Sirar Imam Al-Hassan(a) 156
Published: 19th, October 2025 GMT
156-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshin da suka zo cikin alkur’ani mai girma ko cikin wasu littana wadanda suka hada da littafin Dastane Rastan na Aya. Murtadha Muttahari, ko kuma cikin littafin Mathnawa, na maulana jalaluddeen Rumi ko kuma cikin wasu littafan da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu a cikin shirimmu na yau.
////… Madallah, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, a kuma cikin sirar Imam Hassan Al-Mujtaba(a) dan Fatimah diyar manzon All..(s) da muke kawo muku. Mun yi maganar yadda, yadda Mu’awiya dan abusufyan ya kidemi bayan bayan ya sami labarin cewa an yiwa Imam Hassan bai’a a matsayin Khalifan musulmi a kufa, sannan ya kira taron mashawartansa suka zauna suka kuma fidda wassu al-amura guda biyu don fuskantar Imam Al-Hassan(a). Kuma sune, aika jasusu mai aiko masu labarai sirri daga kasar Iraki, musamman a biranen Kufa da Basra wadanda suka kasance manya-manyan garuruwan a lokacin a kasar Iraki.
Sannan na biyu kuma suna son sayan wasu manya-manyan shugabannin Iraki wadanda suke taimakawa Imam Alhassan (a) don su barshi shikadai, hakan zai tilasta masa ya mika kai ga mu’awiya dan Abusufyan.
Sannan ba tare da bata lokaci ba suka aika mutanen biyu zuwa kasar Iraki, daya a Basra da kuma a Kufa babban birnin daular musulunci karkashin Imam Hassan (a).
A lokacin da wadan nan ma’aikata biyu suka je inda aka turasu suka fara ayyukansu na leken asiri, sai asirinsu ya tonu, Imam Hassan (a) ya tura shurdatul Khamis suka bazu a cikin kufa har sai da suka zakulo jasusun Ma’awiya a cikin birnin suka kawoshi a gaban Imam Alhassan (a) wanda ya bada Umurni a kashe sai aka kashe shi.
Haka ya faru a Basra ma, inda Abdullahi dan Abbas ® ya sa aka nemo shi aka kuma kama shi aka kawo shi a gabansa ya bada umurni aka kasheshi.
Daga sai Imam Hasan (a) ya rubutawa Mu’awiya wasika, inda a ciki ya aibata shi da cusa dan leken asiri a cikin kufa da Basar, sannan yayi masa barazana da yaki. Sannan ya fada masa cewa ya ji labarin ya nuna jin dadi da shahadar mahaifinsa Imam Ali (a).
Mu’awiya ya tsorata ya kuma mayar masa da amsa kan cewa bai ji dadin kasan mahaifinsa ba, amma yaki ya yi magana kan dan leken asirin da ya aika. Haka ma Ibnu Abbas ya rubutawa Mu’awiya wasika yana aibata shi da cusa dan leken asiri a cikin mutanen Basra. Shi ma mu’awiya ya mayar masa da amsa inda ya bayyana masa cewa Imam Alhassan (a) ya rubuta masa wasika irin tasa, yana aibata shi. Amma bai bayyanawa Ibn Abba kan cewa Imam Al-Hassan (a) yayi masa barazana da yaki.
Bayan haka sai Ibn Abbas ya rubutawa Imam Alhassan wasika inda a cikin yake bashi shawara yake kuma kodaitar da shi kan yakar Mu’awiya da kuma wasu dabarbaru da ya bashi. Ga nassin wasikar kamar yadda take.
:Bayan haka, Lalle musulmi sun mayar maka shugabancinsu bayan Aliyu (a), to zage dantse don yaki, ka yi jihadi da makiyinka, ka kusanto da mutanenka, wadanda suke da raunin Imani ka sayi addininsu don kare kanka daga cutar da kai. Ka kuma dora mutane daga manya-manyan gidaje da daukaka don sai danginsu su bika sannan kan jama’a ta hadu, …..
Ka yi koyi da abinda abinda ya zo daga wajen shuwagabanni adilai, suna cewa karya bata halatta sai a yaki… kuma ka san cewa abinda ya sa mutane suka kauracewa mahaifinka suka koma wajen Mu’awiya shi ne shi mai son daidaita rabo a tsakanin, sai wannan yayi masu nauyi.
Kuma ka san cewa kana yakar wanda ya yaki All..da manzonsa(a) a farkonmusulunci ne, har sai da al-amarin All..ya bayyana ya kuma sami rinjaye. A lokacinda aka kadaita Allah aka shafe shirka addini ya daukaka, sai suka bayyana cewa su masu Imani ne a gaban mutane, suka karanta Alkur’ani suna masu istahza’I da ayoyinsa, suka tsaida sallah suna cikin kasala, suna aikata sauran farillu ba da sonsu ba.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan(a) 155 October 19, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 154 October 19, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Alhassan (a) 153 October 19, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 152 October 19, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 151 October 19, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 150 October 19, 2025 Wata Kotun A Murka Ta Haramtawa HKI Kafa Na’urorin Leken Asiri A Wayoyi Masu WattsApp October 19, 2025 Sojojin Najeriya: Rahotanni Dangane Da Juyin Mulki Wa Shugaba Tinubu Ba Gaskiya Bane October 19, 2025 Hamas Ta Gabatar Da Sunayen Kwararrun Da Zasu Gudanar Da Harkokin Gaza October 19, 2025 Doha: Pakistan da Afghanistan sun amince da tsagaita bude wuta a tsakaninsu October 19, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
CBN ya kara yawan kudin da mutum zai iya cirewa a mako zuwa N500,000
Babban Bankin Najeriya (CBN) ya soke iyakance adadin kuɗin da mutum ko kamfani za su iya ajiyewa a banki sannan ya ƙara yawan kudin da za a iya fitarwa a mako da ₦100,000 zuwa ₦500,000.
Wannan na cikin wata sanarwa da Daraktar Sashen Tsarin Kuɗi da Dokoki ta bankin, Dr. Rita Sike, ta sanya wa hannu kuma ta fitar ranar Laraba.
Gobara ta kashe mata da miji da ’ya’yansu 3 a Katsina Mako mai Majalisa za ta kada ƙuri’a kan ƙudurin ƙirƙirar sabbin jihohiA cewar bankin, an yi sauye-sauyen manufofin ne da nufin rage tsadar sarrafa kuɗi, magance matsalolin tsaro, da kuma dakile haɗarin safarar kuɗi ba bisa ka’ida ba da ke da alaƙa da dogaro da mu’amalar kuɗi kai tsaye.
CBN ya ce manufofin da suka gabata kan kuɗi an gabatar da su ne domin rage amfani da kuɗi kai tsaye da ƙarfafa amfani da hanyoyin biyan kuɗi ta intanet.
Sai dai, sauye-sauyen tattalin arziki da na gudanarwa sun sa dole a sake duba dokokin domin daidaita su da halin da ake ciki a yanzu.
Daga ranar 1 ga watan Janairun 2026, an soke iyakance adadin kuɗin da za a iya ajiye gaba ɗaya, kuma ba za a sake cajin kuɗin da ake ɗauka a kan ajiya mai yawa ba.
Sabbin dokokin sun jingine iyakance fitar kuɗi na mako gaba ɗaya ga mutum ɗaya zuwa ₦500,000, yayin da na kamfanoni ya koma ₦5m.
Kazalika, dokar ta ce fitar kuɗin da ya wuce waɗannan iyakokin zai jawo ƙarin caji na kaso cikin 100 ga mutum ɗaya da kuma kaso biyar cikin 100 ga kamfanoni, inda za a raba kuɗin da aka tara da bankuna bisa tsarin 40:60 tsakanin CBN da bankunan da abin ya shafa.
CBN ya kuma umarci bankuna da su tabbatar da cewa sun saka dukkan nau’o’in kuɗi a cikin na’urar ATM domin sauƙaƙa samun kuɗi.
Babban bankin ya kuma umarci bankuna da su rika gabatar da rahoton wata-wata ga Sashen Kula da Bankuna, Sashen Kula da Sauran Hukumomin Kuɗi, da Sashen Kula da Tsarin Biyan Kuɗi domin tabbatar da bin doka.