Ɗaliban Jihar Gombe Sun Samu Ƙarin Kashi 100 Na Kuɗin Tallafin Karatu
Published: 19th, October 2025 GMT
A wani jawabin da aka yada ta kafar sadarwar zamani ta shafin Facebook jiya, ma’aikatar ta kara da cewa tun lokacin da shi Gwamnan ya dare kan Kujerar mulkin Jihar, mulkin gwamna Inuwa ya kafa dokar ta baci kan lamarin daya shafi ilimi, inda ya bullo da tsare tsare da zuba jari da zummar bunkasa bangaren ilimiin.
Wadanda za su amfana da karin tallafin kudin karatun sun hada dalibai masu karatun da suka hada da PhD, MSc, PGD, BSc, HND, NCE, ND, da kuma Satifiket.
Da yake na shi jawabin wajen sa albarkacin baki kan ci gaban da aka samu, Shugaban kungiyar dalibai ‘yan asalin Jihar da suke Jami’ar Jihar Gombe, Abubakar Muhammad Yamanga, ya bayyanawa LEADERSHIP cewa alawus din da dalibai suke amsa yanzu Naira 7,500, ko dayake dais au da yawa su kan amshi Naira 7,000 bayan wasu cire- ciren da aka yi.
“Wannan ya nuna da yake an riga an bayyana karin, da aka yi, ana kuma sa ran dalibai za su rika amsar fiye da Naira 14, 000. Tuni dai aka riga aka biya Naira 21,000 kowane inda aka biya wasu kudaden da, ba a biya ba can baya,” in ji shi
Kamar dai yadda ma’aikatar ilimi mai zurfi ta bayyana, gwamnan ya amince da karin da aka yiwa mutane masu bukata ta musamman, jim kadan bayan da aka kirkiro hukumar kulawa da lamurran masu bukata ta musamman ta Jihar.
Hukumar bada tallafin karatu ta Jihar Gombe ta bada sanarwar lamarin tantancewa da za ayi domin a samu gano dukkan daliban da suka cancanta su amfana, za a fara cancancewar nan bada dadewa ba da kuma ranakun da za ayi haka, da kuma duk yadda za ayi ita tantancewar.
ShareTweetSendShare MASU ALAKAএছাড়াও পড়ুন:
Jihar Kwara Zata Haɗin Kai Da Masu Ruwa Da Tsaki Wajen Horas Da Matasa Fasahar AI
Ma’aikatar raya matasa ta jihar Kwara tare da hadin gwiwar Masu Ruwa da Tsaki don horar da matasa kan amfani da fasahar AI don ganin sun kasance masu amfani da dogaro da kai, da kuma samun fasaha.
Da yake jawabi a lokacin da tawagar ta ziyarci ma’aikatar a Ilorin, kwamishinan ci gaban matasa na jihar, Ndanusa Shehu, ya bayyana matakin a matsayin wanda ya dace kuma ya kawo sauyi.
A cewarsa Artificial Intelligence wata hanya ce ta tsara makomar aiki a duniya tare da jaddada mahimmancin ganin matasa sun iya amfani da irin wannan kirkirarriyar fasaha.
Ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta ci gaba da nuna kyakykyawan manufa na karfafa matasa, tun daga samar da damammaki a fannin tattalin arzikin dijital zuwa saka hannun jari a fannonin fasaha da kasuwanci.
A nasa bangaren masu, Daraktan Sadarwa, Sanni Alausa-Issa ya ce shirin ya himmatu wajen inganta shugabanci na gari, hada kan jama’a, da ci gaban matasa ta hanyar ilimi na zamani.
ALI MUHAMMAD RABIU