An kama ’yan sandan bogi 5 a Kano
Published: 18th, October 2025 GMT
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta kama wasu ’yan sandan bogi guda biyar, da ke damfarar jama’a wajen karɓar kuɗi a Kano, Katsina da kuma Kaduna.
Waɗanda ake zargin sun haɗa Aliyu Abbas mai shekaru 35, Sani Iliyasu mai shekaru 47, Ashiru Sule mai shekaru 41, Abubakar Yahaya mai shekaru 45 da kuma Adamu Kalilu mai shekaru 45.
Sashe na Musamman na Rundunar SIS ne, ya kama su a ranar 16 ga watan Oktoba, 2025, bayan samin wasu bayanan sirri.
Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, yatabbatar da kama su.
Yayin bincike, an samu katin bogi ’yan sanda, ankwa, latattun kuɗi da motarsu ƙirar Peugeot 406 mai launin shuɗi mai lambar NSR-188-BD.
SP Kiyawa, ya bayyana cewa bincike ya gano cewa ƙungiyar tana amfani da katunan bogi wajen yin damfara, tsoratar da direbobi, da karɓar kuɗi a hannun jama’a a sassan Arewa maso Yamma.
“Waɗanda ake zargin sun amsa cewa ’yan sandan bogi ne kuma suna aikata laifuka daban-daban na damfara.
“Za a gurfanar da su a kotu bayan kammala bincike,” in ji Kiyawa.
Kwamishinan ’yan sandan Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya yaba wa jami’an rundunar saboda ƙwarewarsu wajen cafke waɗanda ake zargin.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Sanda Yan sandan bogi bayanan sirri mai shekaru
এছাড়াও পড়ুন:
Xi Ya Taya Hukumar FAO Murnar Cika Shekaru 80 Da Kafuwa
Ya ce kamar ko da yaushe, kasar Sin za ta ci gaba da goyon bayan muhimmiyar rawar da FAO ke takawa a bangaren aikin gona da samar da abinci a duniya.
An kafa hukumar FAO ne a ranar 16 ga watan Oktoban shekara ta 1945, kuma Sin na daya daga cikin kasashe mambobi da suka kafa ta. (Fa’iza Mustapha)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA