HausaTv:
2025-10-19@10:44:51 GMT

Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 152

Published: 19th, October 2025 GMT

152-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshin da suka zo cikin alkur’ani mai girma ko cikin wasu littana wadanda suka hada da littafin Dastane Rastan na Aya. Murtadha Muttahari, ko kuma cikin littafin Mathnawa, na maulana jalaluddeen Rumi ko kuma cikin wasu littafan da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu a cikin shirimmu na yau.

////… Madallah, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, a kuma cikin sirar Imam Hassan Al-Mujtaba(a) dan Fatimah diyar manzon All..(s) da muke kawo muku. Mun yi maganar yadda, aka kawo likitoci don jinyar Amirulmuminina(a). Inda shugaban likitocin Atthi dan Amru Assakuni ya bukaci a kawo masa jijiyar akuwa mai zafi sai aka kawo masa, ya Sanya ta cikin raunin da aka yi masa, bayan wani lokaci ya fitar da ita sai ya ga cewa fari-farin kwakwalwansa na makale a jikinta, sai ya tabbatar da cewa ba zai rayuba, saboda takobin ya kai cikin kwakwalwansa.

Daganan Imam (a) y afara wasiyoyinsa daban-daban da farko ga yayansa Imam Al-Hassan da Al-Hussain(a) sannan wasu ga iyalan gidansa da kuma yayansa. Wasun kuma ga duk wanda wasiyyar ta isheshi.

Sannan ya yi wa sauran musulmi ma iznin shiga wajensa inda ya bukacesu su tambaye shi kafin su rasa shi, inda suka yi masa tambayoyi, amma ba masu yawa ba don halin da yake ciki.

Daga karshe sai yayi wasiyya ga danga Imam Alhassan a matsayin khalifan al-ummar musulmi a bayansa. Sannan Alhusain (a) bayan Alhassan(a). Ya kafa shaidar hakan da sauran yayansa da manya-manyan malaman shi’a, sannan malaman shi’a basu da wani sabani dangane da hakan.

Daga ciki har da hadisin da  Kulaini ya ruwaito, dangane da wasiyya , har zuwa inda yake cewa:

{Ya da na! Manzon Allah (s) ya umurce ni, da in yi wasiyya gareka, kuma in baka littafaina da makamaina, Kumar yadda manzon Allah (s) ya yi sanya ni wasiyyinsa, ya mika mani littafansa, da makamansa, kuma ya umurce ni da in umrceka kan cewa idan mutuwa ta zo maka ka mika su ga dan’uwanka Husain(a)}

Daga karshe ya ce masa shi ne waliyin jininsa, idan ya mutu. In yaga dama ya yi afwa in zai kashe kuma duka da duka.

Sannan muka ce wasu malaman sunna sun bayyana cewa Amirulmuminina (a) bai yi wasiyyah ba, kamar yadda suka ce manzon All..(s) ma bai yi wasiyya ba. Tare da dogara da wani hadisi wanda wanda shu’aib ya ruwaito, shu’ab wanda ya shahara da karyawa.

Don wasiyyar Imam Hassan da al-hussain (a), hadisan manzon All..(a) ne, wasu ma ayoyin Alkur’ani ne. su shuwagabannin Aljannae, ga Alhussain, yana cewa: Kai limami ne, dan Iimami ne, dan Uwar Imam sannan Baban limamai 9. Suna cikin ayar tsarkakiwa, suna cikin ayar mubahala, da sauransu.

Wadanda sun wadatar wajen tabbatar da cewa Imam Alhassan (a) wasiyyi ne daga cikin wasiyyan manzon All..(s).

Sannan yadda ko way a san Amirulmuminina (a) yake son hadin kan al-ummar musulmi, ba zai yu ya tafi ya bar al-ummar manzon Allah(s) ba tare da mai kula da su ba.

A lokacinda tafiyarsa ta karato y afara jin zafin ciwon da kuma mutuwa sai ya yawaita addu’o’io da zikirin Allah karshen abinda Kalmar da ta fito daga bakinsa itace {Saboda irin wannan to masu aiki su yi aiki} cikin suratul Saffaat aya ta 61.

Sannan ruhinsa ya fita, ya tafi aljanna firdauci, ya koma inda ya fito. Ya zo ya haskaka duniya da hasken shiriya, ya kuma huta da musibun duniya. Imam ya barma ilmin wanda al-ummar manzon All..(s) zata amfana da shi har duniya ta nade.

Ya bar mana tarin ayyuka da yayi tun haihuwarsa a dakin Kaaba har zuwa ranar da ya bar nan duniya, yana dan shekara 63 a duniya, bayan gwagwarmaya da mushrikai a makka, da kuma yakarsu a yakokin manzon All..(s) har iya yau da zama karshen wadanda suka kwace hakkinsa na kimani shekaru 25, da kuma shugabanci abin buka misali har duniya ta nade, da kuma yakar munafukai a jamal da siffin na Nahrawan.

Wannan shi ne Aliyu dan Abitalib Amirul muminina (a), taskar ilmin manzon All..(s) sannan Harunansa, kamar yadda annabi haruna yake ga Musa(a).

Imam Hassan (a) ne ya yi masa duk abinda akewa mamaci, kama daga wanka, hanuth da likkafani. Sannan bayan dare ya raba sai shi tare da wasu mutane daga iyalan gidansa suka Sanya shi a Najafur Ashraf, wanda a lokacin Daji ne. a bayan garin Kufa.

A lokacinda gari yaw aye sai Imam Al-Hassan (a) ya bukaci a kawo masa dan Mujam da aka kawo shi sai ya tambaye shi : Menen babanka ya umurceka dangane da ni? Sai Imam (a) ya amsa masa da cewa {Ya umurce ni da cewa kada in kashe sai wanda ya kashe shi. Kuma in cika maka cikinka, in gyara halinka, in yaru yayi kisasa ko ya yi afawa, idan kuma ya mutu in hadaka da shi}

Sai la’anennen yace: Duk da cewa babanka yana fadar gaskiya, amma yana hakan a cikin fushi da yarda.

Sai Imam Hassan (a) ya da kansa ya dauki takobi ya sare shi a kansa amma ya tare dukan da hannayensa. Sai ya kashe kawai. Bai yi muthla da shi ba.

A cikin wasu littafn tarihi, an bayyana cewa wai Imam Hassan yayi Muthla da shi duk tare da nanatawa da mahaifinsa yayi na kada ya yi hakan.

Ko kuma wasu sun bayyana cewa wasu daga cikin yayan Iman Ali (a) suka yi muthla da shi. Sun kuma kawo hadisai da ruwayoyi da suke nuna hakan.

Sai dai wannan zatonsu ne ga iyalan gidan manzon All…(a) sai. Amma gidan tsarki da annabta sun wuce nan, ba wanda zai wuce su a riko da shari’ar Allah ta’ala.

Sannan sabanin da ce cikin hadisan da suka ruwaito na haka ya faru ya tabbatar da cewa zancen karyace ce.

Daga cikin wadanda suka kawo wadannan ruwayoyi na karya suke kuma ganin gaskiya ne haka ya faru, akwai Dr Taha Hussain a cikin littafinsa ‘Aliyu wa banuhu’. Sai dai gaskiyar al-amarin ba haka bane basu yi muthla da shi ba.

Bayan jana’iza da kuma kisasi kan Abdurrahman dan Muljamul Muradi, sai batun bai’a wa Imam Al-Hassan (a). wanda ya kasance a cikin wani hali na rashin tsaro a cikin daular Musulunci.

Imam Hassan (a) ya gaji rundunar mahaifinsa wacce taki fida don yakar Mu’awiya, sannan mu’awiya na na ci gaba da mamayar ragowar yankunan da suke karkashin ikon Amirul muminina Aliyu dan Abutalib (a), wanda Imam Alhassan ya gada.

Sannan shahadar Imam Ali (a) ya karawa Mu’awiya dan Abusufyan karfin giwa na cewa zai iya samun nasara a kan Imam Hassan ya kuma mallaki dukkan daular musulunci, sannan wannan ya sharewa babu umayya hanyar maida khalifanci gadon gidansu. Da kuma shimfida zalunci da kissan al-ummar musulmi da dandana masu azaban da basu tsamman zai faru ba, kafin haka.

Ya zuwa shahadar Imam Ali(a) mu’awiya ya kwace Makka da Madina da yemen da Masar bayan kissan Muhammad dan Abubakar da kuma Malikul Ashatar. Kasar Iraki kadai ta rage a hannunsa zuwa lokacin.  

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 151 October 19, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 150 October 19, 2025 Wata Kotun A Murka Ta Haramtawa HKI Kafa Na’urorin Leken Asiri A Wayoyi Masu WattsApp October 19, 2025 Sojojin Najeriya: Rahotanni Dangane Da Juyin Mulki Wa Shugaba Tinubu Ba Gaskiya Bane October 19, 2025 Hamas Ta Gabatar Da Sunayen Kwararrun Da Zasu Gudanar Da Harkokin Gaza October 19, 2025 Doha: Pakistan da Afghanistan sun amince da tsagaita bude wuta a tsakaninsu October 19, 2025 Isra’ila ta ce mashigar Rafah za ta ci gaba da kasancewa a rufe har sai abin da hali ya yi October 19, 2025 Araqchi: Kuduri Mai Lamba 2231 Ya Zo Karshe October 18, 2025 Kasashen Iran, Rasha, Da China Sun Jaddada Rashin Halaccin Dawo Da Tsohon Takunkumi Kan Iran October 18, 2025 Masani Kan Harkokin Tsaro Ya Ce: Makami Mai Linzamin Iran Kirar Ghadir Ya Aike Da Sako Ga Isra’ila October 18, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

KissoshinRayuwa : Sirar Imam Al-Hassan(a) 156

156-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshin da suka zo cikin alkur’ani mai girma ko cikin wasu littana wadanda suka hada da littafin Dastane Rastan na Aya. Murtadha Muttahari, ko kuma cikin littafin Mathnawa, na maulana jalaluddeen Rumi ko kuma cikin wasu littafan da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu a cikin shirimmu na yau.

////… Madallah, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, a kuma cikin sirar Imam Hassan Al-Mujtaba(a) dan Fatimah diyar manzon All..(s) da muke kawo muku. Mun yi maganar yadda, yadda Mu’awiya dan abusufyan ya kidemi bayan bayan ya sami labarin cewa an yiwa Imam Hassan bai’a a matsayin Khalifan musulmi a kufa, sannan ya kira taron mashawartansa suka zauna suka kuma fidda wassu al-amura guda biyu don fuskantar Imam Al-Hassan(a). Kuma sune, aika jasusu mai aiko masu labarai sirri daga kasar Iraki, musamman a biranen Kufa da Basra wadanda suka kasance manya-manyan garuruwan a lokacin a kasar Iraki.

Sannan na biyu kuma suna son sayan wasu manya-manyan shugabannin Iraki wadanda suke taimakawa Imam Alhassan (a) don su barshi shikadai, hakan zai tilasta masa ya mika kai ga mu’awiya dan Abusufyan.

Sannan ba tare da bata lokaci ba suka aika mutanen biyu zuwa kasar Iraki, daya a Basra da kuma a Kufa babban birnin daular musulunci karkashin Imam Hassan (a).

A lokacin da wadan nan ma’aikata biyu suka je inda aka turasu suka fara ayyukansu na leken asiri, sai asirinsu ya tonu, Imam Hassan (a) ya tura shurdatul Khamis suka bazu a cikin kufa har sai da suka zakulo jasusun Ma’awiya a cikin birnin suka kawoshi a gaban Imam Alhassan (a) wanda ya bada Umurni a kashe sai aka kashe shi.

Haka ya faru a Basra ma, inda Abdullahi dan Abbas ®   ya sa aka nemo shi aka kuma kama shi aka kawo shi a gabansa ya bada umurni aka kasheshi.

Daga sai Imam Hasan (a) ya rubutawa Mu’awiya wasika, inda a ciki ya aibata shi da cusa dan leken asiri a cikin kufa da Basar, sannan yayi masa  barazana da yaki. Sannan ya fada masa cewa ya ji labarin ya nuna jin dadi da shahadar mahaifinsa Imam Ali (a).

Mu’awiya ya tsorata ya kuma mayar masa da amsa kan cewa bai ji dadin kasan mahaifinsa ba, amma yaki ya yi magana kan dan leken asirin da ya aika. Haka ma Ibnu Abbas ya rubutawa Mu’awiya wasika yana aibata shi da cusa dan leken asiri a cikin mutanen Basra. Shi ma mu’awiya ya mayar masa da amsa inda ya  bayyana masa cewa Imam Alhassan (a) ya rubuta masa wasika irin tasa, yana aibata shi. Amma bai bayyanawa Ibn Abba kan cewa Imam Al-Hassan (a) yayi masa barazana da yaki.

Bayan haka sai Ibn Abbas ya rubutawa Imam Alhassan wasika inda a cikin yake bashi shawara yake kuma kodaitar da shi kan yakar Mu’awiya da kuma wasu dabarbaru da ya bashi. Ga nassin wasikar kamar yadda take.

:Bayan haka, Lalle musulmi sun mayar maka shugabancinsu bayan Aliyu (a), to zage dantse don yaki, ka yi jihadi da makiyinka, ka kusanto da mutanenka, wadanda suke da raunin Imani ka sayi addininsu don kare kanka daga cutar da kai. Ka kuma dora mutane daga manya-manyan gidaje da daukaka don sai danginsu su bika sannan kan jama’a ta hadu, …..

Ka yi koyi da abinda abinda ya zo daga wajen shuwagabanni adilai, suna cewa karya bata halatta sai a yaki… kuma ka san cewa abinda ya sa mutane suka kauracewa mahaifinka suka koma wajen Mu’awiya shi ne shi mai son daidaita rabo a tsakanin, sai wannan yayi masu nauyi.

Kuma ka san cewa kana yakar wanda ya yaki All..da manzonsa(a) a farkonmusulunci ne, har sai da al-amarin All..ya bayyana ya kuma sami rinjaye. A lokacinda aka kadaita Allah aka shafe shirka addini ya daukaka, sai suka bayyana cewa su masu Imani ne a gaban mutane, suka karanta Alkur’ani suna masu istahza’I da ayoyinsa, suka tsaida sallah suna cikin kasala, suna aikata sauran farillu ba da sonsu ba.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan(a) 155 October 19, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 154 October 19, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Alhassan (a) 153 October 19, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 152 October 19, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 151 October 19, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 150 October 19, 2025 Wata Kotun A Murka Ta Haramtawa HKI Kafa Na’urorin Leken Asiri A Wayoyi Masu WattsApp October 19, 2025 Sojojin Najeriya: Rahotanni Dangane Da Juyin Mulki Wa Shugaba Tinubu Ba Gaskiya Bane October 19, 2025 Hamas Ta Gabatar Da Sunayen Kwararrun Da Zasu Gudanar Da Harkokin Gaza October 19, 2025 Doha: Pakistan da Afghanistan sun amince da tsagaita bude wuta a tsakaninsu October 19, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kissoshin rayuwa: Sirar Imam Hassan (a) 159
  • Kissoshin rayuwa: Sirar Imam Hassan(a) 158
  • Kissoshin rayuwa: Sirar Imam Al-Al-Hassan (a) 157
  • KissoshinRayuwa : Sirar Imam Al-Hassan(a) 156
  • Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan(a) 155
  • Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 154
  • Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Alhassan (a) 153
  • Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 151
  • Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 150