Gaza: HKI Tana Ci Gaba Da Keta Yarjejeniyar Tsagaita Wuta
Published: 19th, October 2025 GMT
Falasdinawa da dama ne su ka yi shahada, yayin da wasu kuma su ka jikkata sanadiyyar hare-haren keta yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza.
Tashar talabijin din ‘almayadin’ ta bayar da labarin cewa; An sam shahidai 5 da kuma jikkatar wasu da dama a wani hari da ‘yan sahayoniya su ka kai a wani wurin shan shayi dake yammacin birnin “Deir-Balah” dake tsakiyar yankin Gaza.
Haka nan kuma tashar talabijin din ta ce sojojin mamayar sun kai wani harin a garin Zuwaidah, dake tsakiyar zirin Gaza da ya jikkata mutane da dama.Wasu Karin hare-haren na ‘yan sahayoniya sun shafi binin Rafah, da Jabaliya.
Kafafen watsa labarun HKI sun sanar da cewa sojojinsu sun kai wasu hare-hare har 20 a Gaza.
A cikin sa’o’i 24 da su ka gabata adadin shahidan Falasdinawa sun kai 8, yayin da wasu 10 da su ka jikkata.
Kididdigar ma’aikatar lafiya ta Falasdinu ta ce daga 7/10/2023 zuwa yanzu jumillar shahidan Falasdinawa sun kai 68,159, sai kuma wasu 17,203 da su ka jikkata.
A gefe daya ma’aikatar kiwon lafiyar ta Falasdinawa ta sanar da karbar shahidai 15 da HKI ta mika gawawwakinsu a karkashin yarjejeniya, da hakan ya sa jumillar adadin shahidan da su ka karba zuwa 150.
A wani labarin na daban, HKI ta bayar da umarnin dakatar da shigar da kayan agaji zuwa cikin yankin wanda shi ma karya yarjejeniyar tsagaita wuta ce.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Hamas ta yi Allah wadai da Isra’ila kan keta yarjejeniyar tsagaita bude wuta October 19, 2025 An gudanar da zanga-zanga a sassa da dama na Amurka October 19, 2025 MDD : “Zai dauki lokaci” kafin a rage yunwa a Gaza October 19, 2025 ICC ta ki amincewa da daukaka karar Isra’ila October 19, 2025 Kissoshin rayuwa: Sirar Imam Hassan (a) 159 October 19, 2025 Kissoshin rayuwa: Sirar Imam Hassan(a) 158 October 19, 2025 Kissoshin rayuwa: Sirar Imam Al-Al-Hassan (a) 157 October 19, 2025 KissoshinRayuwa : Sirar Imam Al-Hassan(a) 156 October 19, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan(a) 155 October 19, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 154 October 19, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Jihar Kaduna Ta Gabatar Da Kasafin Kudin 2026 Na Kimanin Triliyan Daya
Daga Shamsuddeen Mannir Atiku
Majalisar Dokokin Jihar Kaduna ta karɓi daftarin kasafin kuɗin shekarar 2026 da ya zarce naira miliyan dubu dari tara da tamanin da biyar daga bangaren zartarwa jihar.
Da yake gabatar da kasafin kudin a zauren majalisar, Gwamna Malam Uba Sani ya bayyana kasafin a matsayin na sauye-sauye da ci-gaba wanda aka tsara domin bunkasa al’umma cikin tsarin da ya haɗa kowa da kowa.
Ya ce gabatar da kasafin kuɗi muhimmin al’amari ne na dimokradiyya da ke bai wa gwamnati damar yin waiwaye, da tantance nasarorin da aka samu, da kuma fayyace hanyoyin ci gaba na shekara mai zuwa.
Gwamnan ya bayyana cewa an ware sama da naira biliyan dari shida da casa’in da tara daidai da kashi kashi 71 ga manyan ayyukan ci gaba, yayin da sama da naira biliyan dubu dari biyu da tamanin da shida daidai da kashi 29 za su tafi ga al’amuran yau da kullum.
Ya ce kaso mafi tsoka na ayyukan ci gaba ya mayar da hankali ne kan gina manyan muhimman ababen more rayuwa masu dorewa.
Rabe-raben kason sune: Ilimi ya samu kashi 25 bisa dari, sai Ayyukan Gine-gine da Cigaban KarKarkashi ma kashi 25 bisa 100, Lafiya kashi 15 bisa 100; Noma da Samar da Abinci kashi 11 bisa 100; Tsaro kashi 6 bisa 100; Ci gaban Zamantakewa kashi 5 bisa 100; Muhalli da Matakan Sauyin Yanayi kashi 4 bisa 100; sai Mulki da Gudanarwa kashi 5 bisa 100.
A nashi jawabin, Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kaduna, Rt. Hon. Yusuf Dahiru Liman, ya ce kasafin kuɗin 2026 ya nuna sahihiyar manufa wadda ta ƙunshi faɗaɗa ababen more rayuwa a yankunan karkara, da habbaka kwazon ma’aikata da tabbatar da ganin dukkan al’ummomi suna cin gajiyar ci gaba mai ɗorewa da ya haɗa kowa.
Rt. Hon. Liman ya jinjina ga Gwamna Uba Sani da tawagarsa a bisa gabatar da kasafin da ya dace da hangen nesan gwamnatin da ke ƙoƙarin gina Jihar Kaduna mai yalwar arziki.
Ya kuma gode wa gwamnan bisa samar da zaman lafiya, haɗin kai da sabunta kudurori a fadin jihar, tare da yabawa gwamnan bisa rashin yin katsalandan cikin harkokin majalisar wanda hakan alama ce dake nuna cikakken tsarin rabon iko da ke taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da ingantaccen sa ido da daidaito tsakanin bangarorin gwamnati.