Mataimakin firaministan kasar Sin, kana jagoran tawagar kasar mai tattauna batutuwan tattalin arziki da cinikayya da tsagin Amurka He Lifeng, ya zanta ta kafar bidiyo da sakataren baitul-malin Amurka Scott Bessent, da wakilin cinikayyar kasar Jamieson Greer a jiya Asabar.

Yayin zantawar tasu, jami’an sassan biyu sun amince da gudanar da sabon zagayen tattaunawa game da batutuwan da suka shafi tattalin arziki da cinikayya nan ba da jimawa ba.

Kazalika, sassan biyu sun yi musayar ra’ayoyi bisa sahihanci, da zurfafa tattaunawa, da musaya mai ma’ana dangane da yadda za a aiwatar da matsayar da shugabannin kasashen biyu suka cimma, yayin tattaunawarsu ta wayar tarho a farkon shekarar nan, da ma muhimman batutuwa masu nasaba da dangantakar tattalin arziki da cinikayya dake tsakaninsu. (Saminu Alhassan)

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Ma’aikatar Cinikayyar Kasar Sin Ta Fitar Da Rahoton Shekarar 2025 Game Da Biyayyar Amurka Ga Ka’idojin WTO October 17, 2025 Daga Birnin Sin An Kara Habaka Sabon Karfin Samar Da Kayayyaki Da Hidimomi Mai Dorewa a Cikin Watannin Tara Na Farkon Bana October 17, 2025 Daga Birnin Sin Tawagar Sin Ta Dindindin A Hukumar Fao Ta Fara Aiki October 17, 2025

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Taron Malamai Ya Nemi Haɗin Kai Domin Magance Rashin Tsaro, Talauci Da Rarrabuwa A Arewa

 

Manyan malamai, shugabanni na addini, gargajiya da siyasa daga sassan Arewacin Najeriya sun hallara a Kaduna domin Taron Musamman na Malaman Arewa (Special Northern Ulamah Summit), wanda ya mayar da hankali kan nemo mafita ta dindindin ga matsalolin tsaro da ƙalubalen tattalin arziki da ke addabar yankin.

 

Taron ya tattauna kan ƙarfafa haɗin kai tsakanin malamai, amfani da kafafen sada zumunta ta hanyar da ta dace, da kuma ƙarfafa hulɗa tsakanin shugabannin addini, gargajiya da na siyasa domin dawo da zaman lafiya da daidaito a al’umma.

 

Da yake jawabi, Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar na Uku, wanda Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmad Nuhu Bamalli ya wakilta, ya kira malamai da shugabanni su haɗa kai wajen yaki da rashin tsaro, talauci da rarrabuwa. Ya gargaɗi malamai da al’umma da su guji amfani da kafafen sada zumunta wajen yada ƙarya da haifar da fitina.

 

Sarkin Musulmi ya jaddada cewa zaman lafiya da kwanciyar hankali za su tabbata ne kawai idan aka samu haɗin kai na gaskiya tsakanin sassa daban-daban na al’umma bisa koyarwar addinin Musulunci.

 

A jawabinsu na haɗin gwiwa, Sheikh Abdullahi Bala Lau da Dr. Ahmad Abubakar Mahmud Gumi sun bayyana cewa son kai, rarrabuwa, da matsin tattalin arziki na daga cikin manyan abubuwan da ke kawo rashin tsaro a Arewa. Sun ce lokaci ya yi da shugabannin addini, gargajiya da siyasa za su buɗe tattaunawa mai fa’ida tare da yin aiki tare domin kawo ƙarshen rikice-rikice da koma bayan tattalin arziki.

 

Haka kuma, Sanata Abdulaziz Yari Abubakar na Jihar Zamfara, Sanata Shehu Buba na Jihar Bauchi, da Honourable Alhassan Ado Doguwa na Jihar Kano, sun yaba da wannan taro suna mai cewa lokaci yayi da za a ɗauki mataki na haɗin kai domin ceto yankin Arewa daga ƙalubale.

 

Sanata Yari ya ce rashin tsaro na ci gaba da ƙaruwa ne saboda rashin daidaito da ƙarancin damar tattalin arziki, yayin da Sanata Buba ya jaddada muhimmancin ƙarfafa matasa da aiwatar da gyare-gyaren zamantakewa bisa ka’idojin Musulunci.

 

Honourable Doguwa, wanda shi ne Shugaban Ƙungiyar ‘Yan Majalisar Wakilai na Arewa (Northern Caucus), ya tabbatar da goyon bayan majalisa ga sakamakon taron, tare da alkawarin haɗa hannu da hukumomi da shugabanni domin tabbatar da zaman lafiya da ci gaba a yankin.

 

A ƙarshen taron, mahalarta sun amince da kafa Cibiyar Jagorancin Addinin Musulunci ta Ƙasa (National Islamic Leadership Forum), domin haɗa malamai, shugabanni da masu tsara manufofi a ƙarƙashin dandalin haɗin kai, zaman lafiya da ci gaba.

 

COV: Shettima Abdullahi

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Masanin Ilimin Physics Chen Ning Yang Ya Rasu Yana Da Shekaru 103
  • Kasar Sin Ta Gargadi Amurka Game Da Yunkurin Samarwa Yankin Taiwan Makamai
  • Fitar Da Kudi Ta Haramtacciyar Hanya Na Kara Dagula Matsalar Tattalin Arziki – IMF
  • Ma’aikatar Cinikayyar Kasar Sin Ta Fitar Da Rahoton Shekarar 2025 Game Da Biyayyar Amurka Ga Ka’idojin WTO
  • Ma’aikatar Kasuwanci Ta Kasar Sin: Sin Za Ta Kyautata Matakan Takaita Fitar Da Ma’adanan Farin Karfe Na Rare Earth
  • Taron Malamai Ya Nemi Haɗin Kai Domin Magance Rashin Tsaro, Talauci Da Rarrabuwa A Arewa
  • Wane Ci Gaba Yarjejeniyar Tsagaita Wuta A Gaza Ta Haifar?
  • Alkaluman Jin Ra’ayi na CGTN Sun Shaida Amincewar Al’umma Da Karfin Tattalin Arzikin Kasar Sin
  • Sashen Cinikayyar Kamfanonin Sarrafa Hajoji Na Sin Ya Bunkasa Da Kaso 4.7 Bisa Dari Cikin Watanni Tara Na Farkon Shekarar Nan